Dangote Zai Samu Kishiya, Wani Kamfani Zai Gina babbar Matatar Man Fetur a Najeriya
- Kamfanin BINL zai gina matatar mai da za ta rika tace ganga 500,000 a kullum, sannan zai gina kasuwar cinikayya ta FTZ a jihar Ondo
- BINL ya yi hadin gwiwa da gwamnatin Ondo domin gina matatar a kan kudi $15b, yayin da za a kammala matakin farko a watanni 38
- Kamfanin ya bayyana cewa aikin zai rage gibin cinikayya, bunkasa tattalin arziki, samar da ayyuka, da kuma inganta rayuwar al’umma
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - Kamfanin Backbone Infrastructure Nigeria Limited (BINL) zai gina sabuwar matatar mai ta dala biliyan 15, sannan zai gina katafariyar kasuwar cinikayya, duk a a jihar Ondo.
Matatar da BINL zai gina a filin shakatawa na Sunshine da ke Ogboti, Eruuna, za ta tace ganga 500,000 a kullum, sannan zai gina kasuwar FTZ a karamar hukumar Ilaje, jihar Ondo.

Source: Getty Images
BINL zai gina matatar $15b a Ondo
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ga jaridar The Nation a ranar Laraba, an bayyana cewa wannan aiki hadin gwiwa ne da gwamnatin jihar Ondo ta hannun hukumar ONDIPA.
Ana sa ran za a kammala matakin farko na gina matatar man a cikin watanni 48, yayin da aka ce aikin gina matatar zai lakume dala biliyan 15.
Kamfanin BINL yana kan tattaunawa da NNPCL domin hada hannu wajen tabbatuwar ginin wannan babar matatar mai ta zamani.
Hakanan, kamfanin zai kai wa gwamnan Ondo, Hon. Lucky Aiyedatiwa, ziyarar ban girma a ranar 14 ga Yuli, 2025, yayin da za a rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar a ranar 15 ga Yuli, 2025.
Tasirin gina matatar ga Najeriya
BINL, wanda ke da ofisoshi a Abuja, London da Zug, ya bayyana cewa za a fara aikin ne da gina matatar mai mai fitar da ganga 100,000 a kullum.
Mataimakin shugaban kamfanin, Wale Adekola, ya ce matatar za ta samar da man da za a rika amfani da shi a gida, da kuma albarkatun mai ga masana’antu da kasuwannin duniya.
Aikin zai haɗa da gina manyan hanyoyi, tankunan ajiyar mai, filayen lodin mai, tashoshi da sauran kayayyakin aikin matatar.

Source: Getty Images
Shirin da BINL ya yiwa mazauna Ondo
Ayyukan gina babbar kasuwar cinikayyar kuwa za su haɗa da samar da kayayyakin more rayuwa domin gudanar da kasuwanci da tafiyar da harkoki bisa ka’ida.
Adekola ya ce wannan aiki zai taimaka wajen rage gibin cinikayyar Najeriya, adana kudaden musaya, karawa gwamnati kudin shiga da bunkasa tattalin arziki.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa za a samar da guraben ayyuka, kara kasuwanci da bunkasa rayuwar al’umma.
Kamfanin ya bullo da wani shiri na CSR, inda zai rika ke ba da tallafin ilimi ga mazauna yankunan da zai yi aikin, nema masu guraben aiki da kuma inganta kayayyakin more rayuwa.
Za a gina sababbin matatun mai 3 a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta amince da gina sabbin matatun mai guda uku domin ƙara ƙarfin tace danyen mai zuwa ganga 140,000 a kowace rana.
Hukumar kula da harkokin man fetur (NMDPRA) ta bayyana cewa ƙarin matatun zai taimaka matuƙa wajen tabbatar da isasshen man fetur a cikin gida ba tare da dogaro da waje ba.
Kamfanonin Eghudu, MB Refinery da HIS Refining ne suka samu lasisin gina matatun a jihohin Edo, Delta da Abia domin ƙarfafa fannin tace mai a Najeriya.
Asali: Legit.ng


