Sojoji, Ƴan Sanda Sun Gwabza Faɗa da Ƴan Bindiga a Katsina, An Rasa Rayuka 36

Sojoji, Ƴan Sanda Sun Gwabza Faɗa da Ƴan Bindiga a Katsina, An Rasa Rayuka 36

  • Jami’an tsaro sun kashe akalla ’yan bindiga 30 a Faskari yayin musayar wuta da suka yi da daruruwan ’yan ta’adda da suka kai
  • An ce jami'an sun yi musayar wuta da 'yan ta'addar a kokarin dakilen harin da suka kai garuruwan Kadisau, Raudama, da Sabon Layi
  • Gwamnatin Katsina ta bayyana cewa sojoji biyu, jami’an ’yan sanda uku da wani farar hula sun rasa rayukansu yayin wannan artabun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina – Jami’an tsaro sun kashe aƙalla ƴan bindiga 30 a yayin wani artabu da suka yi a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

A cikin wata sanarwa, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Dakta Nasir Mua’zu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 8 ga Yuli da misalin karfe 5:00 na yamma.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fitar da N7.7bn, zai siyo jiragen sama masu gano maɓoyar ƴan bindiga

Jami'an tsaro sun hallaka 'yan ta'adda 30 a musayar wutar da suka yi a Faskari, jihar Katsina
Dakarun sojojin Najeriya yayin da suka rangadin tsaro a wani yanki na kasar. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jami'an tsaro sun gwabza fada da 'yan bindiga

Sai dai, ya bayyana alhininsa kan cewa sojoji biyu da jami'an ƴan sanda uku, tare da wani farar hula, sun rasa rayukansu yayin musayar wutan, inji rahoton The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa wani mutum guda, wanda ake zaton jami'in hukumar tsaron Katsina ne ya samu raunuka kuma a halin yanzu yana karɓar kulawar likita a asibiti.

Dakta Nasir Mua’zu ya bayyana cewa:

"Jami'an tsaro da suka haɗa da ƴan sandan PMF, sojojin kasa, da na sama, sun fafata da ɗaruruwan ƴan bindiga da ke dauke da miyagun makamai.
"Jami'an sun yi musayar wuta da 'yan ta'addar a kokarin dakilen harin da suka kai garuruwan Kadisau, Raudama, da Sabon Layi da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar 8 ga Yuli, 2025."

An kashe 'yan bindiga 30 a Faskari, Katsina

Bayan samun bayanan sirri game da waɗannan hare-hare, kwamishinan ya ce an tura jami'an tsaron domin su kai daukin gaggawa ga mazauna garuruwan.

Kara karanta wannan

An kama ɗan shekara 25 ɗauke da nonon mace, ƴan sanda sun yi ƙarin bayani

Ya kuma ce an tura karin jami'an tsaro da aka girke a Dandume da kuma taimakon rundunar sojin saman Najeriya, kuma sun garzaya inda 'yan bindigar suke.

"Bayan fafatawa mai tsanani, jajirtattun jami'an tsaronmu sun yi nasarar fatattakar maharan, inda suka tilasta musu ranta wa a na-kare.
"An kashe 30 daga cikin masu maharan ta hanyar haɗin gwiwar hare-haren sama yayin da suke ƙoƙarin tserewa."
Sojojin Najeriya, 'yan sanda da wani farar hula sun mutu a musayar wuta da 'yan bindiga a Katsina
Wasu sojojin Najeriya da suke aikin kakkabe 'yan bindiga a Arewacin kasar. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji, 'yan sanda sun mutu a Katsina

Yayin da ake murnar jarumtakar jami'an tsaron, Dakta Nasir Mua’zuya ce:

"Muna cike da jimami na rasa wasu daga cikin jami'an tsaronmu, waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen kare garuruwanmu.
"Mun rasa jami'an ƴan sanda uku, da suka hada da: Sufeto Suleiman Ibrahim, Sufeto Bello Bala, da Corporal Mohammed Lawal, tare da wani farar hula, Aliyu Sa’adu dan kauyen Kadisau.
"A Sabon Layi, jajurtattun sojoji biyu sun sadaukar da rayukansu, yayin da Ya’u Aliyu ya samu raunuka kuma a halin yanzu yana karɓar kulawar likita."

An rasa rayuka a fadan sojoji da 'yan ta'adda

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dakarun sojin Najeriya sun kutsa wani daji a Katsina inda suka yi kazamin artabu da ’yan ta’adda masu dauke da muggan makamai a maboyarsu.

Kara karanta wannan

Kisan Danbokolo: Abin da al'umma suka shirya saboda tsoron abin da ka iya biyo baya

A yayin artabun, sojojin sun hallaka da dama daga cikin ’yan ta’addan tare da kwato bindigogi da wasu kayan aiki da suka saba amfani da su wajen kai hari.

Bayan fatattakar sauran ’yan ta’addan zuwa cikin daji, dakarun sun lalata sansanin da suka gina domin hana komawar su da sake kai hare-hare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com