Sarki Ya Shiga Uku, bayan Dakatar da Shi, an Tura Shi Gidan Yari kan Kalaman Ɓatanci

Sarki Ya Shiga Uku, bayan Dakatar da Shi, an Tura Shi Gidan Yari kan Kalaman Ɓatanci

  • Wata kotu a Ede a jihar Osun, ta bayar da umarnin tsare wani basarake da aka dakatar, Jimoh Abdulkabir, bisa zargin batanci
  • Ana zargin Abdulkabir da yada kalaman batanci da barazana a manhajar WhatsApp kan wani Alhaji Adam Akindere
  • Lauyansa ya nemi beli, yana cewa yana fama da ciwon gyambon ciki, amma kotu ta dage sauraron kara zuwa 19 ga Yuni, 2025

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Wani basarake ya kuma shiga tsaka mai wuya bayan dakatar da shi da aka yi daga sarauta.

Wata kotun majistare da ke zamanta a Ede a jihar Osun ta bayar da umarnin tsare Jimoh Abdulkabir.

An rasa keyar Sarki zuwa gidan yari
An tsare Sarki a gidan yari kan zargin ɓatanci. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da ake zargin Sarki ya aikata

Ana zargin basaraken ne mai shekara 45, wanda aka dakatar daga matsayin Loogun na Edeland, kan bata suna ga wani Adam Akindere, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Ana zargin Sarki da kokarin hana yin addinin Musulunci bayan hari kan limami, masallaci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana tuhumar basaraken da laifuffuka hudu, ciki har da bata suna, cin mutunci ta kafar sada zumunta.

Ana kuma zargin ya yi musu barazana, inda aka ce ya wallafa kalaman batanci a WhatsApp da suka ci mutuncin Akindere.

Bayan karanto masa zarge-zargen da ake yi kansa,, Abdulkabir ya musanta laifukan da ake tuhumarsa da su.

Mai gabatar da kara, sufeta Adepoju Sunday, ya shaida wa kotu cewa akwai hujjoji masu karfi, yana kuma rokon kotu da ta hanzarta sauraron karar.

Takardar tuhumar da aka shigar a kotu ta ce:

“Kai Abdulkabir Ajibade Jimoh 'M' da wasu da ba a kama ba, kun bata sunan Alhaji Adam Akindere 'M', ka wallafa karya a kafar WhatsApp cewa wai ya sayar da kadada 200 na fili ba tare da sanin Loogun ko wani daga cikin iyalinsa ba.”
“Kai Abdulkabir Ajibade Jimoh da wasu da ba a kama ba, kun aikata wani abu da zai iya haddasa rikici ta hanyar yada kalaman batanci da tunzura jama'a a WhatsApp kan Alhaji Adam Akindere 'M'.”

Kara karanta wannan

Sarkin musulmi ya aika da sako ga jami'an tsaro kan kisan Binuwai

An tsare Sarki a gidan yari kan zargin ɓatanci
An garƙame Sarki a gidan yari kan zargin kalaman ɓatanci Hoto: Gov. Ademola Adeleke.
Source: Twitter

Musabbabin dakatar da Sarki daga kujerarsa

Lauyansa, Taofeek Oyesiji, ya roki kotu ta bayar da belinsa, yana mai cewa laifuffukan da ake tuhumarsa da su ba su hana beli ba a wannan kotun.

Ya kuma sanar da kotu cewa wanda ake tuhuma ya kwanta a asibiti na CID ranar Asabar bayan kama shi, saboda yana fama da matsanancin gyambon ciki.

A tun farko dai, an dakatar da wanda ake kara daga mukaminsa daga fadar Timi na Ede, Oba Munirudeen Lawal a watan Afrilu, bisa zargin rashin girmama Sarki da rigimar filaye.

Mai shari’a V.A. Adedokun ya daga sauraron karar zuwa 19 ga Yuni, 2025, tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan yari, Tribune ta ruwaito.

Dakataccen Sarki ya dawo faɗa da ƙarfi

Mun ba ku labarin cewa rikicin sarauta ya barke a kauyen Muye, ta jihar Niger, bayan tsohon dagacin kauyen ya koma fada da karfi domin kwace kujerarsa.

Kara karanta wannan

'Zai wahala mu bari': Ado Aliero ya faɗi abin da zai sa su cigaba da ta'addanci

Rikicin ya kara kamari bayan magoya bayan bangarorin biyu da ke goyon bayan sarakunan biyu sun yi artabu, lamarin da ya tayar da hankula.

Jami'an tsaro sun shiga tsakani da gaggawa, kuma sun tabbatar da cewa an samu daidaito, yayin da ake cigaba da sa ido a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.