Jami'an DSS Sun Harbe Dan Sanda saboda 'Rashin Fahimta' a Jihar Anambra
- Wani jami'in dan sanda, Sufeto Bello Abdulahi ya rasa ransa bayan da aka harbe shi yayin aikin duba ababen hawa a Uli, jihar Anambra
- Rahotanni sun bayyana cewa jami’an DSS ne suka harbe dan sandan bayan an samu takaddama a lokacin da ake tsayar da abin hawansu
- Hukumar DSS ta fara bincike kan lamarin, yayin da ake kira da a inganta haɗin guiwar jami’an tsaro don hana irin wannan faruwa nan gaba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Anambra – Wani jami’in ‘yan sanda mai mukamin Sufeto da ke aiki a Awka, ya rasa ransa bayan da aka harbe shi yayin aikin duba ababen hawa a garin Uli da ke karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.
Rahotanni sun bayyana cewa harbin ya faru ne a sakamakon rashin fahimta da ya kunshi jami’an Hukumar Tsaro ta DSS.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 24 ga Yuni, da misalin ƙarfe 5.50 na yamma a kan titin Onitsha/Owerri kusa da tashar mai ta Danaks a Uli.
Yadda aka kashe dan sanda a Anambra
Majiyoyi sun ce tawagar ‘yan sanda masu sintiri a hanya sun tsayar da wata mota kirar Toyota Sienna, wacce ta fito daga wata ƙaramar hanya tana zuwa cikin babban titi a hanyar da ba ta dace ba.
Ganau sun bayyana cewa mutanen cikin motar, waɗanda ke sanye da bakaken kaya na ɗauke da bindigu masu linzami, kuma sun ƙi bin umarnin ‘yan sanda, lamarin da ya janyo cece-kuce.

Source: Twitter
Rahoton ya ƙara da cewa mutanen cikin motar sun buɗe wuta kan jami’an ‘yan sanda, inda suka harbe Sufeto Bello Abdulahi a gefen ƙasa, kuma ya samu rauni mai muni.
An garzaya da jami’in da aka harba zuwa Asibitin Our Lady of Lourdes da ke Ihiala, kafin daga bisani a tura shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Nnewi, inda aka tabbatar da rasuwarsa.
An adana gawar dan sanda a Anambra
Rahotanni sun tabbatar da cewa an ajiye gawar jami’in a dakin ajiyar gawa na asibitin domin gudanar da bincike da kuma adanawa.
Sannan daga baya, an gano cewa jami’an DSS ne da ke aiki a gundumar Ihiala, suka yi harbin, kuma sun arce daga wurin bayan afkuwar lamarin.
Zuwa yanzu, an tabbatar da cewa an riga an sanar da hedikwatar hukumar DSS da ke Awka game da lamarin, kuma an fara gudanar da bincike don gano ainihin abin da ya faru.
Wannan mummunan lamari ya janyo kira daga al’umma da ke neman a inganta haɗin guiwar hukumomin tsaro don kauce wa irin wannan hatsaniya a nan gaba.
DSS, Sojoji sun fatattaki yan ta'adda
A wani labarin, mun ruwaito cewa an samu gagarumar nasara a jihar Neja yayin da jami’an DSS tare da hadin gwiwar dakarun sojojin Najeriya farmaki yan ta'adda.
Jami'an sun kai hari mafakar wasu gungun 'yan ta’adda, ayayin wannan artabu, an hallaka ‘yan bindiga masu yawa da ake zargin mayaƙa ne karkashin Dogo Gide da Leyi.
Wannan aiki na hadin gwiwa ya samo asali ne daga wani hari da ‘yan bindigan suka kai garin Chibani da ke karamar hukumar Munya ta jihar Neja.
Asali: Legit.ng

