Gwamnati na Shirin Kara Kudin Wutar Lantarki, 'Yan Najeriya Sun Dura kan Tinubu

Gwamnati na Shirin Kara Kudin Wutar Lantarki, 'Yan Najeriya Sun Dura kan Tinubu

  • Ministan wuta, Adebayo Adelabu ya ce gwamnati za ta sauya tsarin biyan kuɗin wuta don dakatar da ƙaruwar bashin Naira tiriliyan hudu
  • Wannan matakin zai kawo ƙarshen tallafin wuta, wanda hakan zai haifar da ƙarin kuɗin wutar ga kowa, duk da rashin samar da wuta a kasar
  • Ƴan Najeriya sun fusata kan shirin ƙarin kuɗin ba tare da gwamnatin taraya ta inganta samar da wuta ba, suna ganin hakan zai cutar da al'umma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce gwamnati na shirin sauya tsarin biyan kudin wuta domin dakile karuwar bashin N4trn da ake bin kamfanonin wutar lantarki.

Adebayo Adelabu ya ce wannan matakin yana daga cikin gyare-gyaren da za su tabbatar da dorewar bangaren wuta da kuma jawo jari daga masu zuba hannun jari.

Kara karanta wannan

Bayan zargin badakala, Peter Obi ya fadi alakar da ta hada shi da Abacha

Gwamnatin tarayya ta ce za ta sabunta tsarin biyan kudin wuta wanda hakan zai iya jawo karin kudin wuta
Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na shirin sauya tsarin biyan kudin samar da wuta. Hoto: @PBATMediaCentre/X
Source: Getty Images

Ministan wutar lantarkin ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki na Mission 300 da aka gudanar a Abuja, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin gwamnati zai jawo karin kudin wuta

Duk da karin kudin wutar lantarki da aka yi wa 'yan rukunin Band A, jama’a sun koka kan karancin wuta da kuma ci gaba da biyan kudin na’urorin da ba sa aiki yadda ya kamata.

Sai dai, Adebayo Adelabu ya jaddada cewa daukar wannan matakin yana da matukar muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

“A halin yanzu, akwai babban bashi da ake bin kamfanonin samar da wuta na tallafin da gwamnati ba ta biya ba, wanda ya kai kusan N4trn a watan Disambar 2024.
“Gwamnati ta fara shirin rage wannan bashi da kuma dakatar da kara tara sabon bashi nan gaba, ta hanyar sauya tsarin biyan kudin samar da wuta."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An harbe sojan Najeriya har lahira a Kogi, an samu karin bayanai

- Adebayo Adelabu.

Wannan sauyi na nufin cewa gwamnatin za ta daina biyan tallafi a bangaren wuta gaba ɗaya, wanda hakan ka iya janyo karin kudin wuta ga kowa da kowa.

Gwamnati ta dauki kudurin gyara fannin wuta

Rahoto ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kashe N1.1bn a matsayin tallafin wuta cikin watanni shida na shekarar 2025, wanda hakan ya kara yawan bashin zuwa N5trn.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bolaji Tunji, ya fitar, Adelabu ya ce gwamnati za ta mai da hankali wajen farfado da cibiyoyin samar da wuta da ba sa aiki.

Hakazalika, ya ce gwamnati za ta fadada hanyoyin samar da makamashi domin tabbatar da isasshiyar wuta, musamman ta hanyar hanyoyin makamashi masu tsafta da araha.

Ya bayyana muhimman abubuwan da gwamnati za ta mayar da hankali a kai cikin gyaran bangaren wuta, ciki har da tabbatar da dakile yawaitar lalacewar tushen wuta.

Kara karanta wannan

Kano: Ƴan sanda sun fara binciken rikicin magoya bayan Sanusi II da Aminu Ado Bayero

Adebayo Adelabu, ministan wuta ya ce gwamnati na daukar matakin gyara wuta da samar da ita a kasa
Ministan wutar lantarki da makamashi, Mista Adebayo Adelabu. Hoto: @federal_power
Source: UGC

‘Yan Najeriya sun dura kan Tinubu

'Yan Najeriya sun yi martani mai zafi ga gwmnatin Shugaba Bola Tinubu kan kalaman ministansa game da yiwuwar karin kudin wutar lantarki.

Shugaban ƙungiyar kare hakkin masu amfani da kayayyaki a Najeriya, Kunle Olubiyo, ya ce yiwuwar ƙarin farashi ba tare da samar da wuta ba, na nufin rasa masu amfani da wutar.

Ya bayyana cewa ba a samu ci gaba a fannin samar da wuta, gine-ginen layukan wuta, ko inganta hanyoyin rabawa ba, duk da gwamnati ta nunka kudin 'yan Band A a shekarar da ta wuce.

Abubakar Aliyu, wani mai amfani da wuta daga rukunin Band C da ke zaune a Gwagwalada, ya bayyana cewa yana samun kasa da awanni 6 na wuta a kullum, wasu ranakun kuma garin su gaba ɗaya yana cikin duhu.

Ya ce duk wani ƙarin farashi dole ne ya zo da ƙarin samar da wuta, amma yana kokonto ko kamfanonin rarraba wuta (DisCos) suna da ƙarfin yin hakan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya rufe bakin ƴan adawa, ya faɗi abin da ake yi da kudin tallafin man fetur

“Kamar raba wutar suke yi tsakanin unguwa da unguwa, domin tana yawan yanke wa kuma ana samun sauyin lokutan da suke bayar da ita.
"Wannan mataki zai cutar da jama’a matuƙa, duba da yadda kamfanonin ke da rauni wajen ba da wuta da gyaran na’urorin.
"Ko da ace gwamnati na shirin ƙarin farashin kudin wutar, to ya kamata a tabbatar da komai ya daidaita, musamman ta fuskar wadatuwar wutar."

- Abubakar Aliyu.

Gombe: Wutar lantarki ta kashe jami'in gwamnati

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wutar lantarki ta zama sanadiyyar mutuwar wani babban sakatare a gwamnatin Gombe tare da wasu mutane huɗu a unguwar Tudun-Wadan Pantami.

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da afkuwar lamarin, wanda ya faru bayan an kawo wuta mai ƙarfi da safiyar Asabar, 14 ga watan Yuni, a birnin Gombe.

Kwamishinan ƴan sanda ya yi alhinin mutuwar mutanen tare da tabbatar da cewa za a gudanar da bincike mai zurfi don gano musabbabin lamarin da kuma ɗaukar matakin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com