Malamin Musulunci Ya Yi Tir da Harin Iran a kan Qatar da Iraq, Ya Tona Manufar Isra'ila

Malamin Musulunci Ya Yi Tir da Harin Iran a kan Qatar da Iraq, Ya Tona Manufar Isra'ila

  • Sheikh Aliyu Muhammad Sani ya yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai Qatar da Iraq a matsayin ramuwar gayyar harin Amurka
  • Malamin ya kara da cewa harin da aka kai kasashen biyu, ya sabawa ƙa’idar Musulunci da haɗin kan ƙasashen Musulmi da aka cimma
  • Malamin ya zargi Iran da Isra’ila da yin yaƙin ne a matsayin wata dabarar raunana kafin kasashen Larabawa, ba wai yakar junansu da gaske ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Gabas ta Tsakiya – Malamin addinin Musulunci, Sheikh Aliyu Muhammad Sani, ya bayyana damuwarsa da abin da ya kira zalunci da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Shehin Malamin ya caccaki ƙasashen Iran da Isra’ila bisa hare-haren da ke faruwa a yankin, inda ya bayyana cewa sune matsalar Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra'ila na fuskantar barazana, Trump ya gano masu laifi

Jagororin Iran da Isra'ila
An zargi Isra'ila da Iran da kokarin tayar da husuma a Gabas ta Tsakiya Hoto: Getty
Source: Getty Images

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya malamin ya yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai kan ƙasashen Qatar da Iraq.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iran da Isra'ila sun zama matsala Inji Shehin

Malamin ya ce abin da ke faruwa a yanzu ya tabbatar da cewa Iran da Isra’ila ne manyan matsalolin yankin Gabas ta Tsakiya.

Ya kara da zargin cewa yakin da ake gani tsakaninsu kamar wata dabara ce domin su ci gaba da raunana ƙasashen Larabawa.

Shehin malami ya caccaki Iran
Malami ya ce harin Qatar da Iraq bai dace ba Hoto: Getty
Source: Twitter

Ya ce:

“Yanzu dai ya bayyana a fili cewa: Iran da Isra’ila su ne matsala a Gabas ta Tsakiya. Su ne azzalumai a tsakanin ƙasashen Musulmi.”
“Wannan hari shi yake ƙarfafa zargin cewa wannan yakin na Iran da Isra’ila kawai wasan kwaikwayo ne. Ƙasashen Larabawa ne suke so su yaƙa.”

An yi addu'a kan yakin Iran da Isra'ila

A ƙarshe, Sheikh Aliyu Muhammad Sani ya roki Allah Subhanahu wa ta'ala ya kare sauran ƙasashen Musulmi, tare da fatan ganin ƙarshen waɗanda ke haddasa rikice-rikicen a yankin.

Kara karanta wannan

Yaki da Isra'ila: Jerin kasashen da suka gargadi Trump bayan kai hari a Iran

"Ya Allah Ka mayar da kaidinsu kansu.Ya Allah Ka sa ƙarshensu ne ya zo, su duka biyun."

Shehin malamin na wannan adu'a ne a lokacin da Isra'ila ke zargin Iran da kai mata hari, bayan Amurka ta bayyana cewa an cimma tsagaita wuta a tsakanin kasashen biyu.

Isra'ila ta amince da tayin Amurka

A wani labarin, mun wallafa cewa Rahotanni daga yankin Gabas ta Tsakiya sun tabbatar da cewa ƙasashen Iran da Isra’ila sun amince da tsagaita wuta bayan kwanaki 12 na musayar makamai.

A wata sanarwa da Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya fitar da safiyar Talata, ya tabbatar da cewa ƙasarsa ta amince da tsagaita wuta da aka shimfiɗa da haɗin gwiwar Amurka.

Duk da amincewar da aka cimma, Netanyahu ya yi gargaɗi cewa idan aka karya wannan tsagaita wuta, Isra’ila za ta mayar da martani da ƙarfi, yana mai cewa babu wata sassauci da za ta yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng