Tirkashi: Tallar rigar nono ya jawowa jaruma Maryam Booth bakin jini ga masoyanta

Tirkashi: Tallar rigar nono ya jawowa jaruma Maryam Booth bakin jini ga masoyanta

- Fitacciyar Jaruma Maryam Booth ta ssha tofin Allah tsine ga mabiyanta na shafin Instagram

- Jarumar ta sha bakaken maganganun ne bayan ta wallafa wasu rigunan nono a shafinta inda take tallatasu akan kudi naira dubu goma sha shida

- Mabiyanta da yawa sun zage ta akan wannan kaya da ta wallafa, inda wasu kuma suka dinga yi mata nasiha akan cewa hakan da ta yi bai kamata ba

Jaruma Maryam Booth ta sha kalamai marasa kan gado na rashin da'a daga mabiyan shafinta na Instagram sakamakon tallata wasu samfurin rigunan mama da tayi a shafin ta akan zunzurutun kudi har naira dubu goma sha shida (N16,000), kowacce guda daya.

Jarumar dai ta wallafa hoton rigunan ne a shafinta inda ta kuma rubuta a kasa da harshen turanci cewa rigar nono La Senza ta sayarwa akwai lamba 36C da kuma 34D, farashinsu dubu goma sha shida duk guda daya.

Jim kadan da wallafa wadannan hajoji nata sai ta fara shan martani inda mafi akasarin masu korafin tsadar rigar nonon mata ne, inda wasu ke cewa rigar nonon 16,000 zasu siya kuma su dora mata wata rigar a saman ta, wata budurwa kuwa cewa tayi watakila ko tayi kuskure ne tana nufin dozen ne a wannan farashin.

KU KARANTA: Tirkashi: Jim kadan bayan daura aurensu amarya ta rabu da mijinta bayan ta gano cewa bashi da mazakuta

Sai dai jarumar ta mayar da martani da cewa ita wannan rigar mama ta La Senza haka kudinta yake ga wanda ya san farashinta, kowa ya san me tsada ce, sannan kuma ga wanda yake tantama zai iya bincikawa a shafin La Senza na yanar gizo domin tabbatar da farashin na ta.

A bangaren samari 'yan bana bakwai kuwa abin ya kazanta domin maganganu na rashin da'a suka dinga yiwa jarumar.

Wasu daga cikin mabiyan nata masu kaifin hankali sun fadakar da ita cewa a matsayinta na mace kuma sananniya bai kamata ta tallata irin wannan kayan sawar mata na ciki ba wanda mafi yawanci ansan mata da boye su zai fi kyau ta sai da su a shago ko rumfa inda matan za su je su siya amma ba ta wallafa a shafinta ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng