Taraba: Mummunan Hatsari Ya Faru a cikin Kasuwa bayan Motar Yashi Ta Markaɗe Mutane

Taraba: Mummunan Hatsari Ya Faru a cikin Kasuwa bayan Motar Yashi Ta Markaɗe Mutane

  • Wani mummunan hatsari ya faru a kasuwar Mile 6 da ke Jalingo a jihar Taraba wanda ya yi sanadin rayuka
  • Lamarin ya faru ne a jiya Asabar yayin da babbar motar diban yashi ta murkushe ‘yan kasuwa da masu siyayya
  • Babbar motar da ke ɗauke da yashi ta fito daga hanya bayan tayar gaba ta fashe, ta shiga kasuwa tana ragargazar mutane da gine-gine

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jalingo, Taraba - Wani mummunan hatsarin mota ya afku a cikin kasuwa da ke birnin Jalingo a jihar Taraba.

Hatsairn ya faru a jiya Asabar a kasuwar Mile 6 da ke Jalingo lokacin da wata mota ɗauke da yashi ta fadi.

Mutane sun mutu a hatsarin mota a Taraba
Mummunan hatsari ya faru a cikin kasuwar Taraba. Hoto: Legit.
Source: Original

Shafin Zagazola Makama ne ya samu labarin hatsarin wanda ya yi sanadin rayuka da dama da raunuka.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da maganar Ganduje, an yaɗa murabus ɗin sakataren gwamnati, gaskiya ta fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda manyan motoci ke jawo asarar rayuka a Najeriya

Wannan ba shi ne karon farko ba da manyan motoci ke rasa birki wanda suke afkawa mutane ko yan kasuwa dake jawo rasa rayuka da dukiyoyi.

Ko a watan Afrilu, wata babbar motar dakon kaya ta markaɗe mutane har lahira a wurin taron bikin ista a karamar hukumar Billiri a jihar Gombe.

Rundunar ƴan sanda a jihar ta tabbatar da mutuwar mutum biyar a hatsarin, wasu da dama sun samu raunuka an garzaya da su asibiti.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya yi alhinin waɗanda suka rasu, ya umarci a gudanar da bincike don gano musabbabin hatsarin.

An rasa rayuka a hatsarin mota a Taraba
Mutane da dama sun mutu a hatsarin mota a Taraba. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

An rasa rayuka a hatsarin mota cikin kasuwa

Majiyoyi sun ce hatsarin, wanda ya faru kusan ƙarfe 12:00 na rana, ya yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane da dama.

Bayanai sun nuna cewa motar tana gudu ne lokacin da ɗaya daga cikin tayoyinta na gaba ya fashe, hakan ya sa direban ya gagara rike ta.

Kara karanta wannan

Tsaurin ido: An cafke matasa 4 kan zargin gagarumar sata a majalisar tarayya

“Abin ya faru cikin sauri, Tipper ɗin na gudu ne, sai tayar gaba ta fashe, direban bai iya tsayawa ba.”

- Cewar wani dan kasuwa

Daukin da jami'an tsaro, lafiya suka kawo

Jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya sun isa wajen da gaggawa domin ceto wadanda suka jikkata da kai su asibiti mafi kusa.

An cire gawarwaki daga wajen da hatsarin ya faru, kuma ana ƙoƙarin gano sunayen mamatan tare da sanar da iyalansu.

An kama direban motar kuma yana hannun jami’an tsaro, yayin da ake ci gaba da bincike kan musabbabin haɗarin da kare faruwar haka a gaba..

Ango ya rasu a hatsarin mota a Bauchi

Mun ba ku labarin cewa Allah ya karɓi ran wani ango tare da abokinsa a hanyar zuwa masallacin da za a ɗaura aure ranar Asabar, 14 ga watan Yuni a jihar Bauchi.

Mai shirin zama angon, Garba Mustapha ya gamu da hatsarin mota mintuna kaɗan kafin ɗaura aurensa, lamarin da ya jefa yan uwa cikin jimami.

An gano cewa an shirya ɗaura auren marigayin da amaryarsa, Khadija Adamu Sulaiman da misalin karfe 11:00 na safe a babban masallacin Magama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.