An Bayyana Sunan Mutum 1 Tilo da Ya Kashe Hatsabibin 'Dan Bindiga, Yellow Danbokolo

An Bayyana Sunan Mutum 1 Tilo da Ya Kashe Hatsabibin 'Dan Bindiga, Yellow Danbokolo

  • Bashir Maniya, tsohon hatsabibin ɗan bindiga da ya tuba ne ya harbe Yellow Danbokolo har lahira, sabanin jita-jitar cewa 'yan banga ne
  • Maniya ya kasance cikin tawagar haɗin gwiwa ta DSS da HYBRID da suka kai hari sansanonin 'yan bindiga, inda ya samu rauni kuma aka kashe shi
  • Bello Turji ya tabbatar da mutuwar Maniya a bidiyo, yana mai karyata labaran ƙarya game da yadda Danbokolo ya mutu da kuma rawar 'yan banga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Sabanin rahotannin da ake yadawa, an gano cewa ba 'yan banga ne suka kashe gawurtaccen dan bindiga, Kachalla Yellow Danbokolo ba.

Sabon rahoton da aka samu, ya nuna cewa Bashir Maniya, tsohon hatsabibin dan bindigar Zamfara, da ya tuba ne ya harbe Yellow Danboko har lahira.

Kara karanta wannan

Bayan kisan ɗan uwansa, ana zargin Bello Turji na neman sulhu domin miƙa wuya

An bayyana Bashir Maniya a matsayin wanda ya kashe hatsabibin dan bindiga, Yellow Danbokolo
Bashir Maniya ne ya hallaka Kachalla Yellow Danbokolo a harin da suka kai Zamfara. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Maniya: Mutumin da ya kashe Yellow Danbokolo

Zagazola Makama ya rahoto a shafinsa na X cewa Bashir Maniya ya kasance tsohon jagoran 'yan bindiga da aka taɓa jin tsoronsa a dazukan Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton, Maniya ya bar rayuwar laifi, ya rungumi sabuwar rayuwa, inda ya zama mai yaƙi da ta’addancin da ya taɓa taimakawa wanzuwarsa.

An rahoto cewa Maniya na cikin wata tawagar tsaro ta haɗin gwiwa da ta haɗa da DSS da dakarun HYBRID daga Maiduguri.

An kuma ce Maniya na cikin ɗaya daga cikin motocin yaƙi masu sulke yayin da aka tura tawagar don kai farmaki a yankin Shinkafi–Fakai, inda Bello Turji ya ke zama.

An kai farmaki ne kan sansanonin manyan ‘yan bindiga uku: sansanin Bello Turji da ke dajin Fakai kusa da Dutsin Kuris a Karamar Hukumar Shinkafi, jihar Zamfara; sansanin Malam Ila a dajin Kagara, karamar hukumar Isa a jihar Sokoto; da sansanin DanBokolo da ke dajin Fakai, Shinkafi.

Kara karanta wannan

Jirgin kamfanin Rano Air ya gamu da matsala bayan ya tashi daga Kano zuwa Sakkwato

A cikin sauyin kaddara, wannan jarumin da ya tuba, Bashir Maniya, ne ya harbe Danbokolo har lahira. Amma hakan ya zo da sakamako mai tsanani, domin shi kansa Maniya ya rasa ransa.

An kashe Maniya bayan harbin Danbokolo

Lokacin da mayakan Turji suka yi wa motocin tawagarsu Maniya kawanya, an ce daya daga cikin motocin ta kife, kuma Maniya na cikinta.

An ce duk da raunukan da ya samu sakamakon harin da aka kaiwa motar har ta kife, Maniya ya fito daga motar kuma ya fara harbi, yayin da yake kokarin ja da baya.

Yayin da Maniya ke kokarin tserewa daga wajen, mayakan Turji suka yi masa kawanya. A yayin hakan ne ya harbe wasu 'yan bindiga uku ya kuma raunata Yellow Danbokolo a ƙafa.

Akalla ‘yan bindiga 25 aka kashe, yayin da jami’an tsaro suka yi asarar mutane 13, ciki har da dakarun HYBRID 10 da wasu 'yan sa-kai uku.

Sai dai jarumtakar Maniya ta zo karshe a wannan ranar, domin mayakan Bello Turji sun samu nasarar kama shi, kuma daga bisani suka fille kansa.

Bello Turji ya tabbatar da mutuwar Maniya

Kara karanta wannan

Maryam Shetty ta tofa albarkacin bakinta kan murabus ɗin Ganduje daga shugabancin APC

Bello Turji da kansa ya fitar da bidiyo inda ya ɗauki alhakin kashe Maniya. A bidiyon, ya nuna motar yaƙi da aka lalata sannan ya tabbatar da cewa an kashe Maniya a faɗan da suka yi.

A cikin bidiyon, Bello Turji ya karyata jita-jitar da wasu kafafen yaɗa labarai ke yadawa cewa ‘yan banga ne suka kashe Danbokolo.

Majiyoyi daga jami’an tsaro da kuma Askarawan Zamfara sun tabbatar babu irin wannan farmakin ‘yan banga a yankin.

Bayan raunukan da ya samu, mayakan Danbokolo sun kai shi Shanawa don ceton rayuwarsa, amma an kasa samun likita da zai iya duba shi.

Mutanen Zamfara sun cika da murna da aka kashe Kachalla Yellow Danboko
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Zamfara, a Arewa maso Yammacin kasar. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daga nan aka kai shi Kuriyan Dambo, nan ma ba a dace ba, inda aka zarce da shi zuwa Maresuwa, wanda hakan ya sa jikin nasa ya tabarbare.

A Burkawa aka sake kokarin ceto ransa amma hakan ya ci tura. Yayin da ake kokarin kai shi Baje, ya suma, kuma ya fara nuna alamar tsayawar numfashi.

A ƙarshe aka kai shi Kamarawa, inda ya rasu a ranar 26 ga Yuli, 2025, kwana uku bayan harbin da Maniya ya yi masa.

Sai dai wasu kafofin watsa labarai sun sauya lamarin, inda suka rika cewa ‘yan banga ne suka shiga sansanin Turji, suka harbe Danbokolo, suka yanke kansa, kuma har sun kashe sama da mutane 173, yayin da Bello Turji ke tsaye yana kallo.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da maganar Ganduje, an yaɗa murabus ɗin sakataren gwamnati, gaskiya ta fito

Karanta rahoton Makama a nan kasa:

Ana zargin Bello Turji na neman sulhu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, yana neman a yi sulhu bayan mutuwar ɗan uwansa kuma kwamandansa, Yellow Dan Bokolo.

An ce Turji na shirin ganawa da wasu ƙungiyoyin 'yan bindiga domin duba yiwuwar miƙa wuya ga gwamnatocin jihohin Arewa maso Yamma.

Wata majiya ta ce, Turji bai da ƙarfi yanzu, Danbokolo ne ke tafiyar da ayyukan faɗa da samar da kayayyaki a daji. Mutuwar Danbokolo ta yi matuƙar raunana ƙarfin Turji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com