NiMet: Za a Sha Ruwa da Iska Mai Karfi a Kano, Yobe da Jihohi 24 a Ranar Alhamis
- Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a fuskanci tsawa, ruwan sama da iska mai ƙarfi Arewada yankin Kudu a ranar Alhamis
- Jihohin Bauchi, Kano, Kaduna, Yobe za su fuskanci ruwan sama mai ƙarfi da iska mai karfi, yayin da ruwa mai yawa zai sauka a Kudu
- NiMet ta gargadi al’umma da su kasance cikin shiri saboda yiwuwar ambaliya, rushewar gine-gine da tsaikon zirga-zirgar ababen hawa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na ranar Alhamis, 10 ga watan Yulin 2025.
A cikin rahoton, NiMet ta yi hasashen cewa yawancin sassan Najeriya za su samu ruwan sama mai yawa tare da tsawa da iska mai ƙarfi a ranar Alhamis.

Source: Original
A rahoton da ta wallafa a shafinta na X, NiMet ta yi gargadi ga jama'a da su kasance cikin shiri domin akwai yiwuwar ambaliyar ruwa, iska mai ƙarfi, wacce za ta iya jawo rushewar gidaje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar hasashen yanayin, wacce NiMet ta fitar a ranar 9 ga Yulin 2025, ta bayyana cikakken yanayin ruwa da ake sa ran samu a jihohin Arewa, da Kudu.
Arewa: Tsawa, ruwan sama da iska mai karfi
A safiyar ranar Alhamis, ana sa ran za a samu tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a sassan jihohin Taraba, Adamawa, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Jigawa, Yobe, da Bauchi.
Amma ana sa ran sauran jihohn za su fuskanci haduwar hadari da kuma hudowar rana, wanda ba lallai hadarin ya zubar da ruwa ba.
Da yamma zuwa dare kuwa, ana sa ran ruwan sama mai karfi zai sauka tare da tsawa da iska mai ƙarfi a jihohin Bauchi, Kaduna, Adamawa, Taraba, Gombe, Kano, Katsina, Jigawa, Yobe, da Borno.
Hasashen yanayi a jihohin Arewa ta tsakiya
A safiyar ranar Alhamis a jihohin Arewa ta Tsakiya, NiMet ta yi hasashen cewa za a samu tsawa tare da ɗan ruwan sama a sassan jihohin Nasarawa, Babban Birnin Tarayya (FCT), Plateau, da Niger.
Da yamma zuwa dare kuwa, ana sa ran tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a Abuja, Nasarawa, Kogi, Kwara, Benue, Niger, da Plateau.

Source: Getty Images
Jihohin Kudu: Ruwan sama mai yawa
NiMet ta yi hasashen cewa za a samu haduwar hadari tare da saukar ruwan sama a jihohin Ogun, Ondo, Lagos, Bayelsa, Cross River, da Akwa Ibom a safiyar Alhamis.
Amma ana sa ran za a samu ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi, wanda zai dade yana zuba a yawancin sassan yankin kudancin ƙasar da yamma har zuwa dare.
Gargadin hukumar NiMet ga 'yan Najeriya
NiMet ta shawarci jama'a da su kasance cikin shirin yiwuwar ambaliyar ruwa, da kuma rushewar gidaje sakamakon tsawa da iska mai karfi.
Hukumar ta buƙaci 'yan Najeriya da su ɗauki matakan kariya da kuma guje wa wuraren da ke da haɗarin ambaliyar ruwa.
Matsalar ambaliya a Arewacin Najeriya
Yayin da hukumar NiMet ke ci gaba da hasashen ruwan sama mai ƙarfi a sassan Arewa da Kudu, dama na kara bayyana game da tasirin ambaliya da ake fuskanta musamman a jihohin Arewa.
Jihohi irin su Bauchi, Jigawa, Yobe da Borno sun riga sun fara fuskantar ambaliyar ruwa a wasu yankuna, wanda ke barazana ga rayuka, kadarori da ababen more rayuwa.
A wasu kauyuka a jihar Jigawa da Bauchi, ruwan sama mai ƙarfi ya jawo ambaliya da ta lalata gidaje, gonaki da hanyoyi, inda mazauna yankunan ke kira ga gwamnati da ta kawo agajin gaggawa.
A Kano da Kaduna, an samu tsaikon zirga-zirga da faduwar bishiyoyi da ke kan tituna sakamakon iska mai ƙarfi da tsawa.
Masana sun ce wannan matsala na da alaƙa da rashin tsarin magudanan ruwa da kuma gine-gine a wuraren da bai kamata ba.
NiMet ta bukaci jama'a da su guji wuraren da ke da haɗarin ambaliya da kuma kiyaye bin dokokin kariya yayin da damina ke ƙaruwa.
Ruwan sama da ake sa ran zai ci gaba da zuba a makonni masu zuwa na iya ƙara tsananta matsalolin ambaliya, musamman a Arewa, idan ba a ɗauki mataki ba.
Jihohin da za a samu ambaliya a Yulin 2025
A wani labarin, mun ruwaito cewa, NiMet ta yi gargaɗi game da yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohi 20 a watan Yuli 2025, inda ta bayyana Sokoto a matsayin jiha mai matsanancin haɗari.

Kara karanta wannan
Sokoto, Kaduna da jihohin Arewa 8 za su fuskanci ruwan sama da tsawa a ranar Laraba
Cikin jerin da hukumar ta fitar, an haɗa da Kaduna, Zamfara, Yobe da sauran jihohi 16 da za su iya fuskantar ambaliya sakamakon ruwan sama mai yawa a wannan wata.
NiMet ta shawarci jama’a da su tsaftace magudanan ruwa, guje wa tuki a lokacin ruwan sama, da kuma barin wuraren da ke da haɗarin kamuwa da ambaliya.
Asali: Legit.ng


