Ta Faru Ta Kare: Tinubu Ya Rattaba Hannu kan Sababbin Dokokin Gyaran Haraji 4
- Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan sababbin kudirorin dokokin gyaran haraji huɗu, yana mai cewa "sabon babi ne ga Najeriya"
- Waɗannan sababbin dokokin za su daidaita haraji, haɓaka kuɗaɗen shiga, da inganta yanayin kasuwanci a Najeriya baki ɗaya
- Dokokin sun haɗa da dokar haraji, dokar gudanar da haraji, dokar kafa hukumar haraji da kuma dokar kafa hukumar haɗin gwiwar haraji
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan sababbin kudurorin dokokin gyaran haraji huɗu da ke da muhimmanci a yau Alhamis.
Wannan mataki ne mai girma wajen sauya fasalin tsarin kuɗi da tattalin arziki na Najeriya, kamar yadda Tinubu ya sha fada.

Source: Facebook
Tinubu ya sanya hannu kan kudurorin gyaran haraji
Shugaba Tinubu ne da kansa ya sanar da cewa ya rattaba hannu kan kudurorin hudu, wadanda suka zama doka a yanzu, a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar da shugaban kasar ya fitar ta ce:
"Na sanya hannu kan kudirorin gyaran haraji guda huɗu a yanzu haka.
"Wannan sabon babi ne ga Najeriya!"
Kudirorin guda hudu su ne: Kudirin harajin Najeriya, kudirin gudanar da harajin Najeriya, kudirin kafa hukumar haraji ta Najeriya, da kuma kudirin kafa hukumar haɗin gwiwar haraji.
An ce majalisar tarayya ta amince da kudurorin bayan tattaunawa mai zurfi da aka yi da masu ruwa da tsaki da kuma ƙungiyoyi daban-daban.
Manufofin sababbin dokokin haraji 4
A cewar fadar shugaban kasa, sababbin dokokin za su daidaita tsarin gudanar da haraji, haɓaka samar da kuɗaɗen shiga, inganta yanayin kasuwanci, da kuma jawo hankalin masu saka hannun jari na cikin gida da na waje.
An gudanar da bikin sanya hannun a fadar shugaban kasa da ke Abuja, kamar yadda rahoton jaridar The Guardian ya nuna.
Waɗanda suka halarci bikin sun haɗa da shugaban majalisar dattawa, shugaban majalisar wakilai, shugabannin masu rinjaye na duka ɗakunan biyu, da kuma shugabannin kwamitocin kuɗi a majalisar dattawa da ta wakilai.
Haka kuma, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, shugaban kungiyar gwamnonin APC, ministan kuɗi da ministan tattalin arziki, da babban Atoni Janar na Tarayya ma sun halarta.
Bayani dalla-dalla kan dokokin 4
1. Dokar haraji ta Najeriya:
Wannan dokar, da aka sani da dokar sauƙaƙa yin kasuwanci, tana neman haɗa dokokin haraji da yawa na Najeriya zuwa tsari guda, kawar da haraji masu karo da juna, da kuma sauƙaƙa biyan haraji ga masu biyan harajin.
2. Dokar gudanar da haraji na Najeriya:
Ita kuma wannan dokar za ta gabatar da tsarin doka da gudanarwa guda ɗaya don tafiyar da haraji a matakin tarayya, jihohi, da ƙananan hukumomi.

Source: Twitter
3. Dokar kafa hukumar haraji ta Najeriya:
Ita wannan dokar za ta soke dokar hukumar haraji ta tarayya da ke aiki a halin yanzu, kuma za ta kafa sabuwar hukumar haraji ta Najeriya (NRS) mai cin gashin kanta.
Dokar za ta kuma faɗaɗa aikinta da ya haɗa da tattara kuɗaɗen shiga waɗanda ba na haraji ba. Za ta kuma tsara sababbin matakan fito da gaskiya, aiki, da kuma riƙon amana.
4. Dokar kafa hukumar haɗin gwiwar haraji:
Ita wannan dokar za ta ƙirƙiro wata hukumar gudanarwa don daidaita ƙoƙarin tattara kuɗaɗen shiga a dukkanin matakan gwamnati.
Haka kuma, ta tanadi ƙirƙirar kotun kara ta haraji da ofishin babban mai sa ido kan haraji don ƙarfafa sa ido da kuma kare masu biyan haraji.
Fadar shugaban kasa ta bayyana wannan sanya hannun a matsayin wani muhimmin ci gaba wajen gina tsarin haraji na zamani wanda ya dace da manufofin ci gaban Najeriya.
Tinubu ya ki sanya hannu kan kudurin NDLEA
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya ƙi amincewa da sabon Kudirin Dokar Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA Bill, 2025).
Kudirin ya yi niyyar bai wa NDLEA damar riƙe wani ɓangare na kuɗaɗen da aka samu daga laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi.
Sai dai a cikin wasiƙar da ya aike wa majalisar wakilai, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa wannan matakin ya saɓa wa dokokin kuɗi da ake amfani da su a halin yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


