Kano: Ƴan Sanda Sun Fara Binciken Rikicin Magoya bayan Sanusi II da Aminu Ado Bayero

Kano: Ƴan Sanda Sun Fara Binciken Rikicin Magoya bayan Sanusi II da Aminu Ado Bayero

  • An samu hatsaniya a tsakanin magoya bayan Aminu Ado Bayero da na Khalifa Muhammadu Sanusi II a Kano
  • Lamarin da ya haifar da raunuka da lalata dukiyoyi, duk da dai ba a kai ga samun asarar rayuka ba yayin hatsaniyar
  • Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin rikicin da kuma daukar mataki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Rundunar ƴan sanda ta jihar Kano ta kafa wani kwamitin bincike don gano abin da ya jawo hatsaniyar da ta faru a unguwar Kofar-Kudu da ke cikin birnin Kano.

Wannan na zuwa ne bayan rikici da ya barke tsakanin magoya bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, da na Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi magana kan rigimar da ta faru a fadarsa da Aminu Ado ya zo wucewa

Alhaji Aminu Ado Bayero da Khalifa Muhammadu Sanusi II
An samu hatsaniya a Kano Hoto: Masarautar Kano/Sanusi II Dynasty
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hatsaniyar da aka samu a fadar Sarkin Kano

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a yayin wannan hatsaniya, an samu bayanan lalata kofar fada tare da kai wa masu gadi hari.

Rahoton ya kara da cewa wasu daga cikinsu sun ji rauni, sannan an fasa wasu motocin ƴan sanda da ke cikin harabar fadar.

Da yake karin bayani, SP Haruna ya ce:

"Kwamishinan ƴan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ya kafa kwamitin bincike kan wannan hatsaniya."

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a karshen mako lokacin da Aminu Ado Bayero, da tawagarsa suka yi ƙoƙarin wucewa ta yankin daga gidan Mandawari zuwa fadar Nassarawa.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a karshen mako lokacin da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, da tawagarsa suka yi ƙoƙarin wucewa ta yankin daga gidan Mandawari zuwa fadar Nassarawa. Sai dai wasu da ake kyautata zaton magoya bayan Muhammadu Sanusi II ne suka tare su, lamarin da ya jawo rikicin.

Kara karanta wannan

Rashin biyayya: An umarci masoyan Aminu Ado su fice daga gidan Sarki Sanusi II

Ƴan sanda sun kai dauki fadar Sarki

A cewar wani ganau, ƴan sanda sun gaggauta harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa matasa masu tada zaune tsaye, tare da hana rikicin rikidewa zuwa mummunan lamari.

Ya ce:

"Matakin gaggawa da ƴan sanda suka ɗauka ne ya hana rikicin ya rikide zuwa tashin hankali mai tsanani da zubar da jini."
Kakakin rundunar yan sandan Kano
Yan sanda sun tabbatar da ballewar rikici a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Abin da yan sanda ke kokarin yi

A nasu bangaren, mai magana da yawun ƴan sanda na Kano, SP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kiyawa ya tabbatar da cewa ce ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin hatsaniyar da ta faru.

Rikici ya balle a Kano

A baya, mun wallafa cewa an samu ɗan rikici a fadar mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, da ke Ƙofar Kudu, a ranar Lahadi, 6 ga watan Yuli, 2025.

Hatsaniya tabl barke a yayin da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya zo wucewa kusa da fadar tare da rakiyarsa, inda aka ruwaito wasu matasa sun tare tawagar.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da afkuwar wannan rikici, duk da cewa har yanzu ba a fitar da cikakken bayani a kan abubuwan da suka jawo rikicin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng