'APC za Ta Doke Atiku a cikin Sauki,' Abokin Takarar Peter Obi kan Zaben 2027
- Yusuf Datti Baba-Ahmed, wanda ya tsaya tare da Peter Obi a matsayin mataimaki a zaben 2023, ya shawarci ADC game da zaben 2027
- Ya bayyana cewa APC da Bola Tinubu a tsaye suke, kuma sun san dukkanin dabarun siyasar da Atiku Abubakar yake aiki da su
- Datti Baba Ahmed, ya bayar da shawara a kan wanda ya fi cancanta da ya tsaya takarar matukar ana son doke APC daga kan mulki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Yusuf Datti Baba-Ahmed, abokin takarar Peter Obi a zaben shugaban kasa na 2023, ya shawarci jam’iyyar ADC kan tsayar da dan takara.
Yusuf Datti Baba-Ahmed ya shawarci kawancen jam’iyyun adawa da ta tsayar da ɗan takara wanda jam’iyyar APC ba za ta iya doke shi ba a zaben 2027.

Source: Facebook
Vanguard News ta wallafa cewa wannan ya biyo bayan rade-radin cewa jam’iyyar ADC na shirin tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar takara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baba-Ahmed ya ce Shugaba Bola Tinubu da APC sun saba da tsarin siyasar Atiku, domin sun riga sun kayar da shi sau biyu a zabukan shugaban kasa.
Abokin takarar Obi ya magantu kan Atiku
Jaridar The Sun, ta wallafa cewa Baba-Ahmed ya bayyana cewa akwai bukatar yan hadakar adawa su yi hankali da wanda za su tsayar takara da zai kara Bola Tinubu.
Ya bayyana cewa:
“Idan kuka fitar da Atiku, sun san yadda za su yi da shi. Idan ya ci zabe, zai samu goyon bayana. Amma dan takarar da za a fitar don a doke APC shi ne wanda ba su san inda za su kama shi ba — wannan ne hanya mafi sauƙi ta nasara.”
Ana kwatanta manyan adawa da Tinubu
Yusuf Datti Baba-Ahmed, ɗan siyasa daga jihar Kaduna mai shekaru 55, ya bukaci jam’iyyun adawa su fahimci irin tasirin da Bola Tinubu ya yi kafin ya cimma burinsa a 2023.

Source: Facebook
Ya ce:
“Wannan mutumin da ake kira Tinubu, ya shafe shekaru 16 yana tsara dabaru har ya kai ga zama shugaban kasa. Ya aikata abin da babu wani ɗan siyasa da ya taba yi. Kuma ban ga wanda ke cikin kawancenmu da zai iya yin irin wannan haƙuri da tsari ba.”
A wata hira daban da aka yi da shi kwanan nan, tsohon 'dan majalisar ya nuna goyon bayansa ga Peter Obi, yana bayyana cancantarsa wajen jagorancin Najeriya.
Ya ce:
“A bisa rawar da Obi ya taka a zaben 2023, ya cancanci tikitin shugaban kasa a karkashin ADC.”
Jagororin APC sun gaza tarbar Kashim
A baya, kun ji cewa an lura da rashin halartar shugabannin jam’iyyar APC a jihar Kano yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya je ta'aziyya.
A yayin da jami’an gwamnati daga NNPP mai mulki a jihar Kano, suka tarbi Shettima cikin girmamawa, ba a ga ko daya daga cikin manyan ’yan APC ba.
Wannan lamari ya tayar da kura da tambayoyi, inda mutane da dama ke ganin hakan wata alama ce da ke nuni da rarrabuwar kai da baraka a cikin jam’iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

