Kaduna: Ƴan Bindiga Sun Shammaci Mutane da Tsakar Dare, Sun Ɗauke Basarake
- Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace mai unguwar Bauda da ke Maro, karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna da asuba
- Rahoto ya ce 'yan bindigar sun kai farmaki ne da misalin karfe 1:00 na safe, sun tafi da Obadiah Iguda kadai ba tare da kashe kowa ba
- Lamarin ya tada hankalin al'umma, yayin da hukumar Kufana ta bukaci gaggawar daukar matakin tsaro domin hana sake faruwar hakan
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Hankulan al'umma sun tashi bayan da yan bindiga suka farmake su da tsakar dare a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.
Miyagun da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace mai unguwar Bauda da ke Maro a masarautar Kufana, karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Asabar, 28 ga Yuni, 2025, da misalin karfe 1:00 na safe.

Kara karanta wannan
Taraba: Mummunan hatsari ya faru a cikin kasuwa bayan motar yashi ta markaɗe mutane
Yan bindiga sun taso sarakuna a gaba
Sace sarakunan gargajiya a Najeriya musamman a Arewacin kasar ya zama ruwan dare wanda ke kara dagula lamuran tsaro baki daya.
Hankulan mutane na tashi duk lokacin da aka yi garkuwa da manyan kasa da sauran masu rike da mudafiun iko duba da girmansu a cikin al'umma.
Tun farkon dagulewar matsalar tsaro a Arewa, ba za a iya tantance ko lissafa adadin sarakunan gargajiya da mahara suka dauke ko kashe su ba

Source: Original
Yan bindiga sun dauke basarake da tsakar dare
Miyagun sun kai harin ne bayan sun mamaye yankin Bauda wanda hakan ya daga hankulan al'ummar wurin.
An sace basaraken gargajiya, Obadiah Iguda bayan da 'yan bindigar suka kai hari suka tafi da shi ba tare da jikkata wani ba.
A cewar rahoton da mai kula da yankin Kufana, Mista Stephen Maikori, ya mika wa Agom Kufana, ba su sace ko kashe wani ba.
“Wannan danyen aiki ya kara jefa al’umma cikin fargaba da rashin kwanciyar hankali."
- Cewar Maikori
Rokon da aka yi ga hukumomi kan tsaro
Sace shugaban gargajiyar ya rushe tsarin shugabancin gargajiya a Bauda, ya kuma haifar da damuwa kan halin tsaro a yankin.
Hukumar yankin Kufana ta bukaci a gaggauta kawo tsaro mai dorewa domin kare rayuka da dukiyoyi tare da hana farmaki na gaba.
Da aka tuntube shi, Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce zai tabbatar da bayanan kafin magana.
Amma har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, bai kira ya bayar da karin bayani ba tukuna.
Sojoji sun fafata da yan bindiga a Kaduna
Mun ba ku labarin cewa rundunar sojin Najeriya ta dakile hari da ‘yan ta’adda suka kai wa sansanonin soja a jihohin Neja da Kaduna, inda aka hallaka da dama daga cikin maharan.
Majiyoyi sun ce rundunar sojojin kasar nan ta bayyana cewa a yayin fafatawar, wasu daga cikin dakarunta sun koma ga Mahaliccinsu a kokarin kare kasarsu.
Rundunar ta tabbatar da cewa an tura ƙarin dakarun soji domin ƙarfafa tsaro, tare da ci gaba da bin sawun sauran ‘yan ta’addan da suka tsere.
Asali: Legit.ng
