Jirgi Ya Gamu da Mummunan Hatsari Ana Tsakiyar Tafiya, Mutane Sun Rasu a Jihar Kebbi

Jirgi Ya Gamu da Mummunan Hatsari Ana Tsakiyar Tafiya, Mutane Sun Rasu a Jihar Kebbi

  • Mutane huɗu sun rasa rayukansu da wani jirgin ruwa ya nutse ana tsakiyar tafiya a Kogin Yauri da ke jihar Kebbi
  • Jami'an ba da agajin gaggawa sun kai ɗauki wurin amma har yanzu ba a gano sauran fasinjojin da ke cikin jirgin ba
  • Shugaban ƙungiyar agaji ta Red Cross reshen Yauri, Nafiu Nuhu, ya ce suna ci gaba da lalube a kogin domin gano gawarwakin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kebbi - Aƙalla mutane hudu ne aka tabbatar sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya faru a kogin Yauri da ke Jihar Kebbi a ranar Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu ba a gano sauran fasinjojin jirgin ba yayin da jami'ai da mutanen gari ke ci gaba da lalube a kogin domin ciro su.

Kara karanta wannan

Ana batun sulhu a Katsina, ƴan bindiga sun kashe jami'an tsaro da tulin manoma

Kwale-kwale ya nutse a jihar Kebbi.
An rasa mutum 4 yayin da wani jirgin ruwa ya nutse a kogi a jihar Kebbi Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Vangurad ta ce hatsarin ya faru ne lokacin da wani karamin jirgin ruwa watau Kwale-kwale da ke ɗauke da fasinjoji ya nutse a tsakiyar kogin.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da kogin ya cika sakamakon ruwan sama, wanda hakan ya jawo haɗarin zirga-zirgar ruwa a yankin.

Hatsarin jirgin ya yi ajalin mutane a Kebbi

Shugaban ƙungiyar agaji ta Red Cross reshen Yauri, Nafiu Nuhu, wanda ke jagorantar tawagar agajin gaggawa, ya bayyana cewa sun tabbatar da mutuwar mutum uku nan take.

Haka zalika ya ce an gano gawarsu kuma an miƙa su ga iyalansu domin gabatar da jana'iza a wani ƙauye da ke cikin Jihar Neja.

Wani mazaunin garin, ya shaida wa manema labarai cewa yawancin fasinjojin jirgin suna kan hanya ne zuwa kasuwa ko ziyartar iyalai lokacin da hatsarin ya afku.

Jami'an agaji na ci gaba da lalube a ruwa

Nafiu Nuhu ya kara da cewa, ayyukan ceto don gano waɗanda suka bace na ci gaba da gudana, tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya (NIWA) da kuma Red Cross.

Kara karanta wannan

Kisan Benue ya girgiza Najeriya, Kwankwaso, Pantami, Saraki sun yi magana

Ya ce tuni an tura masu bincike da ma’aikatan ceto zuwa yankin domin ci gaba da kokarin gano sauran mutanen da suka ɓata, jaridar The Sun ta rahoto.

Jami'in ya yi kira ga mazauna yankin da su rika bin dokokin zirga-zirgar ruwa da kuma hadin gwiwa da hukumomin tsaro da na agaji domin kare rayuka da hana faruwar irin wannan hatsari nan gaba.

Kwale-kwale ya nutse a Kebbi.
Mutane sun ɓata a ruwa da jirgin ruwa ya nutse a jihar Kebbi Hoto: Getty images
Source: Getty Images

Hukumomi sun ja hankali kan hawa kwale-kwale

“Muna roƙon al’umma da su rika yin amfani da rigar kariya ta ruwa da kuma bin shawarwarin jami’an ruwa kafin shiga jirgin ruwa, musamman a lokutan damina,” in ji shi.

Ya ce an fatan nan da gobe, da taimakon Allah, za a iya gano wasu daga cikin wadanda suka bace, domin iyalansu su samu kwanciyar hankali da sanin halin da suke ciki.

Kwale-kwale ya kife da nutane a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar ba da agajin gaggawa watau NEMA ta tabbatar da hatsarin kwale-kwale a kauyen Sullubawa da ke ƙaramar hukumar Shagari a jihar Sokoto.

Wannan mummunan lamari ya faru ne da safiyar wata ranar Litinin, yayin da kwale-kwalen da ke ɗauke da mutane ya kife a tsakiyar kogi.

Mutum bakwai ne suka rasa rayukansu a hatsarin, wanda aka gano cewa iska mai ƙarfi ce ta kifar da jirgin ruwan yana tsakiyar tafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262