'Ba Rigar Nono, ba Jarabawa' Jami'a a Najeriya Ta Ƙaƙabawa Mata Doka

'Ba Rigar Nono, ba Jarabawa' Jami'a a Najeriya Ta Ƙaƙabawa Mata Doka

  • Hukumomi a jami'ar Olabisi Onabanjo (OOU) ta kakabawa dalibai mata doka kan sanya rigar mama musamman a lokutan jarabawa
  • Dokar da jami'ar da ke jihar Ogun ta kawo ya jawo ce-ce-ku-ce bayan gabatar da dokar 'ba rigar nono, babu jarrabawa'
  • Wani bidiyo ya bayyana yadda jami'an makarantar ke tantance mata don duba ko suna sanye da rigar nono

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abeokuta, Ogun - Hukumar makarantar Olabisi Onabanjo (OOU),) da ke jihar Ogun ta sanya sabuwar doka ga mata dalibai kan sanya rigar nono.

Jami'ar da ke Ago-Iwoye a jihar Ogun ta jawo martani da dama bayan fara bin doka mai taken “ba rigar nono, ba jarrabawa”.

An Ƙaƙabawa mata doka a jami'a kan jarabawa
Jami'ar OOU ta hana mata jarabawa babu rigar nono. Hoto: oou_agoiwoye/X.
Asali: Twitter

Dokar hana mata jarabawa ta jawo ka-ce-na-ce

An gano faifan bidiyo da @dammiedammie35 ya wallafa a X inda wasu jami’an makarantar ke tantance wasu dalibai mata.

Kara karanta wannan

Bayan komawa APC, ƴan PDP sun kunyata ɗan majalisa, sun ƙi karbar tallafinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daliban matan na tsaye a jere, inda jami’an makarantar ke ta duba su domin gano ko suna sanye da rigar nono.

Yayin da wasu daga cikin daliban suka dauki abin da dariya, wasu kuma an hango su cikin rashin jin daɗi da damuwa.

Shi kuwa shugaban kungiyar dalibai na OOU, Muizz Olatunji (MAO), ya ce dokar da ta shafi rashin da’a ba sabuwa ba ce a makarantar.

Ya ce manufar dokar da'a ita ce karfafa sutura mai kyau ga daliban jami'ar OOU da ke jihar Ogun, cewar TheCable.

Hukumar makarantar har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da martanin jama’a.

An ƙaƙabawa mata doka kan jarabawa a jami'a
Jami'a ta hana jarabawa ga mata marasa rigar nono. Hoto: oou_agoiwoye/X.
Asali: Facebook

Wasu daga cikin masu amfani da kafar sadarwa sun yabawa matakin makarantar, yayin da wasu suka ce dokar bata da amfani ko mahimmanci a yanzu.

Ga wasu daga cikin ra’ayoyin jama'a kan lamarin:

@yopy30BG:

“Madalla. Dole mu koma ga tarbiyya."

@Williexhx:

“Akan yana da gaskiya. Afirka tana da tarihi mai kyau, amma rigar nono da salon sa suna da asali a Turai.

Kara karanta wannan

'Sarki ya yi barazanar korar Musulmi bayan sanya musu haraji a Ondo,' MURIC

"Hada tarbiyya da rigar nono kamar cewa Turawa ne suka kawo mana tarbiyya. Muna daukar kananan abubuwa mu bar manya."

@adeolu_bolaji:

“Gaskiya ne. Muna mantawa da rasa tarbiyya. Babu tarbiyyar gida, wasu iyaye suna yawo da nono suna kwance ba tare da kunya ba."

@AfrokonnectNG:

“Da kyau, muna ta lalacewa da kwaikwayon Turawa fiye da kima."

@LaughNLearnX:

“Matakin da ya dace yana da bukatar a dauka don dakile karancin kunya da ke kara yawaita kullum. Wannan yana da amfani."

@RealDamola:

“To yanzu ba sanye da rigar nono ke nuna mutum ba shi da kwakwalwa? Jarrabawa ya kamata ta danganci karatu, ba tufafi ba.
“In har ba don ilimi ba ne, to, wata hanya ce ta tilasta wa mata da sunan tarbiyya. Ba daidai ba ne."

Malaman jami'a sun shiga kuncin rashin albashi

Kun ji cewa malaman jami'ar Ahmadu Bello (ABU) a Zaria sun ce gwamnati na nuna rashin girmama malamai, musamman ma a lokacin bukukuwan Sallah.

Kara karanta wannan

Ana zargin Sarki da kokarin hana yin addinin Musulunci bayan hari kan limami, masallaci

Wani Farfesa ya bayyana takaicin yadda ba a biya malamai albashin watan Mayu ba har zuwa rana ta 6 na watan Yuni ba tare da bayani ba.

Malamin jami'ar ya bayyana cewa rayuwa mai kyau ko sayen ragon sallah sun zama tarihi wajen malamai a Najeriya a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.