Fasto na sayar da dan kamfe da rigar nono ga mata, wadanda zasu dinga jawo hankalin maza kansu

Fasto na sayar da dan kamfe da rigar nono ga mata, wadanda zasu dinga jawo hankalin maza kansu

- Babban fasto JS Yusuf ya zo da wani sabon salo wanda ya zarce na sauran fastocin Najeriya masu mu'ujiza

- Faston na siyar da dan kamfai ne da rigunan nono ga mata dauke da hoton shi

- A cewar faston, idan mace ta saka wadannan kayan cikin, zasu ja hankalin maza zuwa garesu wanda daga baya zasu aure su

JS. Yusuf, babban faston Touch for Recovery Outreach International, wata coci ce da ke Abuja, an gano cewa ya fara siyar da dan kamfai da rigunan nono don samun miji ga 'yan matan cocin.

Yusuf ya ce wadannan kayan zasu sa mace ta samo miji a wannan sabuwar shekarar.

Dan kamfan da rigar nonon na dauke da hoton fuskar faston wanda ya ce zai kawo musu "sa'a" a wajen maza.

Fasto na sayar da dan kamfe da rigar nono ga mata, wadanda zasu dinga jawo hankalin maza kansu
Fasto na sayar da dan kamfe da rigar nono ga mata, wadanda zasu dinga jawo hankalin maza kansu
Asali: Facebook

Ya kara da cewa sanya wadannan kayan cikin zasu sa maza su kallesu idan suka fita kuma har su kai ga aurensu.

An zargi cewa ya kara da janyo aya ta ashirin uku da ke sura ta ashirin daga cikin littafin bibul mai cewa "na samu umarnin in albarkace ku kuma ya albarkaceni. Don hakan ba zan hana ba."

KU KARANTA: Ramuwar gayya: Miji ya harbe matarshi, su kuma matasa sun kone shi kurmus

Ana siyar da wadannan kayan ne a farfajiyar masallacin kamar yadda jaridar The Nation Online ta bayyana.

Wannan ba shine karo na farko da fastocin Najeriya ke zuwa da salo kala-kala na mu'ujiza ba. Akwai wani fasto da ke Abuja da ya hada tafkin wanka wanda ake kira da 'swimming pool' a cikin cocin. Ana biyan naira dubu hamsin kafin a fada don wanka da ninkaya a cikin ruwan.

A cewar faston, wannan ruwan na waraka kuma yana kore talauci. Ga wanda ba shi da dubu hamsin, ana iya dibar mishi ruwan tafkin a kwalba a kan naira dubu goma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: