Sanata Natasha Ta Sanar da Ranar Komawa Majalisar Dattawa bayan Hukuncin Kotu

Sanata Natasha Ta Sanar da Ranar Komawa Majalisar Dattawa bayan Hukuncin Kotu

  • Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akptoi Uduaghan ta sanar da cewa ta fara shirye-shiryen komawa majalisar dattawa a makon nan
  • Kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa dakatarwar wata shida da aka yi wa Natasha ta saba doka kuma an shiga hakkinta da na jama'arta
  • Sai dai duk da haka, kotun ta ci tarar Sanatar saboda bisa laifin karya dokar da aka gindaya masu a yayin shari'ar da ta yi da Majalisa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kogi – Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana cewa tana shirye-shiryen koma wa bakin aiki a ranar Talata.

Wannan na zuwa ne bayan hukuncin kotu da ya soke dakatarwarta tare da umartar majalisar dattawa da ta dawo da ita.

Kara karanta wannan

Majalisa ta gindaya sharudan dawo da Sanata Natasha ofis bayan umarnin kotu

Sanata Natasha H Akpoti
Sanata Natasha za ta koma bakin aiki Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Natasha ta bayyana godiya ga magoya bayanta cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta saboda soyayyar da suka nuna mata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta yi hukunci kan dakatar da Natasha

The Guardian ta ruwaito cewa kotun tarayya da ke zamanta a Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata ta yanke hukuncin cewa dakatarwar wata shida da aka yi wa Natasha daga majalisa ta yi yawa.

Kotun ta ce dakatarwar ta kauce wa kundin tsarin mulki, kuma ta ci zarafin 'yan mazabarta, ta kuma umarci majalisar da ta mayar da ita nan take.

Natasha ta gode wa magoya bayanta

Sai dai kotun ta ci tarar Sanata Natasha N5m saboda raina kotu, inda aka ce wani sakon barkwanci da ta wallafa a Facebook ya karya umarnin kotu.

Mai shari’a Binta Nyako ta ce sakon nata ya sabawa umarnin da aka bayar a ranar 4 ga Maris, 2025 wanda ke hana ɓangarorin magana a bainar jama’a ko a kafafen sada zumunta kan shari’ar.

Kara karanta wannan

Natasha Vs Akpabio: Kotu ta gano mai laifi, ta yanke hukunci kan dakatarwar watanni 6

Sanatar Kogi ta tsakiya
Sanata Natasha za ta koma majalisa a ranar Talata Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Facebook

An dakatar da Natasha daga majalisa a watan Maris bayan wata gardama a zaman majalisa inda ta zargi shugaban majalisar, Sanata Akpabio, da cin zarafinta.

A cikin jawabin da ta yi ga magoya bayanta a jihar Kogi, Sanata Natasha ta tabbatar masu da cewa za ta koma zauren majalisa don ci gaba da wakiltarsu.

Ta kara da cewa:

“Na gode muku bisa goyon bayan da kuka ba ni. Ina farin cikin cewa mun yi nasara yau. Za mu koma majalisa a ranar Talata da ikon Allah."

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar Natasha

A baya, mun wallafa cewa babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta kama Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da laifin raina umarnin kotu kan shari'ar.

A zaman kotun 4 ga Yuli, 2025, mai shari’a Binta Nyako ta bayyana cewa kotu ta gamsu cewa Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta karya umarnin da aka bayar a baya.

Sanata Natasha ta wallafa wani saƙon neman afuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a shafinta na Facebook a ranar 7 ga Afrilu, 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng