Duk da Umarnin 'Yan Sanda, Sarkin Kano Sanusi II Ya Yi Hawan Fanisau

Duk da Umarnin 'Yan Sanda, Sarkin Kano Sanusi II Ya Yi Hawan Fanisau

  • Mai martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya gudanar da al'adar Hawan Fanisau a ranar Talata, 10 ga watan Yuni, 2025
  • Sai dai an gudanar da hawan ba tare da karya dokar haramta hawa dawaki da rundunar yan sandan Kano ta gindaya ba a makon jiya
  • Duk da sauyin da aka samu a tsarin hawan, dubunnan jama'a sun fito kan tituna domin shaida fitowar Sarkin daga Kofar Kudu zuwa Fanisau

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ci gaba da al’adar Hawan Sallarsa ta shekara-shekara, bayan yan sanda sun haramta hawa dawakai.

A wannan lokacin, Mai Martaba Sarkin ya shiga jerin gwanon motoci don gudanar da hawan Fanisau, wanda ya saba wa al’adar da aka saba gani ta amfani da dawaki.

Kara karanta wannan

Da gaske an jefi Sarki Sanusi II da dutse a hawan sallah a Kano? An samu bayanai

Sarkin Kano ya yi hawa
Duk da umarnin yan sanda, Khalifa Sanusi ya yi hawan sallah Hoto: Sanusi II Dynasty
Source: Facebook

Jaridar Leadership News ta wallafa cewa, tun da farko rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanya dokar hana hawan dawakai da aka saba yi a wajen taron saboda tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi ‘hawan’ sallah

Wani ganau da ya shaida fitowar Sarki daga fadarsa, Khalil Ibrahim Yaro, ya tabbatar da cewa dimbin jama’a sun cika tituna suna kallon fitowar mai martaba.

An fito kallon 'hawan' Sarki a Kano
Sarkin Kano ya yi hawan Fanisau a mota Hoto: Sanusi II Dynasty
Source: Facebook

An fara hawan ne da fitowa daga Kofar Kudu, inda Sarkin, tare da manyan baki, mataimaka na masarauta, da kuma masoya, suka nufi Fanisau, wani gari a karamar hukumar Ungoggo ta jihar.

Duk da sauyin da aka samu daga yadda aka saba gudanar da hawan, jama'a sun yi cikar kwarin dango domin kallon 'hawan' Sarki.

Yadda mazauna Kano suka tarbi hawa

Titunan sun cika da masu kallo, wadanda suka taru domin shaida wucewar Sarki, Khalifa Muhammadu Sanusi II zuwa Fanisau.

Duk da haka, wasu mazauna garin sun nuna fargabar bin motocin zuwa Ungoggo saboda dalilan tsaro, wanda suka ce dama hawan Fanisau ya gada.

Kara karanta wannan

'Ndume ba ya iya bakinsa,' Fadar shugaban kasa ta yi zazzafan martani ga Sanatan Borno

Wani mazaunin Kano, Ibrahim Aminu, wanda ya zanta da Legit, ya ce:

“Akwai barazanar tayar da tarzoma ko fadace-fadace da wasu matasa ke yi a lokacin hawan Fanisau, ya sanya al’umma kan kauracewa hawan baki dayansa.”
“Ni ma ba zan ce hawan ba, duk da kuwa ina son hawan Fansau sosai.”

Wannan ita ce shekara ta biyu a jere da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanya dokar hana hawan dawakai a Hawan Sallah, inda suka bayyana barazanar tsaro a matsayin dalilin hana hawan.

Hawan Sallah a idon Hausawa

A al’adance, Hawan Sallah wata muhimmiyar al’ada ce da ake alfahari da ita a Arewacin Najeriya, musamman a jihar Kano, inda take nuna karfin tarihi, al’ada da kuma zumunci tsakanin masarauta da talakawa.

Sai dai tun bayan darewar Gwamna Abba Kabir Yusuf mulki a shekarar 2023, an fuskanci canje-canje da suka janyo cece-kuce da rarrabuwar ra’ayi a tsakanin al’umma, musamman kan yadda ake gudanar da Hawan Sallah.

Wasu daga cikin jama’ar Kano, musamman magoya bayan tsohon sarki Aminu Ado Bayero, na ganin sabbin hanyoyin gudanar da hawan na nuna son zuciya ko sauya al’ada domin amfanin siyasa.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi da wani Musulmi ya mutu a wani irin yanayi bayan dawowa daga idi

A gefe guda kuma, magoya bayan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II na kallon hawan a matsayin ci gaba da martaba masarauta duk da kalubalen tsaro da ke akwai.

Haka kuma, takaddama tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro kan batun hawan dawakai ya haifar da rashin tabbas da rudani a zukatan mutane, inda wasu ke jin tsoron halartar tarukan saboda yuwuwar rikici.

Wannan hali ya sa Hawan Sallah, wanda ke zaman biki na farin ciki da hadin kai, ya rikide zuwa wani abu mai tayar da hankali a wasu lokuta.

An samu bayanai kan jifan Sarkin Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani al'amari ya dauki hankalin jama'a a lokacin da ake bikin hawan Nasarawa, inda aka hangi wani abu ya fado a kusa da hular Khalifa Muhammadu Sanusi II.

Sai dai, wani mai daukar hoto da ke wurin, Salim Ameenu, ya fito fili ya bayyana gaskiyar abin da ya faru, ya tabbatar da cewa ba dutse aka jefa ba kamar yadda wasu ke zargi ya faru.

A cewar Salim Ameenu, yana cikin sarrafa na'urarsa zai zagaya inda Mai Martaba ke jawabi yayin Hawan Nasarawa, sai batirinsa ya yi sanyi, lamarin da ya sa ta fado kusa da Sarkin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng