Kotu Ta Kawo Karshen Shari'ar Mama Boko Haram da wasu Mutum 2 kan Damfarar N11m

Kotu Ta Kawo Karshen Shari'ar Mama Boko Haram da wasu Mutum 2 kan Damfarar N11m

  • Wata babbar kotu a Borno ta yanke wa Mama Boko Haram da abokan aikinta hukuncin dauri na shekara 14 kan zamba
  • Tun da fari, hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ce ta mika su gaban kotun bayan samun wani korafi
  • Ana zargin mutanen uku da amfani da kungiyarsu ta agaji wajen aikata damfara da sunan kwangilar samar da na'urori guda biyu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar BornoWata babbar kotu a Maiduguri ta yanke wa Aisha Alkali Wakil da aka fi sani da “Mama Boko Haram” da abokan aikinta hukuncin dauri kan laifin zamba.

Kotu ta samu Mama Boko Haram, Tahiru Saidu Daura da Prince Lawal Shoyode da aikata zamba ta hanyar amfani da kungiyarsu.

Kara karanta wannan

Za a kafa dokar kisa ga masu taimakon 'yan bindiga a Kebbi

Mama Boko Haram da wadanda ake zargi
An kai Mama Boko Haram gaban kotu kan zamba Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa an yankewa kowannensu hukuncin daurin shekara 14 saboda damfara da ta shafi kwangilar bogi da ta kai kimanin Naira miliyan 11.

EFCC ta kai su Mama Boko Haram kotu

The Cable ta wallafa cewa mai shari’a Aisha Kumaliya ce ta yanke hukuncin a ranar Laraba, 25 ga Yuni, 2025, bayan shari’ar da ta fara tun watan Satumban 2020, bayan gurfanar da su da hukumar EFCC.

An gurfanar da su bisa tuhume-tuhume guda biyu — haɗin baki da kuma karɓar kudi ta hanyar yaudara, da ya shafi ayyukansu a gidauniyar Complete Care and Aid Foundation.

Shugaban hukumar EFCC
An kama Mama Boko Harak da sauran mutanen da laifi Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Mutanen uku ne ne ke jagorantar gidauniyar a matsayin shugabar gudanarwa, manajan shirye-shirye da kuma darakta na ƙasa.

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana, sun karɓi N11m daga wani mai suna Muhammed Ambare na kamfanin Muhammed Ambare Ventures a watan Yulin 2018.

Kara karanta wannan

Sanata Ningi ya dauki zafi, yana son majalisa ta binciki rashin biyan yan kwangila hakkokinsu

Kotu ta kama su Mama Boko Haram da zamba

EFCC ta bayyana cewa sun karɓi kuɗin ne da sunan cewa za su samar da na’urorin hoto na X-ray guda biyu da kuma gyara su, daga baya aka gano bogi ce.

A cewar tuhumar guda na biyu:

“Ku, Aisha Alkali Wakil, Tahiru Saidu Daura, Prince Lawal Shoyode da Saidu Mukhtar da ya shigaemala da nufin damfara, kun karɓi Naira miliyan 11 daga hannun Muhammed Ambare da sunan cewa za ku aiwatar da kwangilar samar da na’urorin X-Ray guda biyu samfurin Model 1800, wanda kun san cewa ba gaskiya ba ne...”

Dukkanin wadanda ake tuhuma sun musanta zargin, wanda hakan ya sa aka ci gaba da cikakken shari’a.

Lauyoyin gwamnati, Mukhtar Ali Ahmed da S.O. Saka, sun gabatar da shaida guda ɗaya da kuma takardu da dama a matsayin hujja.

Mai shari’a Kumaliya ta same su da laifi a tuhume-tuhume biyu, inda ta yanke musu hukuncin daurin shekara bakwai a kowanne, wanda zai gudana a lokaci guda.

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 da suka ja hankalin duniya a kwana 12 na yakin Iran da Isra'ila

Kotu ta kuma umarci su biya wa wanda suka yaudara kuɗi N8m, kuma gazawar biyan kuɗin zai janyo musu ƙarin shekara bakwai a gidan yari.

Shaidun da aka gabatar kan Mama Boko Haram

A baya, kun ji wani babban shaida mai suna Olaleye Isma’il ya bayyana a gaban wata babbar kotun jihar Borno cewa Aisha Alkali Wakil da aka fi sani da Mama Boko Haram.

Mama Boko Haram, wacce ta kafa kuma ke shugabantar gidauniyar agaji ta a Borno ta fuskanci kotu a gaban mai shari’a Aisha Kumaliya kan tuhume-tuhume guda biyar.

Tare da ita a kan shari’ar akwai Dahiru Saidu, shugaban shirye-shiryen gidauniyar, da Prince Lawan Shoyode, daraktan shirin na kasa, suka ana zargin su da zamba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng