Bayan Kashe Mutane Sama da 200, Sufetan Ƴan Sanda na Ƙasa Ya Dura Jihar Benuwai
- Sufeta Janar na rundunar ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya isa jihar Benuwai domin ɗaukar matakan kare rayukan al'umma
- Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan biyan kisan gillar da wasu mahara suka yi wa mutne sama da 200 a ƙaramar hukumar Guma a Benuwai
- Tuni dai shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su kawo ƙarshen zubar da jinin da ke faruwa kuma yayi haramar kai ziyara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue - Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya isa jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya yau Litinin, 16 ga watan Yuni, 2025.
Kayode Egbetokun ya kai ziyara jihar ne domin duba barnar da wasu miyagun makiyaya masu haɗari suka yi a jihar ranar Juma’ar da ta gabata.

Source: Twitter
Channels tv ta tattaro cewa hare-haren da ƴan ta'addan suka kai garuruwa biyu ya haddasa mutuwar mutane da dama tare da raba daruruwa da muhallansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihar Benuwai dai na fama da hare-haren da ake zargin miyagun makiyaya da kai wa kan al'umma tsawon shekaru.
Wadannan hare-hare sun samo asali ne daga rikicin ƙabilanci da kuma rikici kan mallakar filaye tsakanin manoma ‘yan asalin yankin da kuma makiyayan da ke kiwon dabbobinsu daga wuri zuwa wuri.
Maharan sun kashe sama da mutum 200
Sai dai a cikin makonnin da suka gabata, hare-haren sun ƙara muni a kananan hukumomi daban-daban na jihar Benuwai.
Mutane sama da 200 ne aka tabbatar da mutuwarsu a hare-hare da ƴan ta'dddan suka kai ranar Juma'a da ddadare a yankunan ƙaramar hukumar Guma a Benuwai.
Tinubu ya fusata da kashe-kashen Benuwai
A ranar Lahadi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni ga hafsoshin tsaro da su yi duk mai yiwuwa wajen dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a Benuwai.
“Rahoton sababbin hare-hare da kashe-kashe da aka yi a jihar Benuwai yana da matuƙar ban takaici. Ba za mu ci gaba da zuba ido muna kallo ana zubar da jini ba tare da wani mataki ba. Ya isa haka.
"Na bayar da umarni ga hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa domin cafke duk masu hannu a wannan danyen aiki daga kowanne ɓangare tare da gurfanar da su a gaban kuliya,” in ji Tinubu.

Source: Facebook
Sufetan ƴan sandan Najeriya ya dura Benuwai
A kokarin cika umarnin shugaban ƙasa, sufetan ƴan sanda na ƙasa tare da tawagarsa sun dura jihar Benuwai domin ɗaukar matakan da suka dace.
IGP Kayode ya tura dakarun sashen dabaru domin kawo ƙarshen wannan kashe-kashe da ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Su wanene ke yawan kai hari jihar Benuwai?
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Alia ya yi ikirarin cewa makiyaya ɗauke da makamai ne kw yawan kai hare-hare kan al'umma a jihar Benuwai.
Ya ce makiyayan da ke aikata wannan ɗanyen aikin suna shigowa jihar Benuwai ba tare da shanunsu na kiwo ba, lamarin da ke nuna mummunar manufarsu.
Gwamnan ya kuma ce wasu daga cikin masu kai harin na shigowa ne ta iyakar Kamaru, yana mai jaddada cewa ba duka ba ne ƴan Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

