Cin Hanci: Garba Shehu Ya Bayyana Sirrin Mulkin Muhammadu Buhari

Cin Hanci: Garba Shehu Ya Bayyana Sirrin Mulkin Muhammadu Buhari

  • Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana yadda Muhammadu Buhari ya shafe shekaru takwas a mulki
  • Garba Shehu ya ce Muhammadu Buhari ya bar mulki ba tare da an taba kama shi da cin hanci ba daga farko har karshe
  • A game da zargin rashin takardar shaidar karatun Buhari, hadimin ya ce siyasa ce da aka kirkiro lokacin zaben 2015

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Garba Shehu, tsohon hadimin shugaban kasa, ya bayyana yadda Muhammadu Buhari ya jagoranci Najeriya na tsawon shekaru takwas.

Garba Shehu ya ce Buhari ya bar ofis ba tare da wani tabo a kan mutuncinsa ba, domin babu wanda zai iya cewa ya taba karbar cin hanci.

Kara karanta wannan

Cire tallafi: Gaskiya ta fito kan zargin Buhari da neman haɗa ƴan Najeriya faɗa da Tinubu

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
Tsohon hadimin Buhari ya fadi yadda aka gudanar da mulki Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Arise News ta ruwaito cewa Shehu ya kuma bayyana cewa zargin cewa tsohon shugaban kasar ba shi da takardar shaidar makaranta wani salo ne na siyasa da ya kunno kai a lokacin zaben 2015.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin Buhari na rashin magana da jaridu

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, tsohon mai magana da yawun shugaban kasa ya yi magana kan dalilin da ya sa Buhari bai cika ba da dama ga jaridu ba.

Garba Shehu ya bayyana cewa Buhari na daya daga cikin masu karatu fiye da kima a Najeriya, wanda ya san duk abin da ke gudana a kasa.

A cewarsa:

"Yana karanta dukkanin jaridu. Yana tambaya da safe don a kawo masa jaridu. Buhari bai cika magana da manema labarai ba domin ba mutum ne mai son bayyana aikinsa ba; ya fi son aikinsa ne ya yi magana da kansa.”

Garba Shehu ya yi magana kan gama aiki

Mai magana da yawun tsohon shugaban kasar ya ce tun bayan saukar Buhari daga mulki, ya samu karin natsuwa da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

2027: APC ta fadi yadda jihar Sakkwato kadai ta isa kai Tinubu ga nasara a Arewa

A kalamansa:

“Tun da Buhari ya bar ofis, babu wani dan jarida da ya kira ni ya ce ‘za mu buga labari’ muna so mu ji martaninka. Yanzu haka ina yin barci cikin natsuwa.”
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
Garba Shehu ya ce Buhari ba ya cin hanci Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Shehu ya kara da cewa:

"Zargin da ake yi kan takardar shaida ya samo asali ne daga siyasar da ta zagaye zaben 2015.”

Dangane da littafin da ya rubuta kan lokacin da ya yi aiki da shugaban kasa, Shehu ya ce littafin na dauke da bayanai.

Ya ce ya fitar da komai dalla dalla a kan aikinsa, kuma yana dauke da darussa da za su amfani dalibai, masu aikin jarida da masu bincike.

Baya ga Buhari, Garba Shehu ya kasance mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a lokacin mulkin shugaba Olusegun Obasanjo na biyu.

An kwatanta mulkin Buhari da na Tinubu

A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta fi ta tsohon shugaba Muhammadu Buhari aikin ci gaba.

Kara karanta wannan

'Babu hadaka da Atiku,' Peter Obi ya ce zai yi takara a 2027, zai yi wa'adi 1 kawai

Fayose, wanda jigo ne a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ya ce tun da fari yana da yakinin cewa gwamnatin Tinubu za ta yi nasara saboda jajircewar shugaban kasa.

Tsohon gwamnan ya ce a lokacin gwamnatin da ta gabata, tattalin arzikin Najeriya ya karye, amma yanzu ana ganin aikin Tinubu wajen dawo da komai yadda ya kamata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng