Fansho: Tsofaffin Yan Sanda Sun Gaji da Hakuri, An Shirya Gagarumar Zanga Zanga
- Kungiyar tsofaffin 'yan sandan Najeriya ta bayyana takaici a kan yadda ta ce gwamnati ta watsar da al'amuransu duk da kokensu
- Kungiyar reshen jihar Kaduna ta ce za ta shiga zanga-zangar lumana tare da sauran jihohi 35 da aka shirya gudanarwa a watan Yuli
- Ta jaddada cewa zanga-zangar su za ta kasance lumana, inda ake fatan za ta taimaka wajen nusar da gwamnati halin matsi da su ke ciki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Reshen Kaduna na ƙungiyar tsofaffin ’yan sanda da ke ƙarƙashin tsarin fansho na tarayya ya ce sun gaji da matsin rayuwa da suke ciki.
Kungiyar ta bayyana cewa za ta hada kai da sauran rassa 35 na jihohin ƙasar domin gudanar da zanga-zangar lumana a fadin Najeriya da za a gudanar a watan Yuli na shekarar 2025.

Source: Twitter
Jaridar The Nigerian Tribune ta ruwaito cewa wannan matakin wani bangare ne na ci gaba da kira da suke yi na fitar da rundunar ’yan sanda daga tsarin fansho na CPS.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan sandan Najeriya za su yi zanga-zanga
Jaridar Daily Post ta ce Shugaban kungiyar na jihar Kaduna, CSP Mannir M. Lawal Zaria mai ritaya da Mataimakinsa, ASP Danlami Maigamo ritaya, sun tabbatar da wannan matsaya.
Sun ce:
“Ba mu da wani zaɓi illa mu shiga wata sabuwar zanga-zangar lumana da za a fara a ranar 21 ga Yuli, 2025.”
Kungiyar ta kara jaddada cewa wannan zanga-zangar za ta kasance ta kasa baki daya kuma za ta kasance cikin lumana.
Ta kara da cewa:
“Za mu shiga zanga-zangar kasa baki daya cikin lumana.”
Yadda aka cimma shirin yajin aiki
An cimma wannan matsaya ne a wani taron wata-wata da kungiyar ta gudanar a Police Officers’ Mess da ke Kaduna.
Abu mafi muhimmanci a taron ya mayar da hankali a kai shi ne matsalolin da ba a warware ba game da shigar ’yan sanda cikin tsarin CPS.
A cewar kungiyar, a baya an gudanar da wata zanga-zangar lumana daga 24 ga Fabrairu zuwa 3 ga Maris, 2025, a gaban majalisar tarayya da reshen Kaduna da Bauchi suka shirya tare.

Source: Twitter
A lokacin wannan zanga-zangar, an mika koke zuwa ofisoshi biyar masu muhimmanci na shugabannin kwamitocin Majalisar Dattawa da ta Wakilai da kuma Daraktan Hukumar DSS.
Duk da wadannan matakai, kungiyar ta nuna takaicinta kan rashin samun amsa daga Majalisar Tarayya.
Kungiyar ta kuma nesanta kanta daga kowace kungiya da ke shirin tayar da tarzoma, tana mai jaddada cewa koke-koken da suke yi na da nasaba da matsin tattalin arziki.
An farmaki sansanin yan sanda
A baya, mun wallafa cewa yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan sanda a ƙauyen Makuku, karamar hukumar Sakaba, jihar Kebbi, inda suka yi awon gaba da bindigu ƙira AK‑47.
Yan bindigan sun farmaki sansanin ne da ƙarfe 1.00 na rana, suna tare da shanunsu da suka sata daga jihar Neja yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Zamfara, inda su ke zuba ta'addanci.
Majiyoyi masu tushe sun ce harin ya haifar da musayar wuta mai zafi tsakanin jami’an tsaro da yan bindigan, suka kwashe makamai da dama daga sansanin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

