'Yan Bindiga Sun Farmaki Kauyukan Sokoto, an Samu Asarar Rayuka
- Miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki kan wasu ƙauyukan jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma
- Ƴan bindigan sun hallaka mutane takwas a hare-haren da suka kai a wasu ƙauyuka guda biyu na ƙaramar hukumar Tangaza
- Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da aukuwar harin wanda aka kai da tsakar rana
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Ƴan bindiga sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.
Ƴan bindigan sun hallaka mutum takwas tare da jikkata wani mutum ɗaya a hare-haren da suka kai a wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Tangaza.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa maharan suna ɗauke da makamai na zamani kuma sun zo ne a ƙasa da kan babura.
Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Sokoto

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Jami'an DSS sun cafke rikakkun 'yan bindiga bayan dawowa daga Saudiyya
Ƴan bindigan sun fara kai harin ne a ƙauyen Baidi, inda suka harbe wani mutum ɗaya wanda hakan ya jawo ya jikkata.
“Bayan haka sai suka wuce zuwa ƙauyen Sabiyo, inda suka rutsa da wasu manoma da ke aiki a gonakinsu, suka kashe guda shida a wurin."
- Wata majiya
Daga cikin waɗanda aka kai wa hari har da wani matashi mai suna Aminu Sama’ila wanda aka harba a wuya da ƙirji. An garzaya da shi zuwa asibitin ƙwararru na Sokoto don ceto rayuwarsa.
Majiyar ta ƙara da cewa wani manomi mai suna Usman Sama’ila har yanzu ba a san inda yake ba, kuma jami’an tsaro tare da haɗin gwiwar mazauna yankin na ci gaba da bincike domin gano shi.
Ganau sun bayyana cewa maharan sun buɗe wuta ba tare da kakkautawa ba, wanda hakan ya haifar da firgici da ruɗani a cikin al’ummar ƙauyen, inda da dama suka tsere don tsira da rayukansu.
Ƴan sanda sun yi bayani kan harin
Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da aukuwar harin tare da kisan mutanen da ƴan bindigan suka yi.

Source: Original
Mai magana da yawun rundunar, DSP Ahmed Rufai, ya ce an kashe mutanen ne a lokacin wani hari na haɗin gwiwa da ake zargin ƴan Lakurawa ne suka kai a ƙauyukan Baidi da Sabiyo a ranar Talata da rana.
"Mutane takwas ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da mutum ɗaya da ya jikkata ke samun kulawa a asibiti."
- DSP Ahmed Rufai
A halin yanzu, hukumomin tsaro sun ƙaddamar da farautar waɗanda suka kawo harin a ƙauyukan.
Ƴan bindiga sun sace fasinjoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan binɗiga sun tare matafiya da ke kan hanyar zuwa birnin Makurdi na jihar Benue.
Ƴan bindigan sun yi awon gaba da dukkanin fasinjojin da ke cikin motar waɗanda suka taso daga birnin Abeokuta na jihar Ogun.
Rundunar ƴan sandan jihar Benue ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa ta tura ƙwararrun jami'ai da jirage marasa matuƙa domin ceto fasinjojin da ƴan bindigan suka sace.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
