Tashin hankali: Fulani Makiyaya Sun Bankawa Gidaje 100 Wuta, Mutum 1 Ya Mutu a Taraba

Tashin hankali: Fulani Makiyaya Sun Bankawa Gidaje 100 Wuta, Mutum 1 Ya Mutu a Taraba

  • Fulani makiyaya sun kai hari Taraba, inda suka kashe suka kona gidaje sama da 100 yayin da aka rahoto cewa mutum daya ya mutu
  • Wani shugaban matasa, ya tabbatar da harin makiyayan, yana mai cewa an sanar da jami'an tsaro tun da wuri amma ba a ɗauki mataki ba
  • Mazauna yankin sun yi hijira, kuma har yanzu suna ci gaba da ƙidaya asarar da suka yi, yayin da aka umarci mata da yara su da su gudu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Taraba – Wasu 'yan ta'adda da aka ce Fulani makiyaya ne sun kai mummunan farmaki a karamar hukumar Karim Lamido da ke jihar Taraba.

Makiyayan sun hallaka mutum daya yayin da suka cinnawa sama da gidaje 100 wuta, suka kone kurmus a harin da suka kai garin wasu manoma.

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda sun gwabza fada da 'yan bindiga a Katsina, an rasa rayuka 36

Fulani makiyaya sun kai hari Taraba, sun kona gidaje sama 100 yayin da mutum 1 ya mutu
Mutum 1 ya mutu yayin da makiyaya suna bankawa gida sama da 100 wuta a Taraba. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Makiyaya sun kai mummunan hari Taraba

Shugaban matasan yankin Bandawa Gwenzu, Ishaya Peter ne ya tabbatar da wannan farmaki a zantawarsa da Channels TV ta wayar tarho a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ishaya Peter ya shaida cewa makiyayan sun kai harin ne a daren Laraba a yankin na Bandawa Gwenzu, wanda ya ƙunshi ƙauyukan Gwenzu, Langwanshin, da Danzhan.

Ya bayyana cewa makiyayan sun farmaki manoman da ke zaune a wadannan garuruwan ba tare da wani dalili ba, inda suka ci karen su ba babbaka na tsawon awanni.

A cewarsa, mazauna yankin suna zaune suna tattaunawa lokacin da suka ji karar harbe-harbe daga nesa ba zato ba tsammani, lamarin da ya sa suka ruga domin tsira da rayukansu.

Jami'an tsaro ba su iya kai dauki ba

Ishaya Peter ya bayyana cewa ya ji muryoyin makiyaya yayin da suke ke tunkaro ƙauyen su, kuma duk yunƙurin da suka yi na dakile harin ya ci tura.

Kara karanta wannan

Bayan zargin badakala, Peter Obi ya fadi alakar da ta hada shi da Abacha

Shugaban matasan ya ce sun sanar da jami'an tsaro sa'o'i da dama kafin kai harin, amma ba a ɗauki mataki ba don kauce wa faruwar lamarin.

“Ba mu iya dakile harin ba saboda sun zo dauke da manya bindigogi, mu kuma mutane ne masu son zaman lafiya, ba mu mallaki irin wadannan makamai ba, iyakar mu baka da kibau, da adduna, shi ke nan.”

- Ishaya Peter.

Mazauna garuruwan Karim Lamido sun tsere daga gidajensu bayan harin makiyaya
Har yanzu 'yan sandan Taraba ba su fitar da sanarwa game da harin da makiyaya suka kai Karim Lamido ba. Hoto: @KanoPoliceNG
Source: Twitter

Mutum 1 ya mutu sanadiyyar farmakin

Ya ci gaba da cewa:

“Mutum daya daga cikin mu da ya mutu. Ya mutu ne saboda bai iya iyo ba a lokacin da muke ƙetare kogin garin, yayin da suka kawo mana hari. Mun bar gidajensu yanzu, kuma mun rasa kadarori masu yawa.
“An umurci mata da yara su bar ƙauyukan saboda ba mu san lokacin da za su sake kai hari ba, ko kuma inda za su kai harin.”

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, rundunar 'yan sandan jihar Taraba ba ta ce komai ba game da wannan sabon harin.

Idan za a iya tunawa, irin wannan lamarin ya faru a yankin Bandawa a watan Mayun wannan shekarar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 3 tare da raunata da yawa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An harbe sojan Najeriya har lahira a Kogi, an samu karin bayanai

Rikici ya barke tsakanin makiyaya da manoman Taraba

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a jihar Taraba.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan wasu makiyaya sun kai hari a wasu yankuna, inda suka kashe mutane 10 da ba su da wata alaƙa da rikicin.

Biyo bayan harin, wasu matasa sun kutsa cikin daji suka kai hari kan wasu makiyaya da ke kiwon shanunsu, inda suka kona su kurmus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com