Birnin Gwari: Mazauna suna tserewa daga gidajensu saboda harin 'yan bindiga

Birnin Gwari: Mazauna suna tserewa daga gidajensu saboda harin 'yan bindiga

- Mazauna yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna suna tserewa daga gidajensu don neman tsira

- Mutanen yankin suna barin gidajensu da gonakansu saboda tsoron harin 'yan bindiga

- An bayyana sace wasu mutane tare da kashe wasu da dama a yankin a yayin wani hari

Mazauna yankin Randagi da ke karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna suna tserewa daga gidajensu kwanaki kadan bayan da ‘yan bindiga suka far wa yankin.

Wadanda suka gudu, galibinsu mata, yara, tsofaffi sun tattara kayansu a ranar 6,7 da 8 ga watan Fabrairu don neman mafaka tare da danginsu a garin Birnin Gwari da makwabtan jihar Neja.

Daily Trust ta ruwaito yadda barayin suka mamaye kauyen wanda ya sa maza suka kori matansu daga garin.

An tattaro cewa a kokarin tserewa, wani jami’in da ke aikin kula fursunoni, Muhammadu Gagare, an kashe ’ya’yansa uku, biyu daga cikin matansa da wasu yara hudu da 'yan fashi suka sace a hanyarsu ta zuwa Kaduna.

KU KARANTA: Nasarorin da na cimma sun kai a rubuta littatafai akai, in ji Burutai

Birnin Gwari: Mazauna suna tserewa daga gidajensu saboda harin 'yan bindiga
Birnin Gwari: Mazauna suna tserewa daga gidajensu saboda harin 'yan bindiga Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Gagare ya shaida wa Daily Trust cewa har yanzu matansa da ’ya’yansa suna tare da 'yan bindigar wadanda a yanzu ke neman a biya su Naira miliyan 20 kudin fansa bayan ’yan fashin sun bude wuta a kan motar da ke daukar iyalansa zuwa Kaduna.

Wani mazaunin Randagi, Aliyu Muktar ya ce shi da matansa biyu, yara 13 da iyayensu yanzu haka suna samun mafaka tare da danginsa a garin Birnin Gwari bayan sun tsere daga garin.

”Mu kusan mutane 20 ne muka gudu saboda babu abinci kuma mutane suna barin garin ne kawai saboda tsoron kada 'yan fashi su kawo musu hari. Gaskiya abin ya munana,” in ji shi.

Wani, Shehu Muktar Randagi ya shaida wa manema labarai cewa wata al'umma da ta kunshi kusan 40,000 ciki har da wadanda suka fito daga makwabtan Ukuru, Galma da Wamba sun bar gidajensu.

Ya ce kauyukan sun koma kufayi yayin da mutane suka bar gonakinsu, kayan abinci da sauran kayayyakinsu.

”Yayin da muke magana mutane 27 galibi mata da yara suna tare da ni a gidana na Birnin Gwari. Ba su da wurin zuwa kuma ga yunwa a ko’ina,” inji shi.

Ya yi kira da a kara tura jami'an tsaro a yankin don karfafa wa mutane gwiwa su koma gidajensu.

KU KARANTA: Gemu ba ya hana ilimi: Wata mata 'yar shekaru 50 ta shiga makarantar sakandare

A wani labarin, Wani matashi dan shekara 34 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, Sampson Ebiowei, ya bayyana cewa ya samu bindigarsa ta AK-47 ne daga hannun wani sojan Najeriya da ke aikin Operation Lafiya Dole a yankin Arewa maso Gabas.

Ya kuma kara da cewa sojan ya sayar masa da bindigar ne kan kudi N300,000, Sahara Reporters ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel