Dangote Ya Zaftare Farashi, Ya Fitar da Sabon Kudin Man Fetur a Najeriya
- Matatar Dangote ta rage farashin litar man fetur daga N840 zuwa N820 saboda saukar farashin danyen mai a kasuwar duniya
- Sauran kamfanonin man fetur sun bi sahun matatar Dangote wajen saukar da farashin domin fafatawa a kasuwa
- Saukar farashin na zuwa ne bayan yakin kwana 12 da aka yi tsakanin Isra’ila da Iran ya lafa, wanda ya rage darajar danyen mai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Matatar Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga N840 zuwa N820, a wani mataki na daidaita farashi da yanayin kasuwar cikin gida da ketare.
Rahotanni sun bayyana cewa saukar farashi ya biyo bayan faduwar farashin gangar danyen mai a kasuwar duniya daga $77 a watan Yuni zuwa $70 a yanzu.

Kara karanta wannan
Kano: Ƴan sanda sun fara binciken rikicin magoya bayan Sanusi II da Aminu Ado Bayero

Source: Getty Images
Legit Hausa ta gano cewa matatar Dangote ce ta fitar da sabon farashin a wani sako da kamfanin Dangote ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan matakin na Dangote ya sanya sauran kamfanoni da ke rarraba man fetur a Najeriya su ma suka daidaita farashinsu domin gujewa asara da rasa masu saye.
Farashi: Kamfanoni sun bi sahun Dangote
Rahoton da Vanguard ta fitar ya nuna cewa matatar Dangote ce ta fi sauke farashi tsakanin sauran kamfanonin mai.
Kamfanin Fatgbems ya saukar da farashin daga N838 zuwa N837 a lita, yayin da Integrated da Bovas suka daidaita farashinsu zuwa N836 daga N837.
A daya bangaren kuwa, AIPEC ya sauko daga N840 zuwa N837, sai kuma First Royal da ya sauya farashin zuwa N838.
Masana harkar fetur sun bayyana cewa wadannan sauye-sauyen farashi na nuna yadda manyan ‘yan kasuwa ke daidaita kansu da sauyin farashin danyen mai a kasuwar duniya.
Saukar farashi na baya-bayan nan
A cikin makonni da suka gabata, matatar Dangote ta saukar da farashin litar man fetur a matakin tashar daukar kaya daga N880 zuwa N840.
Rahotanni sun nuna cewa saukin da aka samu da ya kai 4.5% na da nasaba da faduwar farashin danyen mai zuwa $67.50 daga fiye da $70 a kasuwannin duniya.

Source: Getty Images
A cewar wani masani mai bibiyar harkar fetur, Olatide Jeremiah, faduwar farashin man a duniya ya samo asali ne daga kawo karshen yaki da aka yi tsakanin Isra’ila da Iran.
Ya kara da cewa ana sa ran karin saukar farashi a makonni masu zuwa idan yanayi ya ci gaba da daidaituwa.
Matakin na Dangote na iya taimakawa wajen saukaka wa ‘yan Najeriya radadin hauhawar farashin fetur da ake fama da shi a baya-bayan nan.
Za a yi taron daidaita farashin fetur
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta amince da taro na musamman domin ganin an samu nasara wajen daidaita farashin man fetur a Najeriya.
Rahoton da Legit Hausa ta samu ya tabbatar da cewa za a shafe kwana biyu ana tattaunawa da masana harkai mai a taron.
Bayanai da gwamnati ta fitar sun nuna cewa za a yi taron ne sakamakon korafin da 'yan kasuwa ke yi kan rashin daidaito wajen rage kudin mai a Najeriya.
Asali: Legit.ng

