Harin Ƴan Bindiga: Mutane Sun Ji Azaba, Sun Fara Tserewa daga Gidajensu a Filato
- A yammacin ranar Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari yankin Bunyun, inda suka sace mutane uku, ciki har da ‘yan fada biyu
- Sakamakon harin, an kona gidaje da dama, wanda ya tilastawa mazauna garin tserewa zuwa garin Bashar don tsira da rayukansu
- Sarkin Bunyun ya bukaci gwamnati ta tura jami’an tsaro domin bai wa manoma damar komawa gonakinsu da cigaba da rayuwarsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Plateau – An sace mutane uku, ciki har da 'yan fada biyu, sannan an kona gidaje da dama a yankin Bunyun, dake Bashar a karamar kukumar Wase ta kihar Plateau, a ranar Laraba.
Wannan harin da aka kai wa al'ummar Bunyun ya faru ne kwana huɗu bayan da 'yan bindiga suka kai hari yankin, inda suka kashe 'yan banga tare da kona gidaje da dama.

Kara karanta wannan
Plateau: Batun kisan ƴan Zaria ya dawo, an gurfanar da mutum 22 bayan gama bincike

Source: Facebook
Yadda 'yan bindiga suka kai hari Filato
Abdulbari'u Muhammad, sarkin gargajiya na garin, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust, inda ya bayyana cewa 'yan bindigar sun sace 'yan fada biyu (Waziri da Wakili) da kuma ƙaninsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sarkin gargajiyan, 'yan bindigar sun kai hari yankin a ranar Laraba da misalin karfe 7:30 na yamma, inda suka rika harbe-harbe ba kakkautawa.
Ya ƙara da cewa wannan sabon harin yana da alaƙa da rikicin da ya faru tsakanin 'yan banga da 'yan bindiga a ranar Lahadi.
Abdulbari'u Muhammad ya ce:
"'Yan bindiga masu yawa haye a kan babura sun afka wa yankin. Sun sace kayayyaki masu daraja, ciki har da abinci, tufafi, babura, da sauran kayayyaki."
Mazauna Bunyun sun tsere daga gidajensu
Sarkin gargajiyan, wanda ya gudu zuwa garin Bashar, ya bayyana cewa yawancin mazauna yankin sun tattara kayansu sun gudu daga yankin saboda tsoro.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Fulani makiyaya sun bankawa gidaje 100 wuta, mutum 1 ya mutu a Taraba
Ya bayyana cewa:
"Mun ruɗe gaba ɗaya kuma ba mu san abin yi ba, shi ya sa muka tsere daga garin zuwa garin Bashar. Kowa ya gudu saboda mutane suna tsoron zama a yankin yanzu."
Sai dai Muhammad ya jaddada cewa mazauna yankin, waɗanda galibi manoma ne, sun riga sun shuka amfanin gonakinsu.
Ya jaddada buƙatar gwamnati ta tura isassun jami'an tsaro zuwa yankin don ba su damar ci gaba da noma da kuma gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.

Source: Original
An ga mata dauke ka kaya suna barin Bunyun
Abubakar Zubairu, wani mazaunin yankin, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa mutane sun yi kaura daga yankin a safiyar Alhamis. Ya ƙara da cewa shi ma ya gudu zuwa Bashar don tsira da rayuwarsa.
Wakilin jaridar ya ruwaito cewa an ga mata da yara suna ɗauke da kayansu a kawunansu suna gudun hijira daga yankin.
Har yanzu kakakin Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom, bai amsa kiran waya ko saƙon kar-ta-kwana da aka tura masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Mutane na tserewa daga gidajensu a Zamfara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, mazauna wasu kauyuka a Kauran Namoda a Zamfara na guduwa daga gidajensu saboda yawaitar harin ‘yan bindiga.
Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutum hudu sun mutu yayin da aka sace wasu 26 a sababbin hare-haren da aka kai a kauyukan.
Gwamna jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ba da tabbacin ƙara taimaka wa hukumomin tsaro don kawo ƙarshen matsalar 'yan ta'adda da ke addabar jihar.
Asali: Legit.ng
