Gwamna Abba Ya Ɗauko Mai Martaba Sarkin Lafiya, Ya ba Shi Shirgegen Muƙami a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Mai Martaba Sarkin Lafiya, Sidi Muhammad Bage a matsayin Shugaban Jami'ar Northwest ta Kano
- Sarkin dai tsohon alkali ne wanda ya yi aiki a kotun kolin Najeriya kafin ya koma masarautar Lafiya da ke jihar Nasarawa
- Abba Kabir ya bayyana cewa wannan naɗi zai kawo ci gaba ga Jami'ar duba da tarihin Sarkin na rikon gaskiya, adalci da kishin al'umma
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗa Mai Martaba Sarkin Lafia, Sidi Muhammad Bage, a matsayin sabon Shugaban Jami’ar Northwest (Chancelor).
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin.

Source: Facebook
A sanarwar da ya wallafa shafinsa da Facebook jiya, ya ce gwamnan ya naɗa basaraken ne domin karfafa danganta tsakanin sarakuna da cibiyoyin ilimi.

Kara karanta wannan
Rikicin sarauta: Gwamnatin Kano ta fito ta fayyace abin da ya faru a Fadar Sanusi II
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Masu ruwa da tsaki sun yaba wa wannan mataki domin suna ganin zai ƙarfafa dangantaka tsakanin masarautun gargajiya da manyan makarantu a Najeriya," in ji Sanusi Bature.
Taƙaitaccen tarihin Sarkin Lafiya na Nasarawa
An haifi Sarki Sidi Bage a ranar 22 ga Yuni, 1956, a Lafia, Jihar Nasarawa. Ya samu difloma da digirin lauya (LLB) daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma zama cikakken lauya a Najeriya a 1981.
Ya fara aikinsa na shari’a a matsayin Alƙali a 1982, sannan aka naɗa shi a matsayin Mai Shari’a na Babbar Kotun Jiha a 1992.
Daga nan ya hau kujerar Kotun Daukaka Ƙara a 2007, kafin daga bisani a naɗa shi a matsayin Alƙalin Kotun Ƙoli ta Najeriya a watan Janairu 2017.
A watan Maris na 2019, bayan rasuwar Sarki Isa Mustapha Agwai I, aka naɗa shi a matsayin Sarki na 17 na masarautar Lafia.
Tun daga lokacin ya kasance shugaba nagari mai riko da gaskiya, zaman lafiya da haɗin kai a cikin al’umma.
Wannan naɗi ya nuna cewa Jami’ar Northwest, Kano, za ta ci gaba da samun jagorori masu nagarta da ƙwarewa domin rike mukaman shugabanci da na ba da shawara.

Source: Facebook
Gwamna Abba na fatan naɗin zai kawo ci gaba
Gwamna Abba ya jaddada cewa naɗa tsohon Alƙalin Kotun Ƙoli kuma Sarki Mai Daraja da ake girmamawa, alama ce ta cewa jami’ar za ta ci gaba ta kowane fanni.
Gwamnan ya kuma bayyana tarihin basaraken na shugabanci mai cike da adalci, kishin al’umma da kwarewa, siffofi da ake sa ran za su ɗaga jami’ar, tare da ɗora ta kan hanyar nasarori.
Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar, Farfesa Hafiz Abubakar, ne ya miƙa takardar naɗin a hannun Sarkin a ranar Litinin, tare da Shugaban Jami’ar (VC), Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa.
Gwamna Abba ya naɗa sababbin hadimai 19
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin ƙarin manyan mataimaka na musamman (SSA) 19 a gwamnatinsa.
Wannan nade-naɗe na daga cikin matakan da Gwamna Abba ke dauka domin ƙara ƙarfafa shugabanci da kokarin isar da ayyuka ga al'ummar Kano.
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana kyakkyawan fata cewa sababbin hadiman za su yi amfani da gwanintarsu da kuma kwazonsu wajen sauke hakkin da ke kansu.
Asali: Legit.ng
