Bauchi: Sarakuna Sun Aika Sako ga Magoya baya kan Shirin Kirkirar Sababbin Masarautu
- Majalisar sarakunan Bauchi ta bayyana damuwa a kan labarin cewa wasu na shirin tayar da hankula a jihar Kano kirkirar sababbin masarautu
- Wannan na kunshe a cikin sanarwar da mai martaba Sarkin Bauchi kuma shugaban majalisar sarakuna, Rilwanu Suleiman Adamu ya fitar
- Ya umarci jama'a a kan su rika bayyana damuwarsu ta hanyoyin da ba za su kawo fitina ko hana zaman lafiya da hargitsa al'umma ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi – A yayin da gwamnatin jihar Bauchi ke shirin kirkirar sababbin masarautu, sarakunan gargajiya na jihar sun bukaci jama’a da su zauna lafiya.
Wannan na zuwa ne bayan an samu rahotannin cewa akwai masu shirin tayar da hayaniya a kan shirin yiwa masarautun kishiya.

Source: Facebook
Leadership News ta wallafa cewa kiran na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai martaba Sarkin Bauchi kuma shugaban majalisar sarakuna, Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu, ya fitar a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarakunan Bauchi sun nuna damuwa
Sanarwar ta bayyana damuwar majalisar kan zargin cewa wasu 'yan kasa marasa kishin kasa na shirin tayar da zaune tsaye domin kawo cikas ga wannan yunkuri na gwamnati.
Sanarwar ta ce:
"Ya kamata a fahimta cewa wasu na shirin tayar da hankula da nufin kawo cikas ga wannan shiri. Mun lura da fadi-tashi da ra’ayoyi masu yawa dangane da batun, wasu na goyon baya yayin da wasu ke adawa, da hakan."
Majalisar ta sarakuna ta jaddada cewa lamarin kirkirar sababbin masarautu da gundumomi ya rataya ne a wuyan gwamnati.

Source: UGC
A cewar sanarwar Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu:
“Ya zama dole bangarori daban-daban su mutunta, su kuma bin duk wani mataki da gwamnati ta dauka, domin tabbatar da maslahar jihar."
Sarakunan Bauchi sun shawarci magoya baya
Sarakunan sun shawarci jama’a da su mika duk wata damuwa ko shawara da suke da ita ga kwamitin da aka samar domin kula da wannan aiki ta hanyar da ta dace.
Sun kara da bayyana cewa:
“Abin da muke bukata shi ne tattaunawa mai ma’ana da hadin kai. Ta haka ne kawai za mu samu cigaba da daidaito a tsakaninmu,” in ji Sarkin Bauchi.
Majalisar ta bukaci jama'a da su bayar da gudummawa wajen samar da yanayi mai kyau da kwanciyar hankali da ci gaba da morar zaman lafiya a jihar Bauchi.
Fulani sun bijirewa gwamnan Bauchi
A baya, mun wallafa cewa kungiyar Fulani mai suna Daddo Pulaku ta bayyana ƙin amincewarta da shirin gwamnatin jihar Bauchi na ƙirƙirar sababbin masarautu.
A yayin wani taro da aka gudanar a Bauchi, kungiyar ta ce babu wani ɗan Fulani ko ƙungiyarsu da za a tilasta wa karɓar sabon tsarin sarauta ba tare da yardarsu ba.
Mai magana da yawun kungiyar, Aminu Tukur, ya ce wannan matsaya ta fito ne daga dattawa, malamai, masu sarauta, matasa da kuma shugabannin Fulanin jihar.
Asali: Legit.ng

