Bam Ya Tarwatse da Matafiya a Yobe, an Samu Asarar Rayuka

Bam Ya Tarwatse da Matafiya a Yobe, an Samu Asarar Rayuka

  • An samu asarar rayuka a jihar Yobe da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya sakamakon fashewar wani bam
  • Bam ɗin wanda ya fashe a kan hanya ya yi sanadiyyar rasuwar mutum huɗu tare da jikkata wasu mutane da dama
  • Mutanen da bam ɗin dai ya fashe da suna kan hanyarsu ne ta zuwa shahararriyar kasuwar Buniyadi da ke jihar Yobe

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Fashewar wani bam ta jawo asarar rayukan mutane huɗu a jihar Yobe.

Bam ɗin wanda ya fashe a kan hanyar Katarko-Goniri da ke ƙaramar hukumar Gujba ya kuma raunata wasu mutum 21.

Bam ya fashe a jihar Yobe
Mutum 4 sun mutu sakamakon fashewar bam a Yobe Hoto: Hon Mai Mala Buni
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta rahoto cewa lamarin ya auku ne a ranar Juma'a, 27 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bam ya hallaka mutane a Yobe

Mutanen da lamarin ya rutsa da su yawancinsu sun fito ne daga ƙauyen Gotala, lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa shahararriyar kasuwar Buniyadi.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama wani ɗalibin Jami'a bisa zargin yiwa Iran leken asiri a Isra'ila

Lamarin ya auku ne lokacin da motar da suke ciki ta taka bam ɗin wanda ake zargin ƴan ta’adda ne suka binne a hanya.

Lokacin da aka ziyarci asibitin ƙwararru na Damaturu an lura cewa an kai gawarwakin mutane huɗu da suka rasa rayukansu gida domin yi musu jana’iza.

Sauran mutanen da suka jikkata kuma suna karɓar magani a asibitin ƙwararru na Damaturu da kuma asibitin koyarwa na jami’ar jihar Yobe.

Al’ummar ƙauyen Gotala na rayuwa ne a gefen dajin Sambisa, inda ake zargin mayaƙan Boko Haram na gudanar da hare-harensu fiye da shekara 15 da suka gabata.

Wata majiya da ba a tabbatar da sahihancinta ba ta bayyana cewa ko a jiya Alhamis, wasu motocin dakarun soji da na ƴan sa-kai su ma sun taka bam a kan wannan hanyar, inda lamarin ya yi sanadiyyar mutuwa ko jikkatar mutane da dama.

'Yan ta'adda sun dasa bam a Yobe
Matafiya sun rasu sakamakon fashewar bam a Yobe Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji ba su yi magana kan harin ba

Har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoton, rundunar sojojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da harin.

Kara karanta wannan

Bayan kashe dalibi, an Rufe jami'ar IBB saboda matsalolin tsaro a Neja

Ƴan uwan waɗanda harin ya shafa da aka tattauna da su a asibiti sun buƙaci gwamnatin jihar Yobe da ta gaggauta gyara hanyar da ta lalace, domin daƙile ayyukan ƴan ta’adda da ke barazana ga rayuwar al’umma da kuma sansanin sojoji da ke Goniri.

Ƴan ta'adda dai sun daɗe sun dasa bama-bamai a kan hanyoyin da mutane ke yin zirga-zirga musamman a jihohin Yobe da Borno inda rikicin Boko Haram ya fi ƙamari.

Ƴar ƙunar baƙin wake ta kashe mutane a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu asarar rayuka a jihar Borno bayan wata ƴar ƙunar baƙin wake ta tada bam a cikin mutane.

Budurwar ƴar ƙunar waken ta tayar da bam ɗin ne a wajen wani cin abinci da ke a ƙaramar hukumar Konɗuga ta jihar Borno.

Tayar da bam ɗin ya yi sanadiyyar hallaka aƙalla mutane 24 yayin da wasu kuma suka samu raunuka daban-daban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng