Za a gina matatar man fetur a Garin Shugaban Kasa

Za a gina matatar man fetur a Garin Shugaban Kasa

- Za a gina wani matatar man fetur a cikin Jihar Katsina

- Ana dai sai rai matatar za ta dauki mutum da dama aiki

- ‘Yan kasuwa su ka zo da wannna tsari a Arewacin kasar

Mun samu labari cewa ana shirin gina wani matatar man fetur a Jihar Katsina. Talban Katsina watau Zakari Ibrahim ne zai bude wannan katafaren matata zai yi wa jama'a hanyar samun abinci.

Za a gina matatar man fetur a Garin Shugaban Kasa

Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari CFR

Alhaji Zakari Ibrahim mai kamfanin man nan na Blak Oil Energy Refinery ne zai gina matatar mai a Garin Mashi wanda ke cikin Jihar Katsina. Kamar yadda labari ya zo mana, babu ruwan Gwamnati da hannu cikin kamfanin.

KU KARANTA:

Ana kiyasin cewa za a kashe Dala Biliyan 2 watau sama da Naira Biliyan 700 wajen bude wannan katafaren kamfani wanda zai dauki sama da mutum 2500 aiki a nan take. Wasu mutum fiye da 10,000 za su samu hanyar cin abinci a nan.

A yau ne aka sa hannu kan wannan yarjejeniya lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da Takwaran sa na Kasar Jamhuriyar Nijar watau Shugaba Moumadou Issoufou a cikin fadar Shugaban kasa na Aso Villa da ke Abuja.

Gwamnatin Buhari na kokarin jawo man fetur daga Kasar Nijar zuwa Jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya. Ma’aikatar harkar man fetur ta Najeriya ce ta bayyana wannan a wata takarda da ta fitar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel