Gwamnati Ta Ɗage Ranar Ɗaukar Ma'aikata 30,000 a Hukumar CDCFIB, Ta Faɗi Dalili
- Gwamnatin tarayya ta dage ranar fara ɗaukar ma'aikata a NSCDC, Immigration, da sauran hukumomi zuwa ranar 14 ga Yuli, 2025
- Hukumar CDCFIB ta sanar da cewa ta canja shafin da za a cike neman guraben aikin, kuma sabon shafin zai fara aiki ne a sabuwar ranar
- An gargaɗi masu neman aikin cewa cike guraben aikin kyauta ne, don haka su yi taka-tsantsan da masu damfarar mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da dage ranar fara ɗaukar ma'aikata a hukumomin tsaro da ke ƙarƙashin ma'aikatar cikin gida.
An ɗage ranar da 'yan Najeriya za su fara cike neman aikin daga 26 ga Yuni, 2025, zuwa 14 ga Yuli, 2025, wanda ke nufin cewa an samu jinkiri na kusan makonni uku.

Kara karanta wannan
'Har gida muka cin masa': Gwamnatin Zamfara ta faɗi illar da ta yi wa Bello Turji

Source: Twitter
An dage ranar fara daukar ma'aikata 30000
Hukumar NSCDC, gidajen gyaran hali, shige da fice, kashe gobara da Immigration (CDCFIB) ce ta sanar da wannan canjin a sanarwar da ta fitar a ranar Laraba, 25 ga Yuni, 2025, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba a bayyana takamaiman dalilin dage ranar ba, amma an ce saboda "gyara tsarin daukar aiki" ne.
Rahoton ya bayyana cewa sabon shafin neman ayyuka a wadannan hukumomi, wanda yanzu za a iya shiga ta recruitment.cdcfib.gov.ng, zai fara aiki daga ranar 14 ga Yuli, 2025.
Sanarwar ta ce:
"Hukumar CDCFIB tana sanar da jama'a cewa shafinta na daukar ma'aikata da aka shirya buɗewa ranar Alhamis 26 ga Yuni, 2025, yanzu zai buɗe ne a ranar Litinin 14 ga Yuli, 2025.
"Har ila yau, sabon adireshin shafin na hukumar ga masu neman shiga aikin da suka zaɓa yanzu shine: recruitment.cdcfib.gov.ng.
"An bukaci masu neman aikin da su lura da waɗannan canje-canje, tare da tunatar da su cewa cike gurbin kowanne aiki kyauta ne, ba tare da an biya sisin kwabo ba."
Muhimman abubuwan lura yayin neman aikin
Wannan shirin ɗaukar ma'aikatan zai mayar da hankali ne kan cike guraben aiki a hukumar NSCDC, hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS), hukumar kashe gobara ta tarayya (FFS), da kuma hukumar gidajen gyaran hali (NCoS).
Wannan shirin na ɗaukar ma'aikata, wanda aka sanar da shi a farkon makon nan, ya shafi masu neman matsayin Inspectorate, da Assistant Cadres.
Akwai kuma takamaiman guraben aiki kamar Sufeto na NCoS wanda ke buƙatar masu neman aikin su mallaki kwalin digiri na BSc a fannin likitanci da tiyata.
Dole ne masu neman aikin su mallaki shaidar zama ƴan Najeriya da ke tsakanin shekara 18 zuwa 35, sannan tsayinsu ya kai mita 1.65 ga maza, mita 1.60 ga mata, kuma su samu mafi ƙarancin kiredit huɗu ko biyar a SSCE, ciki har da Ingilishi da Lissafi.
Har ila yau, dole ne su kasance ba a taba samunsu da aikata laifuffuka ba kuma su gabatar da takardar shaidar lafiyar jiki. Uwa uba, ana so a nemi aiki a ma'aikata daya ne kawai.

Source: Twitter
Tarihin kafuwar CDCFIB da aikin hukumominta
Hukumar CDCFIB, wacce aka kafa a ƙarƙashin Dokar No. 14 ta 1986, tana sa ido kan waɗannan hukumomin tsaro na farar hula, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa a tsarin tsaro da agajin gaggawa na Najeriya.
NSCDC, wacce aka kafa a 1967, tana maida hankali kan tsaron farar hula, yayin da NIS, wacce aka kafa a 1958, ke kula da tsaron iyakoki.
Hukumar FFS, wacce ta fara tun 1901, tana kula da kashe gobara, yayin da ita hukumar NCoS take kula da gidajen gyaran hali.
Hukumar ta nemi afuwar rashin jin daɗin da dage ranar ya haifar, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.
Gwamnatin Tinubu za ta dauki matasa aiki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Bola Tinubu ta buɗe shafin ɗaukar matasa aiki a ƙarƙashin Shirin Kiwon Lafiya na Ƙasa (NHFP), wanda zai shafi dukkan jihohin Najeriya.
Gwamnati ta bayyana cewa za ta bai wa waɗanda aka ɗauka aikin alawus mai tsoka da kayan aiki na zamani, da nufin kawo sauyi mai inganci a fannin kiwon lafiya.
Legit Hausa ta yi cikakken bayani kan yadda matasa 'yan ƙasa da shekaru 35 za su iya neman wannan aikin, tare da jerin takardun da ake buƙata.
Asali: Legit.ng


