Gwamnatin Najeriya Ta Yi Magana kan Ƙera Makamin Nukiliya bayan Yaƙin Iran da Isra'ila
- Gwamnatin tarayya karkashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta ce ba ta da shirin ƙerawa ko gwajin makaman nukiliya
- Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ne ya faɗi matsayar Najeriya da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar CTBTO a Abuja
- Wannan dai na zuwa ne bayan yakin da ya auku na tsawon kwanaki 12 tsakanin Iran da Isra'ila, wanda ya samu asali daga shirin kera nukiliya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da niyyar ƙerawa ko gwajin makamin dukiliya, tana mai cewa ta maida hankali ne kan matsalolin da suka addabi jama'a.
Ta ce Najeriya ta kudiri aniyar hana duk wani gwajin makaman nukiliya ta hanyar haɗin gwiwa da Ƙungiyar Hana Gwajin Makaman Nukiliya Ta Duniya (CTBTO).

Source: Twitter
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya bayyana hakan ranar Litinin, 7 ga watan Yuli, 2027 a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
2027: Jam'iyyar haɗaka ADC ta tono tarihin da ka iya hana Tinubu zama shugaban ƙasa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce Shettima ya faɗi matsayar Najeriya ne a lokacin da ya karɓi bakuncin shugaban CTBTO, Dr. Robert Floyd, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Shettima ya nesanta Afirka da gwajin nukiliya
Ya ce a halin yanzu, nahiyar Afirka ta mayar da hankali ne kan matsalolin da ke addabarta musamman talauci da illolin sauyin yanayi, amma ba ruwanta da kera nukiliya.
"Rikicin nukiliya bai taɓa zama riba ga kowa ba; ko da yaushe illa ce kawai. Mu a nan muna yaki ne da talauci, tabarɓarewar tattalin arziki da ƙarancin ilimin halittu a yankin Sahara.
"Babu abin da ya shafe mu da makaman nukiliya. Ina tabbatar maku da cewa Najeriya na nan daram wajen goyon bayan hana gwaji da ƙera makaman nukiliya.
"Ina kuma godiya ga ƙungiyarku bisa ƙoƙari da wayar da kai da kuke yi, kasancewar kuna da rassa 337 a duniya. Duk gwaje-gwaje bakwai da Koriya ta Arewa ta yi, an gano su.

Kara karanta wannan
Hanyoyi 7 masu sauƙi da za ka shiga jam'iyyar haɗaka ADC ko wata jam'iyya a Najeriya
- Kashim Shettima.
Shettima ya ƙara da cewa ayyukan CTBTO na taimakawa har a fannoni na rayuwar yau da kullum, kamar gano girgizar ƙasa, fashewar tsaunuka da barazanar tsunami.

Source: Twitter
Shugaban CTBTO ya yabawa Najeriya
A nasa jawabin, Dr. Floyd, ya yabawa ƙoƙarin Najeriya ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu, wajen taka dakile gwaje-gwajen nukiliya a duniya da kuma gina ƙa’idojin hana su.
Floyd ya yaba gudummawar da Najeriya ke bayarwa ta hannun hukumomin da abin ya shafa, NAEC da NNRA, waɗand ake kula da harkokin makamashin nukiliya.
Haka zalika ya yaba da ingancin bayanan sirri da waɗannan hukumomi ke bayarwa da kuma yadda Najeriya ta ba da himma wajen cimma manufofin ƙungiyar CTBTO.
Gwamnatin Tinubu ya yi bayani kan tsarin haraji
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Najeriya ta yi karin haske kan sabuwar dokar haraji da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya rattaɓa hannu a kai.

Kara karanta wannan
'Zuwansa alheri ne': Ribadu ya faɗi yadda Tinubu ya ceto Najeriya daga tarwatsewa
Gwamnatin Bola Tinubu ta ce mutanen Najeriya da ke samun ƙasa da N250,000 a wata ba za su biya harajin kuɗin shiga ba.
Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan sauya tsarin haraji, Taiwo Oyedele, ya ce dokar ba za ta cire kuɗi daga aljihun talakawa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng