'Yan Bindiga Sun Ɗebo Ruwan Dafa Kansu, Jirajen Sojojin Najeriya Sun Masu Kawanya a Neja

'Yan Bindiga Sun Ɗebo Ruwan Dafa Kansu, Jirajen Sojojin Najeriya Sun Masu Kawanya a Neja

  • Ƴan bindiga da dama sun sheƙa barzahu da jiragen yaƙin rundunar sama suka far masu a jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya
  • A wata sanarwa da kakakin NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar yau Juma'a, ya ce an halaka ƴan ta'adda masu ɗumbin yawa a wannan samame
  • Wannan na zuwa ne bayan wani kazamin musayar wuta da aka yi tsakanin sojojin ƙasa da ƴan bindiga, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dakaru 17

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Yayin da ake jimamin kisan sojoji 17 a jihar Neja, rundunar sojin saman Najeriya ta maida martani ta hanyar luguden wuta kan ƴan bindiga.

Dakarun sashe na 1 na Operation Fansan Yamma sun kashe gomman ƴan bindiga a wani samame ta sama da suka kai domin agazawa sojojin kasa a jihar Neja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nuna tsaurin ido, sun kashe sojojin Najeriya 20 a Neja

Sojoji sun maida martani a Neja.
Jiragen sojojin Najeriya sun yi wa yan bindiga dirar mikiya a jihar Neja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wannan na ƙunshe ne wata sanarwa da rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta wallafa a shafin X yau Juma'a ɗauke da sa hannun Daraktan Hulɗa da Jama’a, Air Commodore Ehimen Ejodame.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jiragen sojoji sun yi wa ƴan bindiga lugude

Ya ce jiragen yaƙin sojin saman sun kai hari ne kan ‘yan ta’addan da ke da hannu a hare-haren da suka faru a jihar Neja kwanan nan, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji.

Ejodame ya ce an gudanar da hare-haren saman ne daga ranar 24 zuwa 26 ga Yuni, bayan samun sahihan bayanan sirri.

Ya bayyana cewa NAF, da haɗin guiwar sauran rundunonin tsaro da hukumomin gwamnati, ta gano mafakar 'yan ta’adda da suka saba kai hare-hare da satar shanu a ƙauyukan Kakihun da Kumbashi.

Yan bindiga da dama sun bakunci lahira a Neja

“Cikin gaggawa, Jiragen NAF suka kai samame na a-zo-a-gani, inda suka hallaka dimbin 'yan ta'adda, lalata kayan aiki da abinci da kuma hana su sake taruwa a wani wuri.

Kara karanta wannan

Gwamnan Benue ya fusata da kisan matafiya 'yan Kano, ya sha alwashi

“Wannan aiki ya nuna yadda rundunar NAF ke da ƙwarewa, saurin mayar da martani da kuma ƙarfafa haɗin guiwa da dakarun sojin kasa da sauran hukumomi," in ji kakakin NAF.
Jiragen sojin sam sun yi barin wuta a Neja.
An kashe yan bindiga da yawa yayim da jiragen NAF suka kai ɗauki jihar Neja Hoto: @NigAirForce
Source: Twitter

Ejodame ya tabbatar da cewa Rundunar Sojin Sama ta Najeriya za ta ci gaba da tsare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya da kuma tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a fadin kasar.

“Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ba za ta yi ƙasa gwiwa ba a niyyarta na kare rayuka da dukiyoyin 'yan kasa da kuma tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a dukkan sassan Najeriya,” in ji shi.

Yan bindiga sun kashe sojoji a jihar Neja

A wani rahoton, kun ji cewa tsagerun ƴan bindiga sun tafka ɓarna a wani mummunan hari da suka kai sansanin sojojin Najeriya a jihar Neja.

Ana fargabar sojoji kimanin 20 ne suka rasa rayukansu a wannan harin, bayan ‘yan bindigar sun buɗe masu wuta a sansaninsu da ke Kwanan Dutse a karamar hukumar Mariga.

Rahotanni sun nuna cewa sojoji da dama sun samu raunuka a wannan hari, kuma tuni aka yi gaggawar kai su asibiti domin kula da lafiyarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262