Ana tsaka da Rikicin Sarautar Kano, Muhammadu Sanusi II Zai Yi Jawabi na Musamman
- Sarkin Kano na 16 kuma tsohon gwamnan CBN, Muhammadu Sanusi II zai yi jawabi na musamman a taron kasuwanci na ƙasa da ƙasa a Legas
- Ɓangaren kasuwanci na kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA-SBL) ne ya shirya wannan taro kuma aka gayyaci Sarki Sanusi II
- Ana sa ran lauyoyi sama da 1,000 ne za su halarci wannan taro da za a tattauna kan dokokin kaauwanci a wannan zamani na fasaha
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Lagos - Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II zai yi jawabi na musamman a taron kasuwanci na ƙasa da ƙasa a jihar Legas.
Sashen kasuwanci na ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA-SBL) ne ya shirya wannan gagarumin taro a birnin Legas da ke Kudu maso Yamma.

Source: Twitter
A yau Laraba, 2 ga Yuli, 2025, Khalifa Muhammadu Sanusi II, zai gabatar da jawabin na musamman a wannan taro, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wane taro Sanusi II zai yi jawabi a Legas?
Taken taron na bana shi ne, “Makomar dokokin kasuwanci a wannan zamani na fasahar AI," wato yadda dokokin kasuwanci za su ci gaba da tafiya a duniyar da fasahar kere-kere ke kara tasiri.
A cewar kwamitin da ya shirya taron, fiye da lauyoyi 1,000 daga sassa daban-daban na duniya ake sa ran za su hallara a Legas domin wannan taro na shekara-shekara.
Wannan dai shi ne karo na 19 a jerin taron dokokin kasuwanci na ƙasa da ƙasa da kungiyar NBA-SBL ke shiryawa.
Za a gudanar da taron a babban ɗakin taro na Harbour Point da ke Victoria Island a jihar Legas.
Me za a tattauna a taron NBA-SBL?
Ana sa ran manyan masana daga sassa daban-daban, ciki har da lauyoyi, shugabannin kamfanoni, da kwararru a harkar kasuwanci, za su tattauna batutuwa da suka shafi dokokin kasuwanci a duniya da Najeriya.
Ms. Solape Peters, shugabar kwamitim shirya taron, ta shaida wa manema labarai a Legas cewa an shirya taron ne domin kara wa juna sani tsakanin masana da shugabannin kasuwanci game da kalubalen da ke gaban dokokin kasuwanci.

Source: Twitter
Dalilin gayyatar Muhammadu Sanusi II
Masu shirya taron sun gayyaci Sanusi II a matsayin babban bako mai jawabi saboda iliminsa a harkar tattalin arziki, kasuwanci da shugabanci, da kuma irin gudunmawar da yake bayarwa a fagen cigaban Najeriya da Afrika.
Muhammadu Sanusi II dai ya kasance tsohon gwamnan babban bankin Najeriya watau CBN, kafin a naɗa shi a matsayin sarkin Kano.
Taron zai yi nazari kan yadda dokokin kasuwanci za su iya daidaituwa da fasahohi kamar AI, blockchain, da sauran ci gaba da ke sauya yadda ake gudanar da kasuwanci a duniya, rahoton Bussiness Day.
Sanusi II ya faɗi yadda ya san akwai talauci
A wani rahoton, kun ji cewa Khalifa Muhammadu Sanusi II ya ce bai san ainihin talauci ba sai bayan ya hau karagar sarautar Kano.
Sarkin na jihar Kano ya bayyana cewa a iya fahimtarsa manyan mutanr da yawa a ƙasar nan ba su san menene talauci ba, ballantana su taimaki jama'a.
Muhammadu Sanusi II ya kuma yi kira ga shugabanni da su kasance masu jin ƙai da tausayi ga mutanen da suka damƙa masu amanar jagoranci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

