NiMet: 'Za a Sheka Ruwan Sama Kamar da Bakin Kwarya a Adamawa da Wasu Jihohi 7'

NiMet: 'Za a Sheka Ruwan Sama Kamar da Bakin Kwarya a Adamawa da Wasu Jihohi 7'

  • NiMet ta yi hasashen ruwan sama kamar da bakin kwarya zai sauka a jihohi takwas a makon nan, ciki har da Taraba da Bayelsa
  • Hukumar ta kuma yi gargadin yiwuwar ambaliyar ruwa a kan tituna da gadoji, wanda zai iya kawo tsaiko ga zirga-zirgar ababen hawa
  • Ambaliyar ruwa da aka fuskanta a wasu jihohin Najeriya a baya-bayan nan ya jawo asarar rayukan sama da mutum 200 da tarin dukiyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a iya samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu jihohi takwas a makon nan.

A cewar sanarwar mako-mako da hukumar ta fitar, jihohin da ake sa ran ruwan sama mai karfi zai fi yin tasiri sun hada da: Taraba, Bayelsa, Rivers, Delta, Abia, Akwa Ibom, Cross River da kuma Adamawa.

Kara karanta wannan

Abin ya juya: An shiga firgici a Kano da ango ya hallaka amaryarsa da wuƙa

Hukumar NiMet ta yi hasashen saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya a Adamawa da wasu jihohi 7
Ana sheka ruwan sama tare da tsawa da walkiya a wani gari. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jihohin da ruwan sama zai sauka da karfi

A cikin rahoton da NiMet ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata, hukumar an bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A makon nan, ana sa ran ma'aunin Madden-Julian (MJO) zai ci gaba da kasancewa marar karfi a yankin Yammacin Afirka.
“Ana sa ran dan shi da kuma iska mai karfi za su karfafa yiwuwar saukar ruwan sama mai karfi a yankunan Adamawa, Taraba, Bayelsa, Rivers, Delta, Abia, Akwa Ibom da Cross River.”

NiMet ta kara da cewa ana kuma sa ran ruwan sama zai mai karfi zai sauka a wasu sassan jihohin Taraba, Adamawa, Kaduna, Bayelsa da Plateau.

Sauran jihohin da ruwan zai sauka sun hada da Nasarawa, Kwara, Benue, Anambra, Rivers, Imo, Abia, Akwa Ibom, Ebonyi, Osun, Oyo, Ogun, Lagos, Ekiti, Ondo, Edo da Cross River.

'Za a iya samun ambaliya' - NiMet

Wasu sassan kasar da za su fuskanci matsakaicin ruwan sama sun hada da Taraba, Adamawa, Neja, Kaduna, Babban Birnin Tarayya (Abuja), Plateau, Kogi, Kwara, Ebonyi, Benue, Cross River, Ondo, Edo, Enugu da Ekiti.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta kammala shirin ranar dimokuradiyya, Tinubu zai yiwa kasa jawabi

NiMet ta kuma bayyana cewa akwai yiyuwar samun karancin ruwan sama a wasu sassan Bauchi, Sokoto, Zamfara, Kano, Katsina, Yobe, Borno, Jigawa, Gombe da Kebbi.

Hukumar ta gargadi al’umma game da hadurran ambaliya, musamman a kan tituna, gadoji da wuraren da ruwa ke taruwa, inda hakan ka iya haddasa tsaiko ga zirga-zirgar ababen hawa.

Gargadi da shawarwari ga 'yan Najeriya

  1. Ana iya samun iska mai karfi kafin hadari, don haka a dauki matakan kariya.
  2. A daure kayan da ke waje don gujewa hadurra sakamakon karfin iska.
  3. A guji tuka ababen hawa yayin ruwan sama mai karfi.
  4. A cire na’urorin wutar lantarki daga soket yayin da aka fara walƙiya.
  5. A nisanci manyan bishiyoyi ko wadanda ba su da karko yayin tsawa da walkiya.
  6. Masu jiragen sama su nemi cikakken hasashen yanayi na filayen jirgi daga NiMet.
  7. A ci gaba da samun sabbin bayanai ta shafukan NiMet: @nimetnigeria a Facebook, Twitter da Instagram.
Hukumar NiMet ta gargadi mutane kan tuki yayin da ake ruwa ko kuma tsayawa karkashin bishiya idan ana walkiya
Ana zabga ruwan sama hade da walkiya a wani gari. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An samu ambaliya a Afrilu-Yuni, 2025

A tsakanin Afrilu zuwa Yuni 2025, Najeriya ta fuskanci ambaliya, sakamakon ruwa mai yawan gaske da kuma matsaloli irin su toshewar hanyar ruwan ruwa, fashewar madatsan ruwa da kuma sauyin yanayi.

Kara karanta wannan

Tsohon Minista kuma ƙwararren likita, Farfesa Jibril Aminu ya kwanta dama

Jihohi da suka fi fuskantar illar ambaliyar a wannan lokaci sun hada da Neja, Rivers da Kwara, inda mutane da dama suka rasa rayukansu tare da lalacewar dukiyoyi da dama.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jihohi 30 daga cikin 36 na fuskantar hadarin ambaliya, wanda hakan ke barazana ga garuruwa sama da 1,200 da kuma mutane fiye da miliyan 15.

Sai dai, wani lokacin al'umma kan nuna rashin kulawa ga batutuwan da gwamnati ke yi game da sauyin yanayi.

Karanta sanarwar NiMet a kasa:

Sama da mutane 200 sun mutu a Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa ambaliya mai muni da ta auku a garin Mokwa da ke jihar Neja a karshen watan Mayu 2025 ta hallaka sama da mutane 200, ta lalata gidaje 3,000.

Yankunan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa ne suka fi shan wahalar ambaliyar yayin da aka danganta ambaliyar da yuwuwar fashewar madatsar ruwan da ke kusa da garin.

An ce ambaliyar ta tafi da babbar gadar Mokwa, sannan ta shafe gonaki da haura hekta 10,000 na shinkafa, lamarin da ya janyo asarar biliyoyin Nairori ga manoma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com