Dantata: Abba, Namadi, Sanusi II, Tawagar Kano, Jigawa Sun Tafi Madina Jana'iza

Dantata: Abba, Namadi, Sanusi II, Tawagar Kano, Jigawa Sun Tafi Madina Jana'iza

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya jagoranci tawaga ta musamman zuwa jana’izar marigayi Aminu Alhassan Dantata a birnin Madina, Saudiyya
  • A baya, Legit ta rahoto cewa marigayi Dantata ya rasu ne a Abu Dhabi, UAE, inda ya shafe kwanakin ƙarshe na rayuwarsa cikin ibada
  • Tawagar ta haɗa da Gwamnan Jigawa, Umar A Namadi, Khalifa Muhammadu Sanusi II, da wasu manyan jami’an gwamnati da dattawan Arewa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tashi daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano tare da manyan jami’an gwamnati domin halartar jana’izar marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Gwamna Umar A. Namadi na jihar Jigawa na cikin tawagar da suka tafi birnin Madina na ƙasar Saudiyya domin halartar jana'izar.

Kara karanta wannan

Wakilan Tinubu da suka hada da Minista, Daurawa sun isa Madina jana'izar Dantata

Tawagar Kano da Jigawa sun tafi Madina jana'izar Dantata
Tawagar Kano da Jigawa sun tafi Madina jana'izar Dantata. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook.

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce tafiyar na nuna girmamawa da karramawa ga marigayin wanda ya yi fice a fannin kasuwanci, sadaka da taimakon al’umma.

Marigayi Dantata ya rasu ne a Abu Dhabi, babban birnin ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ya shafe kwanakin ƙarshe na rayuwarsa a can.

Dantata: Abba, Namadi, Sanusi II sun tafi Madina

Gwamna Abba ya bayyana marigayi Dantata a matsayin uba ga kowa, wanda rayuwarsa ta cika da karamci da taimako ga kowa da kowa.

Tawagar da ta tafi zuwa jana’izar ta haɗa da Gwamna Umar Namadi na Jigawa da Khalifa Muhammadu Sanusi II.

Haka zalika akwai tsohon gwamnan Jigawa, Ali Sa’ad Birnin Kudu, da wasu manyan sarakuna da jami’an gwamnati daga Kano da Jigawa.

Marigayi Dantata da za a yi jana'izarsa a Madina
Marigayi Dantata da za a yi jana'izarsa a Madina. Hoto: Hassan Mohammed
Source: Twitter

Daga cikin wadanda suka shiga tawagar har da sarakai irinsu Galadiman Kano, Matawallen Kano da Sarkin Yakin Kano

Kara karanta wannan

Najeriya ta girgiza: Tinubu da Atiku sun yi jimamin rasuwar Aminu Dantata

Sannan kuma akwai 'dan majalisar binrin Kano, Injiniya Sagir Koki, Nastura Ashir Sharif, Alhaji Sabiu Bako da Sanusi Bature Dawakin Tofa.

An bayyana cewa halartar jana’izar na nuna irin mutuncin da gwamnatin Kano da Jigawa da al’ummar jihohin ke yi wa marigayi Dantata.

Abba ya ce za a dade ana tuna Dantata

An bayyana marigayi Dantata a matsayin babban ginshiki a harkar kasuwanci da jin ƙai, wanda ya bar tarihi mai kyau a fannin raya al’umma da taimako ga marasa ƙarfi.

An tsara gudanar da jana’izar a birnin Madina, wadda ake sa ran za ta jawo hankalin manyan baki daga jihohi da ƙasashe daban-daban ciki har da ‘yan kasuwa, malamai, dangin marigayin.

Abba ya roƙi Allah ya jikan marigayin da rahama, ya saka masa da gidan Aljanna Firdausi, yana mai ƙara nanata cewa jihar Kano ta yi rashi babba kuma ba za a taɓa mantawa da shi ba.

Tinubu, Atiku sun yi jimamin Dantata

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan rasuwar Alhaji Aminu Dantata.

Kara karanta wannan

Shekarar Hijira: Sarkin Musulmi ya yi magana kan rashin tsaro, yakin Iran da Isra'ila

Alhaji Aminu Dantata ya rasu bayan shafe shekara 94 kuma ya bayar da gudumawar sosai wajen habaka tattalin Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce marigayin ya bar babban gibi a Najeriya tare da yi wa mutanen Kano jaje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng