Wike Ya Fadi Muhimmin Dalilin da Ya Sa Ya Shiga Gwamnatin Tinubu
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan daliƙin da ya sa ya shiga gwamnatin mai girma Bola Tinubu
- Nyesom Wike ya bayyana cewa ya shiga gwamnatin Tinubu a 2023 ne don ya yi amanna cewa ƴan Najeriya za su amfana da ita
- Ministan ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri domin ƙalubalen da ake fuskanta a ƙasar nan zai wuce nan ba ɗa jimawa ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da ya sanya ya shiga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Nyesom Wike ya bayyana cewa ya shiga gwamnatin Shugaba Tinubu ne saboda ya tabbata za ta kawo wa ƴan Najeriya ribar dimokuraɗiyya.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta ce Wike ya yi wannan jawabi ne a yayin bikin godiya bisa nasarar kammala ayyuka da kuma ƙaddamar da su da aka gudanar a cocin St. James ta Asokoro da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nyesom Wike ya ba ƴan Najeriya tabbaci
Wike ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa yawancin ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta za su gushe nan ba da jimawa ba.
Ministan ya roƙi ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da gwamnatin da ke ci a halin yanzu.
A cewarsa, Shugaba Tinubu ya cimma nasarori masu yawa a cikin shekaru biyu da ya shafe yana kan mulki.
Ministan na Abuja ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin shugaba mai himma wajen tafiyar da gwamnati, inda ya ce ya ba ministoci umarni na musamman don tabbatar da cigaban ƙasa.
Ya kuma roƙi cocin da ta ci gaba da addu’a ga Shugaba Tinubu da kuma masu aiki tare da shi.
Wike ya shawarci cocin da kada ta saurari ƴan siyasa da tsofaffin shugabanni waɗanda burinsu kawai shi ne su amfanar da kansu.
Ministan ya ce waɗanda suka ƙirƙiri haɗakar siyasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC burinsu shi ne lalata ƙasar nan.

Kara karanta wannan
"Ku yarda da ni": Obi ya fara lallaɓa ƴan Arewa, yana neman ƙuri'un doke Tinubu a 2027

Source: Facebook
Wike ya yabi gwamnatin Bola Tinubu
“Bari na faɗa muku gaskiya, da gwamnatin Tinubu ba ta aiki, da ban mara mata baya ba."
"Mazauna Abuja da ƴan Najeriya gaba ɗaya za su iya shaida sauye-sauyen da shugaban ƙasa ya kawo a Abuja."
"A baya, samun kuɗi ga Abuja babban ƙalubale ne. Amma shugaban ƙasa, cikin hikimarsa, ya cire mu daga tsarin Asusun bai ɗaya na tarayya (TSA), wanda ya hana ci gaban Abuja na dogon lokaci."
"A yau, muna iya ganin ayyuka da ido saboda ba mu ƙara aiki a ƙarƙashin tsarin asusun TSA ba."
“Ina so na yi amfani da wannan dama na gaya muku, musamman coci, kusan cewa kun yi babban kuskure a 2023. Dole ne mu yi taka-tsantsan a wannan karon."
"Wannan kuskuren da kuka kusan yi da ya faru, da wasu daga cikinmu sun rasa makomarsu."
- Nyesom Wike
Wike ya faɗi masu kawo masa matsala a Abuja
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyyana cewa akwai masu kawo masa matsala wajen tattara kuɗaɗen haraji.
Nyesom Wike ya bayyana cewa wasu manyan Abuja na kawo masa cikas wajen karɓar kuɗaɗen haraji.
Ministan ya nuna cewa halayyar da manyan mutanen suke nunawa abin takaici ne domin kuɗaɗen haraji na da matuƙar muhimmanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

