Rundunar ƴan Sanda Ta Kaddamar da Operation Kukan Kura, Ta Cafke Mutum 98 a Kano

Rundunar ƴan Sanda Ta Kaddamar da Operation Kukan Kura, Ta Cafke Mutum 98 a Kano

  • Rundunar ‘yan sandan Kano ta ƙaddamar da Operation Kukan Kura wanda ya kai ga cafke mutum 98 da ake zargin da laifuka daban-daban
  • CP Ibrahim Bakori ya ce shirin zai hana fashi, garkuwa, fataucin miyagun ƙwayoyi da sauran laifuffuka, a wani yunkuri na inganta tsaro a Kano
  • Rundunar ta kwato manyan makamai, motocin sata, kayan haram, kuɗin jabu da miyagun kwayoyi yayin samame da aka kai a fadin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano – Rundunar ƴan sandan Kano ta ƙaddamar da wani sabon shiri na musamman mai suna ‘Operation Kukan Kura,’ wanda ya kai ga cafke mutane 98 a faɗin jihar.

Kwamishinan ƴan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a hedikwatar ƴan sandan da ke Bompai a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Darajar Annabi SAW: 'Yan sandan Kano sun gayyaci Sheikh Lawan Triumph

Rundunar 'yan sandan Kano ta cafke mutum 98 bayan kaddamar da shirin Operation Kukan Kura
Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, yana bayani game da Operation Kukan Kura. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kakakin 'yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa CP Ibrahim Adamu Bakori ya bayyana irin dabarun da rundunar ke amfani da su da kuma nasarorin da ta samu kwanan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manufar kaddamar da 'Operation Kukan Kura'

CP Ibrahim Bakori ya ce an kaddamar da Operation Kukan Kura domin gano duk wata barazana ta laifuffukan ta'addanci da suka shafi birnin Kano, da kuma dakile su tun da wuri.

Laifuffukan da ake son dakilewa sun haɗa da fashi da makami da garkuwa da mutane a kan iyakokin Kano, sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma sauran munanan ɗabi'u a jihar.

Ya nanata cewa:

“An samu gagarumin ci gaba tun daga lokacin da rundunar ta fara gudanar da aikinta a ranar 1 ga watan Yulin 2025.”

A cewar Kwamishinan, an kafa rundunar ne bisa umarnin Sufeto-Janar na 'yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, na inganta tsarin aikin ƴan sanda da ya shafi al'umma.

Kara karanta wannan

Aminu vs Sanusi: Rikicin sarautar Kano na neman dawowa ɗanye, an aika saƙo ga Kotun Ƙoli

Nasarorin da aka samu karkashin Operation Kukan Kura

CP Ibrahim Bakori ya bayyana cewa daga taron manema labarai na ƙarshe a ranar 16 ga Yuni zuwa yau, an kama mutane 98 da ake zargi da hannu a cikin manyan laifuffuka 21.

Waɗanda aka kaman suna da alaka da fashi da makami, garkuwa da mutane, fataucin miyagun ƙwayoyi, satar ababen hawa, zamba, da kuma dabanci.

Ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan gudanar da samame na musamman a faɗin jihar, musamman a yankunan da ake yawan samun aikata laifuffuka.

'Yan sanda sun kwace miyagun makamai daban-daban da kuma abubuwan da ake zargin kayan sata ne ko kayan aikata laifuffuka.

'Yan sandan Kano sun fara cafke masu aikata miyagun laifuffuka ta shrin Operation Kukan Kura
Wasu daga cikin miyagun kwayoyi, baburan sata da wayoyin da 'yan sandan Kano suka kwato. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Abubuwan da rundunar ta kwato

Abubuwan da aka kwato sun haɗa da motoci shida na sata, keke-napep takwas, babura 10, wayoyin salula 13, batirin mota biyar, da kuma tayoyi uku.

Jami'ai sun kuma kwace haramtattun abubuwa da suka haɗa da sholisho 42, buhuna 35 da kunshi 1,123 na tabar wiwi, kwalabe 86 na madarar sukudai, fakiti 30 na kwayoyin Exol, da kuma fakiti 10 da guda 53 na kwayoyin diazepam.

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda sun gwabza fada da 'yan bindiga a Katsina, an rasa rayuka 36

Bugu da ƙari, an kwato adduna 16, wuƙake 98, da kuma dala $10,000 na kuɗin Amurka na jabu yayin gudanar da ayyukan.

CP Bakori ya sake jaddada aniyar 'yan sandan Kano na kare rayuka da dukiyoyi a faɗin jihar kuma ya yi kira da a ci gaba da ba da goyon baya daga jama'a.

Kalli hotunan a kasa:

'Yan Kano sun jinjinawa kokarin 'yan sanda

A zantawar Legit Hausa da wasu mazauna Kano, sun nuna matukar jin dadinsu da aka kafa wannan sabuwar runduna ta Operation Kukan Kura.

Abba Hassan Kano wanda ya yi magana da Legit Hausa a wayar tarho, ya ce:

'Ai Mallam Sani ina fada maka wannan ba karamin ci gaba ba ne, domin yanzu Kano tana nema ta zama dabdala ta 'yan daba da masu kwacen waya.
"Yanzu a Kano an kai kadamin da ba za ka iya yin yawo da wayarka a hannu a wasu anguwanni ba. Allah akwai anguwar da ko hasken waya aka gani a hannunka, sai an sare ka an karbeta.

Kara karanta wannan

Harin da aka kai Fadar Sarki Muhammdu Sanusi II ya ƙara tayar da ƙura a jihar Kano

"Akwai gadojin da aka yi, wadanda sun zama mafakar wadannan bata-garin. Ga kuma uwa uba masu sayar da kwayoyi, wadanda ke kara haukata mana matasa."

Abba Hassan ya ce yana fatan wannan runduna za ta zafafa ayyukanta a lungu da sako tare da hada kai da jama'ar gari, domin kusan an san duk wani mai aikata laifi, sai dai idan ba a so nuna shi ba.

An kama wanda ya jagoranci kashe DPO a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da kisan DPO na Rano, CSP Baba Ali, a yayin da yake bakin aikinsa a yankin.

Bayan binciken gaggawa, an cafke mutane 41 da ake zargi da hannu a kisan, ciki har da wanda ake zargi ya jagoranci aikata laifin.

Kwamishinan ‘yan sanda ya tabbatar da cewa za a tabbatar da hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aikin a kan lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com