A Karon Farko bayan Gama Yakin Iran da Isra'ila, Farashin Fetur Ya Sauka a Najeriya

A Karon Farko bayan Gama Yakin Iran da Isra'ila, Farashin Fetur Ya Sauka a Najeriya

  • Matatar hamshaƙin attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Ɗangote ta sauke farashin man fetur daga N880 zuwa N840 ga ƴan kasuwa
  • Mai magana da yawun matatar Ɗangote. Anthony Chiejina ne ya bayyana hakan, ya ce rangwamen zai fara aiki daga 30, watan Yuni, 2025
  • Wannan sauki da aka samu na zuwa ne bayan tsagaita wuta da ya faru tsakanin Iran da Isra'ila, lamarin da ya jawo tashin gangar mai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Matatar Ɗangote da ke Lekki a jihar Legas ta bayyana rage farashin kowace litar man fetur daga N880 zuwa N840 ga ƴan kasuwa.

Wannan dai shi ne karo na farko da matatar Ɗangote ta yi rangwame a farashin man fetur tun bayan dakatar yaƙin Isra'ila da Iran, wanda ya shafe kwanaki 12.

Kara karanta wannan

Kwanaki kaɗan bayan ɗaura aurensa, fitaccen ɗan wasan Liverpool ya rasu

Matatar Dangote ya sauke farashin fetur.
An fara samun saukin man fetur a Najeriya bayan gama yaƙin Iran da Isra'ila Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Mai magana da yawun matatar Ɗangote, Anthony Chiejina ne ya tabbatar da rage farashin ga jaridar Punch yau Litinin, 30 ga watan Yuni, 2025.

"Farashin PMS watau fetur ya ragu daga N880 zuwa N840 a kowace lita, kuma wannan ragi ya fara aiki daga ranar 30 ga Yuni,” in ji Chiejina.

Rikicin Iran da Isra'ila ya jawo tsadar mai

Wannan saukin na zuwa ne bayan ƙarin farashin da aka samu har ya kai zuwa N880, sakamakon rikicin kwanaki 12 da ya ɓarke tsakanin ƙasar Isra’ila da Iran.

Yaƙin ƙasashen biyu, ya haifar da tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya, inda farashin gangar mai ya kusa kaiwa $80.

Wannan tashin farashi a wancan lokaci ya tilasta matatar Dangote da sauran kamfanoni da ke da alaƙa da shi ƙara farashin mai domin daidaita asarar da za su iya fuskanta.

Gidajen mai sun shirya ba Ɗangote haɗin kai

Rahotanni sun nuna cewa gidajen mai da ke haɗin gwiwa da Dangote kamar su, MRS Oilx, Heyden Petroleum AP sun shirya rage farashin fetur ga ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Saukin da ƴan Najeriya ke murnar samu a farashin fetur ya gamu da cikas daga ƴan kasuwa

Ana ganin idan wannan ragi ya fara aiki gadan-gadan, yan kasuwa za su sauke na su farashin sakamakon ragin da aka masu daga inda suka ɗauko shi.

Rage farashin da matatar Ɗangote ta yi daga N880 zuwa N840 na iya kawo sauki ga yan kasuwa, musamman masu tuki da motocin haya da masu ababen hawa na kai da kai.

Amfanin rage farashin fetur ga ƴan Najeriya

Bugu da ƙari, ragin ka iya zama sanadin saukar farashin kayayyakin amfani na yau da kullum, saboda kuɗin jigila zai sauka, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Duk da dai Ɗangote ya rage farashin ne ga ƴan kasuwa kaɗai amma ana ganin saukin zai isa ga ƴan Najeriya da zaran ƴan kasuwar sun kai sabon kaya gidajen mansu.

Farashin mai ya tashi.
Farashin litar fetur ta fara sauka a Najeriya bayan tsagaita wuta Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai wani ɗan bunburutu ma'ana mai sayar da man fetur a bakin titi, Abdullahi Kabir ya shaidawa wa Legit Hausa cewa ba anan gizon ke saƙa ba.

A cewarsa, wani lokacin guga kan ba da ruwa amma igiya ta hana, don haka ba lallai ne wannan ragin ya iso ga ƴan Najeriya a kan lokaci ba.

Kara karanta wannan

ADC: Haɗakar Atiku ta fara ƙarfi, tsohon shugaban Majalisar Dattawa ya fice daga PDP

Audu mai fetur ya ce:

"Wannan ragin wani lokaci a baki ne kawai ko nace ƴan can zama ake yi wa, mu nan a Katsina da jihohin Arewa sai a ɗauki dogon lokacu ba kaga an samu ragi yadda ya kamata ba.
"Alal misali yanzu an cire masu N40, to sai a yi sati sannan za ka ga nan sun cire mana N5 ko N10, masu imanin gaske ne za su cire N20 zuwa N30. Allah Ya gyara mana kawai."

NNPCL ya kara farashin fetur zuwa N925

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin NNPC ya ƙara farashin kowace lita guda ta man fetur daga N915 zuwa N925 a jihar Legas.

Wannan ƙari na zuwa ne sa'o'i 48 bayan kamfanin NNPCL ya ƙara farashin litar fetur daga ƙasa da N900 zuwa N915.

Rahoton da aka tattara ya tabbatar da cewa kamfanin NNPCL ya yi ƙari na biyu a farashin litar man fetur, cikin awanni 48.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262