"Lauyoyi na cikin Matsala": Cikakken Jawabin da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II Ya Yi

"Lauyoyi na cikin Matsala": Cikakken Jawabin da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II Ya Yi

  • Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya yi jawabi a wurin taron dokokin kasuwanci da ƙungiyar NBA-SBL ta shirya a jihar Legas
  • Sanusi II ya bayyana cewa ayyukan lauyoyi na fuskantar barazana saboda zuwan fasahohin zamani kamar AI da sauransu
  • Basaraken ya bukaci a ƙara kwas din koyon amfani da fasahohin zamani a karatun lauyoyi na Najeriya domin inganta ayyukan masana doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya ce aikin lauyoyi na fuskantar barazana ta rushewa gaba ɗaya a duniya saboda zuwan fasaha.

Sanusi II ya bayyana haka ne jiya a birnin Lagos, a yayin gabatar da jawabi na musamman a taron da aka shirya kan dokokin kasuwanci na shekara-shekara karo na 19.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarautar Kano, Muhammadu Sanusi II zai yi jawabi na musamman

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.
Sarki Muhammadu Sanusi ya ce lauyoyi na fuskantar gagarumar matsala a ayyukansu Hoto: @masarautarkano
Source: Twitter

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa sashen dokar kasuwanci na ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA-SBL) ne ya shirya taron kamar yadda aka saba a duk shekara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sansui II ya hango barazana ga lauyoyi

Muhammadu Sanusi II ya ce:

“Lauya, a yadda muka san shi, mutum ne masanin dokoki, mai adana shaidu na doka, mai kula da bin ka’ida, a yau wannan mutumin yana fuskantar barazanar zama marar amfani.
“Ba wai saboda dokar ce aka shafe ba, a’a, sai dai duniya tana canzawa da sauri fiye da ka’idojin da ake da su. A wannan zamanin na fasaha, dole ne ayyukan lauya su sauya domin su ci gaba da aikinsu.
"Fasahar aiki da kai na iya zama barazana, amma kuma dama ce ga lauyoyi su inganta ayyukansu ta hanyar amfani da fasaha.”

Akalla lauyoyi 1,000 daga sassa daban-daban na duniya ne ke halartar wannan babban taro da NBA-SBL ke daukar nauyi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya mika wa 'yan adawa bukatar takara bayan samun sarauta a Pantami

Jawabin Muhammadu Sanusi II ga dubban lauyoyi

A kalamansa, Sarki Sanusi ya ci gaba da cewa:

“Ba wai muna gab da shiga zamanin sauyi ba ne, mun riga mun shiga cikinsa tsundum. Mun tsinci kanmu a wani lokaci a rayuwar ɗan adam da ci gaban fasaha ke canza komai a rayuwarmu.
“Fasahar AI, koyon sarrafa na’ura, haɗa bayanai da fasahar blockchain, ba kalmomin ban dariya ba ne, a yanzu sun zama jigogin rayuwarmu ta yau da kullum, har da sana’o'inmu."
“Damarmakin da wannan zamanin ke samarwa suna da yawa, tun daga sauƙaƙa ayyuka, inganta hulɗa da abokan kasuwanci, ƙara inganci, da bunƙasa riba.
Fasaha na rage nauyi, ta inganta aiki, amma duk da haka, akwai ƙalubalen da ke tafe da hakan.”

Mai martaba Sarkin ya ƙara da cewa a halin yanzu, fasaha ba zaɓi ba ce ga al'umma, ta zama tilas.

Muhammadu Sanusi II ya yi jawabi kan fasahar zamani a Legas.
Sarkin Kano ya bukaci a zamanantar da aikin lauyoyi a Najeriya Hoto: @marautarkano
Source: Twitter

Wace mafita ta rage wa lauyoyin Najeriya?

Ya ce dole ne a haɗa koyar da fasaha cikin kwasa-kwasan karatun lauya, domin matasa masu shirin zama lauyoyi su samu ƙwarewa tare da gogewar da ake bukata a wannan zamani.

Kara karanta wannan

Dantata: Dangote ya karbi tawagar gwamnatin Kano da Jigawa a Madina

“Lauya a ƙarni na 21 a Najeriya dole ne ya kammala karatu yana da ilimin dokar kasuwanci da kuma fahimtar yadda fasaha ke da tasiri a aikinsa.
"Ya kamata ya fahimci hakkokin kundin tsarin mulki da kuma barazanar sirrin bayanai da tsaron intanet.”

- Inji Muhammadu Sanusi II.

Sanusi II ya jawo hankalin masu zuba jari

A wani labarin kuma, mun kawo maku cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya bukaci 'yan kasuwa na kasashen ƙetare su zo su zuba jari a Najeriya.

Sanusi II ya bayar da tabbacin cewa akwai duk abin da yan kasuwa suke bukata na zuba hannun jari a Najeriya da zummar samun riba.

Basaraken ya yi wannan jawabin a taron masi zuba jari na duniya wanda ya samu halarta a ƙasar Tunusia.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262