Bayan Matatar Dangote, Kamfanin NNPCL Ya Kara Farashin Man Fetur

Bayan Matatar Dangote, Kamfanin NNPCL Ya Kara Farashin Man Fetur

  • Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya yi ƙari kan farashin da yake sayar da kowace lita a gidajen man da ke ƙarƙashinsa
  • A gidajen man NNPCL da ke Abuja da Legas an lura da ƙarin da aka samu kan yadda ake siyar da kowace litar man fetur
  • A babban birnin tarayya watau Abuja, farashin kowace litar man fetur ya koma N945 saɓanin N910 da ake sayarwa a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An wayi gari da labarin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya ƙara farashin litar mai a gidajensa.

Kamfanin NNPCL ya ƙara farashin kowace lita ta man fetur zuwa Naira 915 a Legas da Naira 945 a Abuja.

NNPCL ya kara farashin man fetur
NNPCL ya kara kudin litar man fetur Hoto: @nnpclimited
Source: Twitter

Jaridar TheCable ta lura a ranar Litinin cewa farashin man ya ƙaru zuwa N915 a wasu gidajen sayar da man NNPCL da ke Legas.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'asa, sun hallaka tsohon shugaban jam'iyyar PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPCL ya ƙara farashin man fetur

Wannan sabon farashi ya nuna ƙarin Naira 45 daga tsohon farashin N870 a Legas da kuma ƙarin Naira 35 daga tsohon farashin N910 a Abuja.

A gidan man NNPCL da ke Fin Niger, titin Badagry Expressway, an sayar da litar man a kan N915.

Haka kuma a gidan man NNPCL da ke Igando, litar man ta kai N915.

A babban birnin tarayya Abuja kuwa, an sayar da man a farashin N945 a yankin Federal Housing da ke Kubwa, wanda ya ƙaru daga tsohon farashin N910.

Wani direban Uber a Abuja, Ibrahim Zulkiful, ya tabbatarwa da Legit Hausa cewa NNPCL ya yi ƙarin kuɗin fetur a gidajen man da ke ƙarƙashinsa.

"Eh tabbas an yi ƙari na sha mai yau a NNPCL, suna siyar da kowace lita a kan N945."
"Sauran gidajen mai su ma sun yi ƙarin kuɗi. Matrix da AY Shafa suna sayarwa a kan N950 kowace lita."

Kara karanta wannan

Dangote ya kara farashin fetur yayin da yakin Iran da Isra'ila ke kara kamari

- Ibrahim Zulkiful

Gidajen mai sun ƙara farashin fetur

Wasu gidajen sayar da mai masu zaman kansu suma sun ƙara farashin man fetur a Legas.

Gidan man MRS, wanda ke haɗin gwiwa da matatar Dangote, ya ɗaga farashin man zuwa N925 a Legas, daga N875 da ake sayarwa a baya.

Farashin man fetur ya karu a gidajen NNPCL
NNPCL ya kara farashin man fetur Hoto: @nnpclimited
Source: Getty Images

Wannan ci gaban na zuwa ne kwanaki biyu bayan matatar Dangote ta ƙara farashin na man fetur zuwa N880 kowace lita.

Gidan man TotalEnergies ya kara farashin lita ɗaya zuwa N910, daga tsohon farashin N879 da ake sayarwa a baya.

A gidan man Oluwafemi Arowolo Petroleum da ke Iba, farashin man ya tashi zuwa N920 kan kowace lita.

Dangote zai fara raba man fetur kyauta

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar man Dangote da ke birnin Legas ta shirya kawo sabon tsari wajen rabon man fetur ga abokan hulɗarta.

Matatar ta ce daga ranar 15 ga Agusta, 2025, za ta fara raba fetur da dizel ga ƴan kasuwa, dillalan mai, kamfanoni, masana’antu da sauran masu buƙatar mai da yawa.

Alhaji Aliko Dangote wanda ya sanar da hakan ya bayyana cewa tsarin rabon zai kasance kyauta ne ga dukkanin masu saye daga matatar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng