Atiku Ya Tsokani Tinubu, Ya Hango Ruɗani a Ɓullar Sabon 'Abokin Karatunsa'
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa akwai shakku a cikin ikirarin Shugaban ƙasa kan abokin karatunsa
- A ranar Litinin ne shugaban kasa ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alaƙa a tsakaninsa da ɗan kasuwar Belarus, Alexander Zingman
- Ofishin harkokin labaran Atiku Abubakar ya bayyana fargabar cewa wannan Zingman din na da hannu a zarge-zargen safarar makamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kalubalanci ikirarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan 'sabon' abokin karatunsa ne.
Shugaban kasa ya bayyana wani ɗan kasuwa daga ƙasar Belarus, Alexander Zingman, da cewa abokinsa ne kuma sun yi makaranta tare a jami’ar Chicago State University (CSU).

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Tinubu ya bayyana haka ne a yayin ƙaddamar da shirin Renewed Hope Mechanisation Programme a Abuja ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ya ce bayan karatunsu a CSU, ba su taɓa tunanin cewa zai zama shugaban Najeriya ba, kuma Zingman zai zama ɗan kasuwa mai tasiri a Belarus ba.
Atiku yana shakku kan abokin karatun Tinubu
Business Day ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya nuna shakku a kan mutumin da Tinubu ke ikirarin cewa abokin karatunsa ne saboda dalilai da dama.
A sanarwar da ofishin tsohon mataimakin Shugaban kasa ya fitar, ya ce:
"Maimakon ikirarin Tinubu ya kawo kwanciyar hankali, sai ya ƙara haifar da ruɗani, musamman la'akari da yadda tarihi da takardun karatunsa ke ci gaba da zama abin tambaya”
"Sanarwar ta bayyana cewa bayanan da ke akwai na nuna cewa an haifi Zingman ne a 1966, kuma an ce Tinubu ya kammala CSU a 1979."

Kara karanta wannan
Bidiyo: Yadda Shugaba Tinubu ya gabatar da abokin karatunsa a Amurka ya ƙayatar da jama'a
Atiku ya jero tambayoyi ga Tinubu
Atiku Abubakar ya bayyana mamakin yadda duk wasu bayanai a kan takardun karatun sa shugaban kasa ke kara haddasa rudani, maimakon su bayar da amsoshin da ake nema.

Source: Facebook
Sanarwar ta cigaba da cewa:
“Shin wannan Alex Zingman ɗin da ake ce-ce-ku-ce da sunansa – wanda ake danganta shi da safarar makamai da damfara a Afrika – shi ne ɗin da Tinubu ke magana a kansa?”
“Shin me ya sa duk wani yunƙuri na fayyace tarihin karatunsa ke ƙara haddasa tambayoyi maimakon amsoshi?”
“Me ya sa har yanzu ba a samu ko ɗaya daga cikin tsofaffin ɗalibai ko malamai da suka tabbatar sun yi karatu da shi a kwalejin gwamnati ta Legas ko jami'ar Chicago?”
Atiku ya kuma jaddada cewa mutanen Najeriya na da 'yancin sanin gaskiya game da tarihin shugabanninsu.
An shawarci Atiku ya yafe takara
A baya, mun wallafa cewa Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya shawarci Atiku Abubakar da ya daina fafutukar neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 mai zuwa.
A tsokacin da ya yi, Baba-Ahmed ya nanata cewa lokaci ya yi da tsohon dan takarar shugaban kasa zai daina neman mulki, ya dora alhakin shugabanci a hannun matasa.
Ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa na tsawon shekaru takwas a zamanin shugaba Olusegun Obasanjo, ya riga ya taka rawar gani a tarihin siyasar Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

