Yadda Mama Boko Haram da wasu suka karkatar da kudin kwangila N111.7m - Shaida

Yadda Mama Boko Haram da wasu suka karkatar da kudin kwangila N111.7m - Shaida

Wani shaida, Olaleye Isma’il, a ranar Litinin, 16 ga watan Maris, ya fada ma Wata babbar kotun Borno a Maiduguri cewa Aisha Wakil wacce aka fi sani da Mama Boko Haram, ta hada kai da wasu mutane biyu wajen karkatar da kudin kwangila har naira miliyan 111.7.

Mama Boko Haram wacce ta kasance shugaba kuma wacce ta kafa gidauniyar agaji ba Complete Care and Aid Foundation, na fuskantar shari’a a gaban Justis Aisha Kumaliya kan tuhume-tuhume biyar da suka hada da damfara.

Wadanda aka hada a matsayin sauran da ake kara a tuhumar sun hada da shugaban shirin da daraktan shirin na kasa, Dahiru Saudi da Prince Lawan Shoyode.

Isma’il, mai bincike a hukumar yaki da cin hanci da rashawa, yayinda ya jagoranci hujjar daga Benjamin Manji, ya fada ma kotu cewa daga cikin binciken da aka yi a zargin zambar, an yi wasu nazari a kan wayoyin Samsung din wadanda ake karar.

Yadda Mama Boko Haram da wasu suka karkatar da kudin kwangila N111.7m - Shaida

Yadda Mama Boko Haram da wasu suka karkatar da kudin kwangila N111.7m - Shaida
Source: Twitter

Ya ce: “kan binciken kwangilar kamar yadda kamfanin Nyeuro International Limited ya yi zargi, na farko shine kan kwangilar biyan naira miliyan 45 cikin asusun bankin wani Saidu Mukhtar Hospital Equipment kamar yadda wanda ake karar ta yi umurni.

“Kwangila na biyu shine cewa an umurci Nyeuro da ya biya naira miliyan 1.650 a asusun Tahiru Saidu Daura domin shigo da wani na’ura. Bincike ya nuna cewa babu wannan kwangilar.

“Hakazalika an umurci Nyeuro International Limited da ya shigo da farin wake na naira miliyan 66, wanda aka shigo da shi wajen ajiye na gidauniyar Complete Care and Aid Foundation, wanda wadanda ake kara suka sa hannu”.

Bincike ya kuma nuna cewa yan kwangilar sun biya kudin a cikin asusun Mukhtar.

Ya fada ma kotu cewa a yayin tambayoyi, wanda ake kara na biyu ya yarda a jawabansa cewa wannan tsarin na biyan kudin na dawowa.

KU KARANTA KUMA: Duk da tarin bashin N33tr Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta cikin matsala

A cewarsa, koda dai Wakil da Shoyode sun karyata masaniya kan kwangilar da ake magana a kai, bincike ya nuna cewa sun zanta kan haka a WhatsApp kuma sun amince da tsarin juyar da kudin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel