Jerin Ƙasashen da Suka Mallaki Makamin Nukiliya a Duniya da Adadinsu
- Kasashen da ke da makaman nukiliya sun kai tara, bayan kera bam na farko a 1945 wanda ya tilasta samar da yarjejeniyar NPT
- Amurka da Rasha na da fiye da kashi 87 na makaman nukiliya a duniya, ciki har da na yaki kusan kashi 83 a fadin duniya
- Hakan ya biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin Iran da Isra'ila musamman saboda zargin kokarin samar da makamin nukiliya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yau Juma'a 27 ga watan Yunin 2025 kwana uku kenan bayan tsagaita wuta kan rikicin Iran da Isra'ila wanda ya tayar da hankulan al'ummar duniya.
An kwashe kwana 12 ana gwabza fada da kai hare-hare kan wanda daga bisani Amurka ta shiga yakin tare da kai mummunan hari a kasar Iran.

Source: Getty Images
Nukiliya ta zama musabbabin rikicin Iran da Isra'ila
Kasashen biyu sun tsunduma a rikicin musamman saboda zargin Iran tana kokarin kera makamin nukiliya a kasarta, cewar rahoton ICAN (The International Campaign to Abolish Nuclear Weapons).
Dukan kasashen biyu sun rasa rayukan al'ummarsu da asarar dukiyoyi kafin samar da mafita na tsagaita wuta.
Shugaba Donald Trump na Amurka shi ne ya shiga tsakani duk da marawa Isra'ila baya da yake yi.
Trump ya amince da kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran inda ya tabbatar da cewa ya yi mata illa.
Kasashen da suka mallaki makaman nukiliya
Tun bayan kera bam din nukiliya na farko a 1945, kasashe kalilan ne suka mallaki makaman nukiliya a duniya.
Fargaba kan yaduwar wadannan makamai ya sa aka sanya hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar nukiliya (NPT) a 1968.
A wancan lokacin, kasashe kadan ne suka mallaki irin wadannan makamai, sai dai daga nan adadin ya karu zuwa tara.

Kara karanta wannan
'Ba haka ba ne,' Iran Ta yi martani bayan Trump ya ce zai zauna da ita kan nukiliya
Kasar Koriya ta Arewa ce kadai ta fice daga yarjejeniyar NPT kuma ta ci gaba da kera makaman nukiliya.

Source: Getty Images
Kasashe 2 da suka fi kowa makaman nukiliya
Amurka da Rasha na da kimanin kaso 87 cikin 100 na duka makaman nukiliya da ake da su a duniya.
Har ila yau, suna da kaso 83 cikin 100 na makaman yaki da aka ajiye don amfani a rundunar sojojinsu, kamar yadda Miami Herald ta ruwaito.
An kiyasta cewa akwai makaman nukiliya 12,241 a duniya, inda 9,614 ke cikin ajiyar sojoji, a shirye don harbawa idan bukatar hakan ta tashi.
Ana iya harba su ta hanyar makamai masu linzami, jiragen sama, jiragen ruwa ko kuma jiragen karkashin ruwa.
Majiyoyi sun lissafo kasashe tara masu makaman nukiliya da yawan makaman kowanne kamar haka:
Ga jerin kasashe da suka mallaki makaman nukiliya:
1. Kasar Rasha – makamai nukiliya 5,459
2. Kasar Amurka – makaman nukiliya 5,177
3. Kasar China – makaman nukiliya 600
4. Kasar Faransa – makaman nukiliya 290
5. Kasar Burtaniya – malaman nukiliya 225
6. Kasar Indiya – makaman nukiliya 180
7. Kasar Pakistan – makaman nukiliya 170
8. Kasar Isra’ila – makaman nukiliya 90
9. Koriya ta Arewa – makaman kukiliya 50
Illar da makamin nukiliya zai iya yi
An ce makamin nukiliya guda ɗaya kaɗai na iya hallaka dubban mutane, tare da barazana mai tsanani ga lafiyar ɗan adam da muhalli.
Idan aka harba makami irin haka a saman birnin New York, ana hasashen zai kashe mutum 583,160 da raunata dubban mutane da illa ga muhalli, Britannica ta ruwaito.
Kasashe kamar China, Faransa, Indiya, Isra’ila, Koriya ta Arewa, Pakistan, Rasha, Birtaniya da Amurka suna da fiye da makaman nukiliya 12,300, yawancinsu sun fi ƙarfi fiye da wanda aka jefa a Hiroshima.
Sauran ƙasashe 32 ma suna da hannu a matsalar, inda ƙasashe shida ke ajiyar wasu makaman, yayin da wasu ƙasashe 28 ke goyon bayan amfani da su.
Iran tana bincike kan barnar da aka yi mata
Kun ji cewa kasar Iran ta tabbatar da cewa harin Isra'ila ya yi mata illa a cibiyoyin nukiliyarta a harin da ta ke kaiwa da kuma na Amurka a makon jiya.
Sai dai kasar ta ce har yanzu ba ta san iya adadin barnar ba yayin da hukumomi masu kula da cibiyoyin ke bincike don gano adadin.
Hakan ya biyo bayan harin Amurka kan cibiyoyin nukiliyar bayan Donald Trump ya fito ƙarara yana goyon bayan Isra'ila inda ya ce sun lalata cibiyoyin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


