Za a Kafa Dokar Kisa ga Masu Taimakon 'Yan Bindiga a Kebbi
- Gwamnan Kebbi, Nasir Idris ya ce gwamnati na shirin kafa dokar hukuncin kisa ko daurin shekaru 25 ga masu ba wa ‘yan bindiga bayanai
- Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan mataki na zuwa ne bayan wani hari da ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 30 a masarautar Zuru
- Gwamna Nasir Idris ya kuma bukaci dattawan jihar da dukkan masu ruwa da tsaki su guji siyasantar da batun rashin tsaro a jihar Kebbi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da shirin kafa doka da za ta tanadi hukuncin kisa ko daurin shekaru 25 ga duk wanda aka kama yana taimaka wa ‘yan bindiga da bayanai.
Wannan mataki ya biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a wasu kauyuka na masarautar Zuru wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 30.

Source: Facebook
Legit ta gano bayanan da gwamnan ya yi ne a cikin wani sako da tashar gwamnatin Najeriya ta NTA ta wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Nasir Idris ne ya bayyana haka yayin da yake ziyarar jaje ga al’ummar Kebu da Tadurga da ke masarautar Zuru.
Nasir Idris ya ce lokaci ya yi da za a dauki matakin hukunta masu taimaka wa ‘yan ta’adda domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
'Yan bindiga: Za a saka dokar kisa a Kebbi
Nasir Idris ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da ‘yan bindiga, satar shanu da garkuwa da mutane da ke addabar yankuna da dama na jihar Kebbi.
Gwamna ya ce za su gabatar da kudurin doka domin tabbatar da hukuncin kisa ko kuma daurin shekaru 25 ga duk wanda aka kama yana ba wa ‘yan bindiga bayanai.
Vanguard ta wallafa cewa gwamnan ya ce wannan mataki zai zama darasi ga wasu da ke taimakon 'yan bindiga cikin jama’a.
Ya ce hare-haren da ake ci gaba da kai wa a wasu yankuna sun samo asali ne daga bayanan da wasu bata-gari ke bai wa ‘yan bindiga.

Source: Twitter
Gwamnan ya jaddada cewa hakan ke kara tsananta matsalar tsaro da tabarbarewar rayuwar al’umma.
Nasir Idris ya ce gwamnati za ta kara zurfafa hadin gwiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an kakkabe duk masu hannu wajen taimaka wa ‘yan ta’adda.
An gargadi 'yan siyasa kan lamarin tsaro
A yayin ziyarar, Gwamna Idris ya yi kira ga dattawa da shugabannin al’umma da su guji siyasantar da lamarin tsaro.
Ya yi magana ne yana mai cewa hakan yana kawo cikas ga kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya a jihar.
Jihar Kebbi na daya daga cikin jihohin Arewa da ke fuskantar matsalar tsaro, musamman a yankunan da ke makwabtaka da jihohin Zamfara da Sokoto.
Lakurawa sun sa sharudan noma a Kebbi
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan ta'addan Lakurawa sun kafa sharudan noma a wasu garuruwa da ke jihar Kebbi.
Mutanen yakunan da abin ya shafa sun ce 'yan ta'addan sun hana su amfani da injunan zamani wajen yin ayyukan gona.
Rahotanni sun nuna cewa Lakurawa na tilasta mutane amfani da shanu, amma kuma suna satar shanun idan mutane na aiki da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

