Wike Ya Kara Neman Fada Wurin Shugaba Tinubu, Ya Canza Sunan ICC da ke Abuja
- Nyesom Wike ya canza sunan cibiyar taro ta ƙasa da kasa da ke Abuja, ya sa mata sunan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
- Ministan harkokin Abuja ya bayyana haka ne a wurin taron kaddamar da cibiyar wanda Tinubu ƴa jagoranta a yau Talata
- Wike ya ce daga yanzu, duk wanda zai amfani da cibiyar sai ya biya kuɗi, yana mai cewa za a yi amfani da kuɗin wajen kula da wurin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya sauya sunan babbar cibiyar taro ta ƙasa da ƙasa da ke Abuja bayan kammala gyaran wurin.
Mista Wike ya canza sunan cibiyar taron daga 'International Conference Centre (ICC)', zuwa 'Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre'.

Source: Twitter
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ministan ya sanya wa babban ɗakin taron sunan 'cibiyar taron ƙasa da ƙasa ta shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu'.

Kara karanta wannan
"Abubuwa sun lalace," Peter Obi ya faɗi hanya 1 da ƴan Najeriya za su ƙifar da Tinubu a 2027
Tsohon gwamnan jihar Ribas ya bayyana hakan ne a wurin taron kaddamar da sabon ginin wanda ya gudana yau Talata, 10 ga watan Yuni, 2025 a Abuja.
Minista ya bullo da tsarin amfani da cibiyar
Da yake magana yayin bude ginin a a Abuja, Wike ya bayyana sabon ɗakin taron a matsayin gini na zamani mai inganci, wanda ke bukatar a riƙa kula da shi a kai a kai.
Ya kara da cewa duk wanda zai yi amfani da wannan wurin, ya zama dole ya biya kudi, komai matsayinsa a cikin al'umma, rahoton Vanguard.
Wike ya bayyana cewa cibiyar taron da gwamnatin soja ta Ibrahim Babangida ta gina a 1991 ta kama hanyar lalacewa saboda ba a taba gyara ta ba tun da aka buɗe ta.
Ya kara da cewa duk wata ma’aikata ko hukumar gwamnati da ke son amfani da dakunan taro na cibiyar dole ne ta biya kudi don a kula da kayayyakin wurin.
"Ta ya za mu tabbatar da cewa cibiyar ta dore? Ina san kowa ya sani daga yau, ma'aikata ko hukumar gwamnati, duk wanda zai amfani da wannan wuri sai ya biya kuɗi.
"Ba ruwanmu da auren ɗan uwana ko ƴar uwata za a yi a wurin, matukar kana so mu baka wurin ku yi amfani da shi, sai ka biya wani abu."
- Nyesom Wike.

Source: Twitter
Shugaba Tinubu ya goyi bayan Wike
A nasa jawabin, Shugaba Tinubu ya goyi bayan Wike, yana mai cewa ana bukatar biyan kudi kafin a iya amfani da wannan cibiyar domin kula da ita yadda ya kamata.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ƴa jagoranci kaddamar da cibiyar taron bayan ya dawo daga hutun Sallah da ya shafe makonni a Legas.
Wike ya musanta zargin akwai masu juya Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya musanta zargin cewa wasu tsirarun mutane ke juya gwamnatin shugaban kasa, Bola Tinubu.
Tsohon gwamnan ya nuna mamaki ƙarara kan yadda mutane ke yaɗa jita-jita mara tushe ballantana makama ba tare da sun yi bincike ba.
Mista Wike ya kuma caccaki masu cewa bai dace da matsayin minista ba, yana mai cewa duk masu faɗar hakan ba su san abin da suke yi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
