Nasara daga Allah: An Kashe Gawurtaccen Ɗan Bindiga da Ya Addabi Al'umma a Zamfara
- Ƴan sa-kai sun yi nasarar kashe ƙasurgumin ɗan bindiga a Arewa maso Yamma, Kachalla Yellow Ɗanbokolo a wani artabu a jihar Zamfara
- Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun tabbatar da mutuwar kwamandan ƴan bindigar, wanda ake ganin ya zarce Bello Turji haɗari
- Duk da babu wata sanarwa a hukumance daga hukumomin tsaro har kawo yanzu, amma an ce an kashe Ɗanbokolo ne tare da ƴan bindiga aƙalla 173
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - Rahotanni daga jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya sun nuna cewa na kashe ɗaya daga cikin hatsabiban ƴan bindiga.
Dakarun rundunar ƴan sa-kai sun samu nasarar hallaka ɗan bindigar, wanda ya jima yana addabar al'umma, Kachalla Yellow Danbokolo a jihar Zamfara.

Source: Original
DCL Hausa ta tabbatar da wannan nasara da ƴan sa-kai suka samu a wani rahoto da ta wallafa a shafinta na Facebook, a yau Litinin, 30 ga watan Yuni, 2025.
Ƴan sa-kai sun yi ajalin Yellow Ɗanbokolo
Sai dai har kawo yanzu babu wani cikakken bayani kan yadda jami'an tsaron samu wannan gagarumar nasara.
"‘Yan sa kai a jihar Zamfara sun yi ajalin kasurgumin dan bindiga, Kachalla Yellow Danbokolo," in ji rahoton.
Wani mai suna Shehu Umar ya tabbatar da wannan nasara a shafinsa na Facebook, yana mai cewa an kashe Ɗanbokolo ne tare da mayaƙansa sama da 170.
Yadda ƴan sa-kai suka samu nasara a Zamfara
A cewarsa, dakarun rundunar ƴan sa-kai na Shinkafi ne suka kashe hatsabibin ɗan bindigar, wanda yana ɗaya daga cikin kwamandoji masu haɗari a Arewa maso Yamma.
"An tabbatar da cewa ƴan sa-kai na Shinkafi sun kashe ɗaya daga cikin kwamandojin ƴan bindiga a Arewa maso Yamma, Kachalla Yellow Ɗanbokolo.
"An kashe shi ne tare da ƴan bindiga 173 a wani samame da ƴan sa-kai na yankin Shinkafa suka kai kan miyagun," in ji Shehu Umar.
Alakar Ɗanbokolo da Bello Turji
Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa Ɗanbokolo na da alaƙa da gawurtaccen ɗan bindigar nan, Kachalla Bello Turji, wanda har yanzu jami'an tsaro ke farautarsa.
Ana ganin dai Yellow Ɗanbokolo ya fi Bello Turji haɗari wajen kai hare-hare, kashe mutane, garkuwa da sauran ayyukan ta'addanci a Zamfara da jihohin Arewa maso Yamma.
An tattaro cewa Ɗanbokolo, ɗa ne ga kawun Bello Turji, kuma ya yi ƙaurin suna wajen kai hare-haren rashin imani fiye da Bello Turji.

Source: Facebook
Jami'an tsaro sun gwabza da mayaƙan Bello Turji
A wani rahoton, kum ji cewa gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta ce an samu nasarar kassara ƙarfin ƴan bindiga.
A wata sanarwa da mai taimaka wa gwamna kan harkokin tsaro, Alhaji Ahmad Manga ya fitar, ya ce jami'an tsaro sun yi ƙazamin artabu da mayakan Bello Turji a ranar Litinin.
Ya ce jami'an tsaro sun ƙashes mayaƙan Turji masu yawa a samamen wanda aka kai bisa haɗin guiwa tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

