Malamin Addini Ya Watsawa Gwamna Kasa a Ido, Ya Ki Karbar Kyautar N30m a bainar Jama'a
- Gudunmawar da gwamnan jihar Kebbi ya ba da a wajen wani taron bishara da cocin Dunamis Internation Gospel Centre ta shirya
- Dr. Paul Enenche ya ƙi karɓar gudunmawar Naira miliyan 30 da Gwamna Nasir Idris ya ba da
- Babban faston ya bayyana cewa kamata ya yi a yi amfani da kuɗaɗen wajen yi wa jama'a ayyukan da suka dace
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Babban faston cocin Dunamis International Gospel Centre, Dr. Paul Enenche, ya ƙi karɓar gudummawar kuɗi daga wajen Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi.
Fasto Paul Enenche ya ƙi karɓar gudunmawar Naira miliyan 30 da gwamnan ya bayar yayin wani babban taron bishara da cocin ta shirya a jihar.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a wajen taron bishara warkarwa na jihar Kebbi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wajen taron Gwamna Nasir Idris ya samu wakilcin kwamishinan harkokin jama’a na jihar Kebbi, Zayyanu Umar Aliero.
Gwamna Nasir ya ba Fasto gudunmwar N30m
Zayyanu Umar Aliero ya sanar da ba da gudummawar ta tsabar ƙuɗi a madadin gwamnan, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Kwamishinan ya sanarwa da mahalarta taron cewa gwamnan ya amince da ba da gudunmawar Naira miliyan 30, kuma an zo da su wurin.
"Gwamnanmu, mai girma Dr Nasir Idris, gwamna mai imani ya amince da bayar da gudummawar Naira miliyan 30 ga kwamitin shirya wannan taro."
“Wannan kuɗi yana nan a hannu, domin idan Gwamna Nasir Idris zai bayar da gudummawa, yana tabbatar da cewa yana zuwa da kuɗin kai tsaye."
"Don haka kafin na bar wannan dandalin, zan miƙa wannan gudummawar ta Naira miliyan 30 a hannu."
- Zayyanu Umar Aliero
Fasto Enenche ya ƙi karɓar kuɗin
Sai dai, Dr. Enenche ya ƙi karɓar kuɗin, inda ya hau kan dandalin ya roƙi a mayar da kuɗin zuwa wajen yin wasu ayyukan jin ƙai.
“Idan akwai gidan marayu ko wani abu makamancin haka, da yardarku, sai a yi amfani da wannan kuɗin a can. A'a. Ba za a karɓa ba."
- Dr Paul Enenche

Source: Twitter
Daga bisani, Enenche ya bayyana matsayin cocin, inda ya jaddada cewa ya kamata kuɗin gwamnati su kasance don amfanin jama’a kawai.
Ya ba da shawarar cewa a mayar da kuɗin ga wata hukuma ta addini da gwamnati ta amince da ita, kamar hukumar kula da mahajjata Kirista ko ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).
Zayyanu Umar Aliero, bayan an ƙi karɓar kuɗin, ya bayyana fahimtar su dangane da matakin da Enenche ya ɗauka.
“Ba su karɓa ba saboda duk abin da yake yi, yana yi ne domin Allah. Mun yaba sosai kuma muna godiya matuƙa da irin abin da yake aikatawa a jiharmu."
- Zayyanu Umar Aliero
Gwamnatin Kebbi za ta tura ɗalibai Saudiyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta shirya tura ɗalibai zuwa ƙasar Saudiyya don ƙaro karatu.
Gwamnatin shirya ɗaukar nauyin ɗalibai 70 zuwa ƙasar Saudiyya domin karatun digiri a ɓangaren ilmin zamani da na addini.
A ƙarƙashin shirin, za a ɗauko ɗalibai daga ƙananan hukumomi 20 na jihar domin kai su ƙasa mai tsarki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

